Saturday, March 14
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyon: A karin Farko an hango Jirgin saman sojojin Najeriya, C-130 dake ajiye a filin jirgin kasar Burkina Faso

Kalli Bidiyon: A karin Farko an hango Jirgin saman sojojin Najeriya, C-130 dake ajiye a filin jirgin kasar Burkina Faso

Duk Labarai
An Hango jirgin saman sojojin Najeriya C-130 dake ajiye a filin jiragen saman kasar Burkina Faso. Jirgin dai na dauke da sojoji 11 ne na Najeriya da hukumomin Najeriya suka ce ya samu tangarda a hanyarsa ta zuwa kasar Portugal ya sauka a kasar ta Burkina Faso. Saidai hukumomin kasar Burkina Faso sun zargi akwai wata maqarqashiya game da saukar jirgin a kasarsu. https://twitter.com/GallantDaletian/status/2000892186674528536?t=yxeUTLLX9UFobJ9bdyftuw&s=19
Ji yanda na kusa da Buhari suka so a tsayar da Sanata Ahmad Lawal takarar shugaban kasa a APC

Ji yanda na kusa da Buhari suka so a tsayar da Sanata Ahmad Lawal takarar shugaban kasa a APC

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, na kusa da Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari sun yi kokarin ganin an tsayar da Sanata Ahmad Lawal takarar shugaban kasa a jam'iyyar ba Tinubu ba. Rahoton yace wadannan mutane sun rubuta takardar Boge inda suka ce daga shugaban kasa ne suka mikawa shugaban 'yansanda da shugaban DSS suka basu Umarnin su tabbatar Sanata Sanata Ahmad Lawal ne ya zama dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC. Saidai shugaban 'yansandan a wancan lokacin ya nemi tabbatar da wannan umarni kai tsaye daga wajan shugaba Buhari inda Buharin yace ba gaskiya bane. Hakan ya bayyana ne a sabon Littafin da aka rubuta da ya kunshi tarihin rayuwar tsohon shugaban kasar wanda aka kaddamar a fadar shugaban kasa jiya.
Nasan Comedy(Wasan Barkwanci) Hàràmùn ne amma ba zan daija yi ba>>Sale Naci

Nasan Comedy(Wasan Barkwanci) Hàràmùn ne amma ba zan daija yi ba>>Sale Naci

Duk Labarai
Dan wasan barkwanci, Sale Naci ya bayyana cewa yasan abinda yake yi Haramun ne amma ba zai taba dainawa ba. Yace hakane bayan da wani Boka yace zai bashi tallar bokancin da yake ya tayashi tallatawa zai biyashi daga Miliyan 10 zuwa sama. Saidai Sale Yace ba zai karbi wannan tallar ba. https://www.tiktok.com/@sulenaci_/video/7584114589726559496?_t=ZS-92GY12TS1s9&_r=1
Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda wani Ladani ya rika nina Maqogoronsa yayin da yake Alhinin Abinda ya faru da ladanin Hotoro

Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda wani Ladani ya rika nina Maqogoronsa yayin da yake Alhinin Abinda ya faru da ladanin Hotoro

Duk Labarai
Wannan wani Ladani ne da ya nuna Makogoronsa a yayin da yake Alhinin rasuwar Ladanin Hotoro wanda aka cirewa Makogoro. Ladanin ya baiwa 'yan uwansa Ladanai shawarar su rika shiga Masallaci da makami yayin da suka je kiran Sallah. Hakanan kuma ya Yace Ladanai su rika kulle kofofin Masallaci yayin da suke kiran Salah. https://www.tiktok.com/@shugaba_tv1/video/7584208558418398485?_t=ZS-92GRMDQt7Vg&_r=1
Kalli Hoton Wanda ya kawo damuwa a masallacin Hotoro jiya

Kalli Hoton Wanda ya kawo damuwa a masallacin Hotoro jiya

Duk Labarai
Wannan shine hoton wanda ake zargin ya yanke Maqogoron Ladani a masallacin Hotoro dake Kano. Rahotanni sun ce tuni mutane shima suka taru suka shèkyèshi kuma an je an kona gidansu. Hakaan Rahotanni sun ce ba dan Najeriya bane dan kasar Chadi ne chirani suka zo Najeriya. https://www.tiktok.com/@abis_fulani/video/7584218871389850902?_t=ZS-92GOLK0HB6u&_r=1 https://www.tiktok.com/@harun.shalele/photo/7584172216699325716?_r=1&_t=ZS-92GPCHgIKDh https://www.tiktok.com/@muhammadyahaya573/video/7584036450144898322?_t=ZS-92GPJOifNKL&_r=1
Kalli Bidiyon: Ni Kirista ce, Na yi bincike na gano cewa Jesus yana Sallah shiyasa na Musulunta

Kalli Bidiyon: Ni Kirista ce, Na yi bincike na gano cewa Jesus yana Sallah shiyasa na Musulunta

Duk Labarai
Wannan wata Kirista ce data Musulunta, ta bayyana cewa abu na farko daya fara jan hankalinta kan Addinin Musulunci shine yanda ta fahimci cewa musulmai sun yadda da Annabi Isa (AS). Tace ta ci gaba da bincike inda daga baya ta gano cewa, Jesus yayi Sallah amma gashi Kiristoci basa yi. Tace dan haka ne yasa ta Musulunta. https://twitter.com/A_Y_Rafindadi/status/2000553931500585139?t=yhb2-45JaS_e3ksy0AVWew&s=19