Thursday, January 9
Shadow

Duk Labarai

Rahotanni sun ce, Israela ta kashe Falasdinawa 50 a wani mummunan hari data kai Rafah, Kalli Bidiyon yanda mutane suka kone kurmus

Rahotanni sun ce, Israela ta kashe Falasdinawa 50 a wani mummunan hari data kai Rafah, Kalli Bidiyon yanda mutane suka kone kurmus

Duk Labarai, Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Rahotanni sun nuna yanda Israela ta kai wani mummunan hari a wajan sansanin 'yan gudun Hijira dake Rafah. Harin yayi sanadiyyar wuta ta tashi a sansanin inda mutane akalla 50 suka kone kurmus. An ta ganin gawarwakin mutane sun kone ana zakulosu a bidiyon da suke ta yawo a shafukan sada zumunta. Saidai hakan na zuwane bayan da kotun majalisar dinkin Duniya ta baiwa Israelan umarnin daina kai hari Rafah: https://twitter.com/CensoredMen/status/1794815544425873773?t=YnxpkOAzQnE8MDsF5KvKOg&s=19 https://twitter.com/syylllia/status/1794855529753506121?t=vZml1Ho1zA4AK7Yvdj7yew&s=19 https://twitter.com/jacksonhinklle/status/1794824350195167660?t=5qymwlqoX0GFP57gJcujrQ&s=19 Abin jira a gani shine wane mataki majalisar dinkin Duniyar zata dauka tunda dai gashi I...
Hoto: Sojojin Najeriya sun kai samame inda suka kashe ‘yan ta’adda 6 a Kaduna

Hoto: Sojojin Najeriya sun kai samame inda suka kashe ‘yan ta’adda 6 a Kaduna

Tsaro
Sojojin Najeriya sun kai samame maboyar 'yan ta'adda a Jihar Kaduna inda suka kashe guda 6. Sojojin sun yiwa 'yan Bindigar kwatan baunane inda suka kashesu tare da kwace makamai da yawa a hannunsu. Lamarin ya farune bayan da sojojin suka samu bayanai akan ayyukan 'yan Bindigar a kananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari ranar Friday, May 24, 2024. Sojojin sun je hanyar da 'yan Bindigar zasu wuce inda suka musu kwantan bauna, suna zuwa kuwa suka afka musu. An yi bata kashi sosai inda daga baya 'yan Bindigar suka tsere:
Mulkin Tinubu ya saka ‘yan Najeriya cikin matsananciyar Wahala>>Obasanjo

Mulkin Tinubu ya saka ‘yan Najeriya cikin matsananciyar Wahala>>Obasanjo

Duk Labarai, Siyasa
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, Mulkin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya jefa 'yan Najeriya cikin wahala. Ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 26 ga watan Mayu. Ya bayyana cewa, Gwamnatin Tinubu ta dauki matakai 3 wanda 2 dolene amma ba'a daukesu yanda ya kamata ba. Yace Gwamnatin Tinubu ta dauki matakin cire tallafin man fetur da kuma na dala. sannan sai kuma shiga lamarin juyin mulkin kasar Nijar. Yace gyaran tattalin arziki ba'a yinshi dare daya. Yace dolene sai an dage, yace idan aka dauki matakan da suka dace, cikin shekaru 2 Najeriya zata iya daukar saiti. Ya bayar da misalin yanda kamfanin Total Energy suka zagaye Najeriya suka je kasar Angola suka zuba jarin dala biliyan 6. Obasanjo yace maganar gaskiya dole a f...

Sunayen maza masu dadi

Duk Labarai, Ilimi
Kuna neman sunayen maza masu dadi? Gasu kamar haka: Bashir Ahmad Muhammad Aminu Abubakar Aliyu Umar Usman Haidar Lukman Faisal Fa'izu Fawaz Sani Yunus Yahya Isa Musa Zakariyya Sulaiman Yakubu Abdulrahman Abdullahi Abdulshakur Walid Jafnan Jawad Salisu Salim Sha'aban Zilkiflu Zannurain Yusuf Yasa'a Tukur Lawal Garba Bala Buba Mannir Mansir Jamilu Junaidu Haruna Khalid Huzaifa Rabi'u Ibrahim Ubaida Gali Inuwa Sama'ila Ma'aruf Izuddin Saifullahi Abbas Anas Rufa'i Khalifa Zakari Abdulhadi
Masoya Aminu Ado Bayero sun yi Sallar Rokon Allah ya dawo dashi kan sarautar Kano

Masoya Aminu Ado Bayero sun yi Sallar Rokon Allah ya dawo dashi kan sarautar Kano

Duk Labarai, Kano
Masoya tsohon sarkin Kano, Aminu Ado Bayero sun yi Sallah inda suka roki Allah ya dawo dashi kan sarautar Kano. Ranar Alhamis ne dai majalisar Kano ta soke dokar data kirkiro masarautu 4 a Kano sannan ta sauke Aminu Ado Bayero inda aka dawo da tsohon Sarki, Muhammad Sanusi II kan karagar Sarautar. Saidai Aminu Ado ya koma Kano inda ya je gidan Nasarawa ya kafa fadarsa acan, kuma masoyansa sun mai maraba. An ga masoyan Tsohon sarkin da yawa suna Sallah inda suke rokon Allah ya dawo dashi kan karagar sarautar Kano.
Bidiyo Da Duminsa: Zanga-zanga ta barke a Kano inda ake kone-konen Tayoyi

Bidiyo Da Duminsa: Zanga-zanga ta barke a Kano inda ake kone-konen Tayoyi

Duk Labarai, Kano
Zanga-zanga ta barke a Kano kan rikicin sarautar da ya faru a jihar. An ga wasu matasa dauke da kwalaye inda suke ihun basa so. An kuma ga an kunnawa taya wuta a karkashin wata fastar Abba da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. https://twitter.com/daily_trust/status/1794756398351356238?t=lWt28qaBdF9DMh57LPzSgw&s=19 Daily Trust ta wallafa bidiyon wanda ya nuna abinda ke faruwa. A wani bidiyon kuma an ga matasan na kabbara: Jaridar dai tace matasan dake zanga-zanga suna neman a sake dawo da Sarki, Aminu Ado Bayero ne kan karagar Mulkin Kano: https://twitter.com/daily_trust/status/1794760364070187113?t=-yPmQeNl8DbliJ5gkTzO7Q&s=19 Lamari dai ya kazancene bayan da Aminu Ado Bayero ya dawo Kano kuma ya sauka a gidan sarki dake Nasarawa.
Karanta Jadawalin Daraktoci 14 da CBN suka kora daga aiki

Karanta Jadawalin Daraktoci 14 da CBN suka kora daga aiki

Duk Labarai
Wadannan Daraktocine da babban bankin Najeriya, CBN ya kora daga aiki su 14. A kwanannan ne dai aka samu rahoton cewa, CBN din ta kori ma'aikata 200 da suka hada da manya da kanana. Clement Oluranti Buari, Director, Strategy Management Dr Blaise Ijebor, Director, Risk Management Lydia Ifeanyichukwu Alfa, Director, Internal Audit Jimoh Musa Itopa, Director, Capacity Development Muhammad Abba, Director, Human Resources Rabiu Musa, Director, Finance Dr Mahmud Hassan, Director, Trade & Exchange Dr Ozoemena S. Nnaji, Director, Statistics Dr Omolara Duke, Director, Financial Markets Chibuike D. Nwaegerue, Director, Other Financial Institutions Supervision Chibuzo A. Efobi, Director, Payments System Management Haruna Bala Mustafa, Director, Financial Pol...