Da Duminsa: Babban Bankin Najeriya, CBN ya soke lasisin bankin Heritage Bank da kuma kulle bankin
Babban bankin Najeriya, CBN ya sanar da soke lasisin bankin Heritage Bank da kuma kulle bankin.
Babban Darakta a CBN, Hakama Sidi Ali, ne ya bayyana hakan inda yace an dauki wannan mataki ne dan tsaftace harkar banki da kuma karawa mutane kwarin gwiwar yadda da tsarin banki a kasarnan.
Ya kara da cewa bankin na Heritage Bank ya kasa fitar da bayanai kan yanda yake gudanar da ayyukansa dan ganin ya ci riba ko ya fadi.
Sannan an bashi damar farfadowa daga matsalar da yake ciki amma lokaci me tsawo ya wuce bankin bai nuna alamar farfadowa ba dan hakane CBN ta ga cewa kawai abu magi a'ala shine rufe bankin.
CBN ta kara da cewa hukumar (NDIC) wadda ke baiwa kudaden Al'umma dake banki kariya ta hanyar Inshora ce zata kula da yadda za'a kulle bankin.
CBN yace yana baiwa 'yan Najeri...