Muhammad Sanusi II ya goyi bayan zalunci a Kaduna>>Inji Shehu Sani
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya goyi bayan zalunci a jihar Kaduna.
Sanata Sani ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumuntar Twitter.
Sani yace Sarki Muhammad Sanusi II yana yakar zalunci a jihar Kano amma kuma a baya ya goyi bayan zaluncin a jihar Kaduna.
Sarki Sanusi dai abokine a wajan Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai kuma a lokacin da aka cireshi daga mukamin sarkin Kano, ya koma Kaduna inda El-Rufai ya bashi waje ya bude fada sannan kuma ya bashi mukami a jami’ar jihar Kaduna.