Monday, November 23
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyon: Gidan mu musulmai ne, kakana Musulmi ne kakata ma musulmace, amma ‘ya’yan gidan mu an bar kowa ya zabi addinin da yake so yayi>>Inji Davido

Kalli Bidiyon: Gidan mu musulmai ne, kakana Musulmi ne kakata ma musulmace, amma ‘ya’yan gidan mu an bar kowa ya zabi addinin da yake so yayi>>Inji Davido

Duk Labarai
Tauraron mawakin Najeriya, Davido ya bayyana cewa gidansu musulmai ne kakansa namiji musulmi ne hakanan kakarsa mace musulmace. Yace amma kowa a gidansu babu wanda aka takurawa, an bar mutum yayi addinin da yake so. Ya bayyana hakane a wani Bidiyo inda ake masa tambayar addininsa. https://www.tiktok.com/@.gg6114/video/7636448762239864084?_r=1&_t=ZS-97OSEuUVMka
Kalli Bidiyon: Wannan matar da ta cinye kwanuka 5 na abinci a wajan taron jana’iza ta jawo cece-kuce

Kalli Bidiyon: Wannan matar da ta cinye kwanuka 5 na abinci a wajan taron jana’iza ta jawo cece-kuce

Duk Labarai
Wata mata ta janyo cece-kuce bayan data nuna abinci kala-kala data ci a wajan jana'izar Tauraron fina-finan kudu Alexx Ekubo da ya rasu. Matar dai ta dauki Bidiyon abinci kala-kala sun kai 5 wanda taci a wajan jana'izar. Hakan ya jawo cece-kuce inda wasu da yawa ke cewa ita bama jana'izar ce ta kaita wajan ba. https://twitter.com/i/status/2068420705281040482
Da Duminsa: Matan Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai dake tsare a hannun gwamnati sun bayyana wani mummunan abu da Gwamnati ta musu

Da Duminsa: Matan Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai dake tsare a hannun gwamnati sun bayyana wani mummunan abu da Gwamnati ta musu

Duk Labarai
Matar Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Asia El-Rufai ta yi zargin cewa an yiwa wayarta data abokiyar zamanta, Aichatou kutse. Ta bayyana hakane a shafin ta na sada zumunta inda tace suna zargin Gwamnati, Kuma duk abinda ya samesu, gwamnati ce sila. Ta bayyana cewa an musu kutse ana saka ido akan abubuwan da suke aikatawa. Hakan na zuwane yayin da mijinsu ke can hannun jami'an tsaro ana tuhumarsa kan zarge-zargen daban-daban.
Kalli Bidiyon: Tauraron fina-finan Amurka, Giancarlo Esposito ya musulunta

Kalli Bidiyon: Tauraron fina-finan Amurka, Giancarlo Esposito ya musulunta

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Tauraron fina-finan Amirka, Giancarlo Esposito ya karbi Musulunci. Tauraron wanda yayi suna a fim din Breaking da sauransu an ganshi yana sallah a wani Bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta. https://twitter.com/i/status/2068483303082967191 Rahotanni sun ce ya musulunta ne a kasar Saudiyya yayin da suke daukar wani fim kuma an yi sallah dashi.
Kalli Bidiyon: Hotal ne suke zagaye da Ka’aba me yasa ba’a cewa mutane iskanci suka je yi acan?>>Nafisa Abdullahi

Kalli Bidiyon: Hotal ne suke zagaye da Ka’aba me yasa ba’a cewa mutane iskanci suka je yi acan?>>Nafisa Abdullahi

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa, Hotals ne suka zagaye Ka'aba kuma ana shiga otal din maza da mata. Tace me yasa mutanen dake zuwa can ba'a musu kallon sun je yin iskanci ne sai su a Najeriya? Nafisa ta bayyana hakane a hirarta da Nasiru Ali Koki. https://www.tiktok.com/@eeeshaofficial/video/7653649246943481108?_r=1&_t=ZS-97O96rAa54R
Kalli Bidiyon: Ni ke daukar nauyin tsohuwar matar Gfresh Al-amin, watau Maryam Nicki Minaj, kuma ni ke bata kudi, zan aureta ne aure na har abada>>Inji Hassan Make-Up

Kalli Bidiyon: Ni ke daukar nauyin tsohuwar matar Gfresh Al-amin, watau Maryam Nicki Minaj, kuma ni ke bata kudi, zan aureta ne aure na har abada>>Inji Hassan Make-Up

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Hassan Make-Up ya bayyana cewa shine ke daukar dawainiyar tsohuwar matar Gfresh Al-amin watau Maryam Nicki Minaj. Yace kuma shine ke bata kudi. Sannan yace zai aureta aure na har abada. https://www.tiktok.com/@officielhassanmakeup227/video/7653429765688265991?_r=1&_t=ZS-97O6tLkyyna Tuni dai Maryam itama ta yi reposting din wannan Bidiyon na Hassan Make-Up inda suke kiran junansu da kalaman soyayya. https://www.tiktok.com/@maryamnickim/video/7653455290666388756?_r=1&_t=ZS-97O7YoZOHhg
Kalli Bidiyon: Bayan da Nafisa Abdullahi ta ce bature zata aura, an gano cewa tana soyayya da wani bature kirista

Kalli Bidiyon: Bayan da Nafisa Abdullahi ta ce bature zata aura, an gano cewa tana soyayya da wani bature kirista

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa idan ma zata yi aure, to ba zata auri Bahaushe dan Najeriya ba. Bature zata aura, musamman saboda sakawa mata ido da Hausawa kan yi su hanasu walwala. Saidai a cikin hirar, wanda yake hirar da ita ya nemi cewa, dan Allah idan ta tashi auren ta auro musulmi baturen. https://www.tiktok.com/@eeeshaofficial/video/7653151238220942613?_r=1&_t=ZS-97Mp7R89mTq