Sunday, April 26
Shadow

Duk Labarai

Tsohon Mataimakin Peter Obi a zaben 2023>>Yusuf Datti Baba Ahmad ya fito takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party

Tsohon Mataimakin Peter Obi a zaben 2023>>Yusuf Datti Baba Ahmad ya fito takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party

Duk Labarai
Tsohon Mataimakin Peter Obi a zaben shugaban kasa na shekarar 2023, Yusuf Datti Baba Ahmad ya bayyana cewa, zai fito takarar shugaban kasa zaben shekarar 2027 a jam'iyyar Labour Party. Ya bayyana cewa idan ya zama shugaban kasa, a watanni na farko zai tabbatar ya linka Albashin jami'an tsaro da sau 4. https://twitter.com/i/status/2008929943150071954
Kotu ta bayar da Umarnin EFCC ta rike kadarorin Abubakar Malami 57

Kotu ta bayar da Umarnin EFCC ta rike kadarorin Abubakar Malami 57

Duk Labarai
Kotun tarayya dake da zama a Abuja ta amincewa hukumar EFCC ta ci gaba da rike kadarorin tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami. Kotun tace EFCC ta rike kadarorin guda 57 na wucin gadi kamin a amince a kwacesu na dindindin. Hakanan Kotun ta bayar da belin Malami da dansa da matarsa. Hakanan a zaman kotun, Mai Shari'a, Justice Emeka Nwite ya Gargadi Lauyan Abubakar Malami cewa kada ya sake yace zai nemi wata Alfarma a wajansa. Yace ba zai lamunce a bata masa suna ba kuma duk sanayyarsa da mutum idan aka zo wajan aiki zai nuna ba sani ba sabo.
Abin Kunya: ‘Yan Kwallon Najeriya, Super Eagles sun ce ba zasu je buga wasan su da Algeria ba idan ba’a biyasu hakkokinsu ba

Abin Kunya: ‘Yan Kwallon Najeriya, Super Eagles sun ce ba zasu je buga wasan su da Algeria ba idan ba’a biyasu hakkokinsu ba

Duk Labarai
Kungiyar 'yan kwallon Najeriya ta Super Eagles da masu horas dasu sun ce ba zasu je wasan da zasu buga da Algeria ba idan ba'a biyasu hakkokinsu ba. Kungiyar ta bayyana cewa akwai alkawuran kudaden da aka musu idan suka yi nasara a wasanni da kasashen Tanzania, Tunisia, Uganda, da Mozambique amma ba a cika musu wadannan alkawuran ba. Kungiyar tace ba zata ke garin Marrakech ba ranar Alhamis dan yin Atisayen wasan da zasu buga da kungiyar kasar Algeria ba idan ba'a biyasu ba. Najeriya dai zata yi wasan Quarter finals da kasar Algeria.
Kalli Bidiyon: Ni kirista ne amma na zama Musulmi

Kalli Bidiyon: Ni kirista ne amma na zama Musulmi

Duk Labarai
Wannan Kiristan ya bayyana cewa, ya Musulunta, saidai yace shi mawaki ne Yace babban dalilinsa na komawa Musulmi shine dan wakarsa ta samu daukaka. https://www.tiktok.com/@funnyalpha/video/7592315088418229524?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7592315088418229524&source=h5_m&timestamp=1767796279&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&item_author_type=2&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_iid=7568740291232040721&share_link_id=3704f903-f8e3-4f92-8cbe-059cd3640d9e&share_app_id=1233&ugbiz_name=MAIN&ug_btm=b8727%2Cb2878&link_r...
Wani na Kusa da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi magana kan Malamin da aka ce yana son auren Hajiya A’isha Buhari

Wani na Kusa da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi magana kan Malamin da aka ce yana son auren Hajiya A’isha Buhari

Duk Labarai
Bashir Ahmad yayi magana kan jita-jitar auren Shiekh Pantami da Aisha Buhari Wannan ba labari ba ne da ya kamata ma a tsaya ana ƙoƙarin ƙaryata shi, domin duk wani mai hankali ba zai ɗauke shi da muhimmanci ba. Sai dai tunda har yanzu wasu na ci gaba da yaɗa wannan jita jitar, ya zama dole a fayyace gaskiya. Labarin da wasu ke yadawa cewa Hajiya Aisha Buhari ta amince za ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ce tsagwaronta. Babu ko ƙwayar gaskiya a cikinsa kwata-kwata. -inji Bashir Ahmad tsohon hadimin margayi Buhari Me zaku ce? Daga Kafar Ayau News
Kalli Bidiyon: Gwamna Abba ya bayyana wata Magana da Kwankwaso yayi da bai ji dadinta ba

Kalli Bidiyon: Gwamna Abba ya bayyana wata Magana da Kwankwaso yayi da bai ji dadinta ba

Duk Labarai
An ga wani tsohon Bidiyon gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya na fadar wata magana da Kwankwaso yayi wadda bai ji dadinta ba. Bidiyon dai tsohone amma yana ta yawo a kafafen sada zumunta. An ji Abba yana cewa, Kwankwaso yace idan sun nemi shawara zai basu idan basu nema ba zai zuba musu ido. Saidai Abban yace bai ji dadin wannan magana ba dan har sai da ya je ya samu Kwankwaso akan maganar. https://twitter.com/i/status/2008838947787731344