Ji yanda ake ciki kan maganar mafi karancin Albashi tsakanin Gwamnati da NLC, inda ake tunanin za’a sake komawa yajin aiki
Tattaunawa na ci gaba da gudana tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago ta NLC da TUC inda ake tsammanin za'a karkare a yau.
Kungiyar tace ta gabatarwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da bukatarta ta a biya Naira 250,000 a matsayin mafi karancin albashi kuma tana jiran ta ji amsa daga gareshi.
Saidai matsayar gwamnati shine biyan Naira 62,000 a matsayin mafi karancin Albashin.
Shuwagabanni kwadagon sun je Geneva, Kasar Switzerland inda suke halartar taro kan kungiyoyin kwadago na Duniya.
Kuma ana tsammanin bayan aun kammala taron, zasu dawo a samu matsaya kan mafi karancin Albashin.