Sunday, April 26
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyon: Da Gwamnan daya saka hannu a Dokar Haraji, Da Dan majalisar, da Shugaban kasar….. Maryam Gombe ta fusta bayan data tura dubu 20 aka cire mata Naira 100 kudin Haraji

Kalli Bidiyon: Da Gwamnan daya saka hannu a Dokar Haraji, Da Dan majalisar, da Shugaban kasar….. Maryam Gombe ta fusta bayan data tura dubu 20 aka cire mata Naira 100 kudin Haraji

Duk Labarai
Tauraruwar Tiktok, Maryam Gombe ta bayyana fushinta akan cire mata Harajin Naira 100 bayan data tura Naira dubu 20. Ta yiwa shuwagabannin Najeriya Tofin Allah Tsyne inda tace kuma kudinta ba zata yafe ba. Tace ko babantane ya saka wannan doka bata yafe masa ba. Danna nan dan kallon Bidiyon ta
Tsohon Ministan Tsaro, Muhammad Badaru ya musanta Rahotan cewa zai koma jam’iyyar ADC

Tsohon Ministan Tsaro, Muhammad Badaru ya musanta Rahotan cewa zai koma jam’iyyar ADC

Duk Labarai
Tsohon Ministan tsaro, Muhammad Badaru ya musanta Rahotannin dake yawo cewa, zai koma jam'iyyar ADC. A wata sanarwa da ya fitar ta bakin me magana da yawunsa, Safwan Sani Imam ya bayyana cewa rahotanni shirin komawarsa ADC ba gaskoya bane. Yace shi har yanzu dan jam'iyyar ADC ne wanda dashi aka kafata. Yayi kira ga jama'a da su yi watsi da rahotannin dake cewa zai koma jam'iyyar ADC.
An bayyana manyan mutane 40 da Ministan Abuja, Wike ke fada dasu

An bayyana manyan mutane 40 da Ministan Abuja, Wike ke fada dasu

Duk Labarai
An fitar da Jadawalin manyan mutane 40 da Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike me fada dasu Gasu kamar haka: *HE Atiku Abubakar - Archenemy*HE Aminu Tambuwal*HE Rotimi Amaechi*HE Peter Obi*HE Bukola Saraki*HE Peter Odili and Wife*Sen. David Mark*HE Rauf Aregbesola*Gov. Makinde*Gov Fubara*Gov Douye Diri*Gov Bala Mohammed*Dr. Ajibola*Dr. Patience Jonathan*Senator Azuta Mbata*Prince Uche Secondus*Professor Iyorchia Ayu*Lieutenant General Buratai rtd*Vice Admiral Gambo rtd*Senator David Umahi*Major General Jamil Sarham*HE Adams Oshiomole*HE Godwin Obaseki*HE El Rufai*Commodore Bode George rtd*Lieutenant Yerima*Dr. Good luck Jonathan*HE Celestine Omehia*Abiye Sekibo*Late President Muhammadu Buhari*Senator Seriake Dickson*Prince Tonye Princewill*George Turnah*Dino Melaye*Sena...
Wata Sabuwa: Obasanjo yace Peter Obi yake son ya tsaya takarar shugaban kasa, Kwankwaso ya masa Mataimaki a ADC

Wata Sabuwa: Obasanjo yace Peter Obi yake son ya tsaya takarar shugaban kasa, Kwankwaso ya masa Mataimaki a ADC

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bukaci Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya koma jam'iyyar ADC. Ya kuma bayyana cewa, Peter Obi yake son ya fito a matsayin dan takarar shugaban kasa sai Kwankwaso ya masa mataimaki. An dauki wannan matakinne dan a kayar da Atiku kada ya samu tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC. Hakanan Rahoton wanda Jaridar Daily Trust ta ruwaito yace tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida me ritaya shima ya gayawa Kwankwaso ya koma ADC. Hakan na zuwane yayin da ake ganin Atiku ne zai lashe tikitin takarar shugaban kasa a ADC idan Kwankwaso da Peter Obi basu hada kai ba.
Da Duminsa: Bayan da suka Haramtawa ‘yan kasar Amurka shiga kasarsu, Kasar Mali ta kama wani dan Amurka ya shiga kasarta

Da Duminsa: Bayan da suka Haramtawa ‘yan kasar Amurka shiga kasarsu, Kasar Mali ta kama wani dan Amurka ya shiga kasarta

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Mali na cewa, kasar ta kama wani dan kasar Amurka da ya shigar mata kasa. Tuni kuma aka mayar dashi kasarsa. Kasar Mali dai ta hana 'yan kasar Amurka shigar mata kasa a matsayin martani ga hanin da kasar ta Amirka tawa 'yan kasar Mali shigar mata kasa. https://twitter.com/i/status/2008230251382309256
Ji abinda Kwankwaso yace akan Abba game da zagayowar ranar Haihuwar gwamnan Kanon

Ji abinda Kwankwaso yace akan Abba game da zagayowar ranar Haihuwar gwamnan Kanon

Duk Labarai
Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya taya Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf murnar zagayowar ranar Haihuwarsa. Ya wallafa sako a shafinsa na X inda yace yana Taya Abba Murnar zagayowar ranar Haihuwarsa. Kwankwaso yace ya tuna irin yanda suna yi rayuwa tare da Abba inda ya masa mataimaki na musamman a lokacin yana Gwamna a zangon farko, hakanan sanda ya zama Ministan tsaro ya kuma tafi da abba a matsayin mataimaki na musamman. Kwankwaso yace bayan nan ma kuma daya sake zama Gwamnan Kano, ya sake dauko abba a matsayin kwamishina kamin daga baya ya zama gwamnan Kano. Kwankwaso yace sun yi aiki tare dan ciyar da jihar Kano gaba. inda yace yana masa fatan Alheri. https://twitter.com/i/status/2008306292075421909
Allah Sarki: Na karanta Qur’ani na fahimci cewa wannan littafi ne da ba wani mutum da ya isa ya Rubutashi, Shiyasa ni da matata muka musulunta>>Inji Baturen Ingila, Dr. Mark Thompson

Allah Sarki: Na karanta Qur’ani na fahimci cewa wannan littafi ne da ba wani mutum da ya isa ya Rubutashi, Shiyasa ni da matata muka musulunta>>Inji Baturen Ingila, Dr. Mark Thompson

Duk Labarai
Baturen Ingila, Dr. Mark Thompson wanda yanzu ya canja suna zuwa Abdullahi ya karbi Musulunci shi da matarsa. Yace ya karanta Qur'ani ya fahimci cewa Littafi ne wanda mutum bai isa ya rubutashi ba dan haka shi da matarsa suka karbi Musulunci. Yace ya ziyarci Makkah yayi ibada amma kuma da ya koma kasarsa, sai ya kasa samun nutsuwa. Yace dan hakane ya sake komawa dan yayi Ibada.
Kalli Bidiyon: Rikicin Osimhen da Ademola Lukman ya dauki hankula

Kalli Bidiyon: Rikicin Osimhen da Ademola Lukman ya dauki hankula

Duk Labarai
A wasan da Najeriya ta buga da Mozambique a daren jiya, An ga Victor Osimhen nawa Ademola Lukman tsawa a filin wasan. Lukman dai be biye masa ba wanda hakan yasa wasu suka rika sukar Osimhen game da lamarin. https://twitter.com/i/status/2008282216510447942 Bayan wasan an tambayi Ademola Lukman kan cewa menene ya faru tsakaninsa da Victor Osimhen, saidai ya kayar da baki yace ba komai wasane. https://twitter.com/i/status/2008312453608689986 Wannan amsa ds ya bayar ta dauki hankulan mutane sosai inda akai ta yaba masa.