Saturday, January 11
Shadow

Duk Labarai

Hotuna: Dangote ya kaddamar da kamfanin hada manyan motoci a Legas

Hotuna: Dangote ya kaddamar da kamfanin hada manyan motoci a Legas

Duk Labarai, Kasuwanci
Babban Attajirin Najeriya, Aliko Dangote, ya kaddamar da kamfanin hada manyan Motoci a Legas. Gwamnan Legas, Sonwo Olu, Kakakin majalisar tarayya, Goodswill Akpabio, na daga cikin wanda suka halarci bikin kaddamar da kamfanin. https://www.youtube.com/watch?v=3mgRsma4s8o?si=fQCNR0Vvdd2Rfcsi kamfanin zai rika hada manyan motoci akalla dubu 10 a shekara kuma zai samarwa da mutane dubu 3 aikin yi.
Hotuna: ‘Yan IPOB sun kashe ‘yansanda biyu a Imo

Hotuna: ‘Yan IPOB sun kashe ‘yansanda biyu a Imo

Tsaro
Rahotanni daga jihar Imo na cewa wasu da ake kyautata zaton 'yan IPOB ne sun kashe 'yansanda 2 da kuma farar hula 1. Lamarin ya farune ranar Talata a Titin Oweri Ogikwe dake jihar. Hakanan dayan mutumin an harbeshine a cikin gida. Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya farune da misalin karfe 6:25 na safe. Zuwa yanzu dai hukumar 'yansandan jihar batace uffan ba kan lamarin.

Abincin dake gina jiki

Duk Labarai
Abincin dake gina na da yawa, saidai za'a iya cewa iya kudinka iya shagalinka. Yawanci an fi alakanta abincin dake gina jiki da wanda wuta bata tabashi ba amma akwai abincin dake gina jiki da yawa wanda ake dafawa. Bari mu fara da abincin dake gina jiki wanda wuta bata tabasu ba. Akwai: Zogale Yadiya Lansir Latas kabeji dabino Lemun zaki Ayaba Tuffa(Apple) Inibi Kankana Gwanda Mangwaro. Gwaba Kwakwa Gyada Abinci me gina jiki wanda aka sarrafa: Yoghurt Chocolate Coffee Madarar waken suya Kunun Gyada Kunun Aya Kunun Tsamiya. Abinci me gina jiki wanda aka dafa Wake Dafaffiyar masa Gasashshiyar masa Kayan cikin. Nama gasashshe Nama Farfesu Fate da wake ko da gyada a ganye. Dambu da G...

Sunayen Larabawa masu dadi

Duk Labarai
Ga sunayen larabawa masu dadi kamar haka: Bari mu fara da sunayen Larabawa maza: Abbas Abdulaziz Abdulkarim Abdulmalik Abu Bakr Adil Adnan Aiman Akram Alaa Aladdin Ameer Asad Atif Ayham Badr Baha Bassam Basim Dawud Dhulfiqar Eid Emad Fadi Faisal Firas Ghassan Habib Haitham Hakim Hani Harith Hilal Idris Ihab Ilyas Ismail Issa Jabir Jafar Jamil Jibril Kamal Kareem Khalaf Latif Luay Lutfi Majed Marwan Mazin Moustafa Mufid Munir Murad Mustafa Nasir Nawaf Nazim Nouman Numan Qasim Qays Radwan Rami Rayyan Ridwan Rifat Riyad Sabir Saber Saif Salah Sameer Sami Samir S...
Gwamnonin kudancin Najeriya suna son a kafa ƴansandan jiha

Gwamnonin kudancin Najeriya suna son a kafa ƴansandan jiha

Katsina
Ƙungiyar gwamnonin kudu-maso-yammacin Najeriya sun nemi a kafa rundunonin ƴansanda mallakar jihohi. Sai dai kuma sun yi fatali da fafutukar da wasu ke yi na kafa ƙasar Yarabawa zalla. Wannan na cikin ajanda 11 da suka amince da su bayan taron da suka gudanar a Ikeja babban birnin jihar Legas a ranar Litinin. Gwamnonin sun kuma taɓo batun sabon mafi ƙarancin albashi, inda suka yi nuni da cewa zai zo da tsarin tarayya na gaskiya. Matsalar tsaro malace da daɗe tana ciwa jihohin ƙasar tuwo a kwarya, sai dai wasu na ganin kafa ƴansandan jihohin zai taimaka wajen magance matsalar. A baya dai rundunar ƴansandan ƙasar ta yi watsi da irin wannan buƙata ta kafa ƴnsandan jiha a ƙasar.
Ƴanbindiga sun kashe mutane 25 a Ƙanƙara jihar Katsina

Ƴanbindiga sun kashe mutane 25 a Ƙanƙara jihar Katsina

Katsina, Tsaro
Akalla mutane 25 aka hallaka, sannan aka sace wasu da dama a lokacin da ƴanbindiga suka kai hari a wani ƙauyen a jihar Katsina a arewacin Najeriya, a cewar hukumomi. Gwamman ƴanbindigar sun isa ƙauyen Yargoje da ke ƙaramar hukumar Ƙankara a ranar Lahadi da daddare ne, kamar yadda kwamishinan tsaro na jihar, Nasiru Babangida Mu'azu, ya shaida wa BBC Hausa. Mazauna ƙauyen sun ce maharan sun dinga harbin kan mai uwa da wabi, yayin da suka fasa shaguna tare da sace mutanen da kawo yanzu ba a san adadinsu ba. Sai dai wasu rahotanni na cewa ƴanbindigar sun kashe fiye da mutane 50 tare da jikkata kimanin wasu 30. A watan Disamba 2020, wasu ƴanbindiga sun sace ɗaliba 300 daga wata makarantar sakandare ta kwana ta maza da ke wajen Ƙankara, amma daga bisani aka sake su. Matsalar ƴanfa...
Matatar Dangote ta ɗage fara samar da fetur a Najeriya

Matatar Dangote ta ɗage fara samar da fetur a Najeriya

Duk Labarai
Katafariyar matatar mai mallakar hamshaƙin ɗankasuwan nan, Alhaji Aliko Dangote ta ɗage ranar da zata fara fitar da man fetur domin sayarwa a cikin ƙasar zuwa watan Yuli. Attajirin ya ce an ɗage ne saboda sun samu wani jinkiri, amma ya bayar da tabbacin fara samar da man fetur ɗin a tsakiya zuwa ƙarshen watan goben, kamar yadda kafar watsa labarai ta Channels TV ta bayyana. Tuni dai wasu dillalan man suka yi rajista da kamfanin domin fara ɗaukar man tare da rarraba shi a fadin ƙasar. Haka kuma kamfanin ya fara sayar da man dizil da na jirgin sama a ƙasar. Tun a watan Disambar 2023 ne matatar ta fara aiki, inda ta ke tace gangan danyen mai 530,000 a rana. Mahukunta a ƙasar na fatan fara samar da man fetur daga matatar ta Dangote za ta taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar ƙaran...
Atiku ya yi Allah-wadai da harin da ya kashe mutum 50 a jihar Katsina

Atiku ya yi Allah-wadai da harin da ya kashe mutum 50 a jihar Katsina

Labaran Atiku Abubakar, Siyasa
Ɗan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyar adawa ta PDP, a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi alla-wadai da harin da aka kai ƙauyen Ƴargoje da ke jihar Katsina, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama. Harin da ‘yan bindiga suka kai, ya kuma haɗa da garkuwa da mata da kananan yara marasa galihu, lamarin da ya kara ta’azzara wa al’ummar yankin. Da yake nuna alhininsa game da faruwar lamarin, Atiku ya yi ƙarin haske kan harin kwantan ɓauna da maharan suka yi wa jami’an tsaron da ke amsa kiran gaggawa a kauyukan Gidan Tofa da Dan Nakwabo wanda yayi sanadin mutuwar jami’an ‘yan sanda hudu da wasu ‘yan kungiyar sa ido na jihar Katsina guda biyu. “Wannan babban rashi ne, kuma tunanina yana tare da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu,” in ji shi Atiku ya soki matakan da gwamnati...

Mataimakin shugaban Malawi ya mutu

Siyasa
Mataimakin shugaban ƙasar Malawi, Saulos Chilima ya mutu sakamakon haɗarin da jirgin da ke ɗauke da shi ya yi ranar Litinin. Shugaban ƙasar ta Malawi, Lazarus Chikwera ya ce "jirgin nasa ya daki dutse" ne inda jirgin ya tarwatse kuma mista Chilima da dukkan waɗanda ke cikin jirgin suka rasu. An dai samu tarkacen jirgin ne a kusa da wani tsauni. An dai kwashe awanni ana bincike domin gano jirgin saman da ke ɗauke da mataimakin shugaban ƙasar Malawi. Jirgin saman ya ɓace ne a ranar Litinin da safe. Ana tunanin ya faɗi ne a dajin Chikangawa Forest da ke arewacin ƙasar. Ya fuskanci rashin kyawun yanayi abin da ya sa aka hana jirgin sauka a filin jirgin sama na Mzuzu. Shugaban Malawi ya ce ya ba da umarnin a ci gaba da aikin ceto mataimakinsa Saulos Chilima har sai an gano ...