Saturday, January 11
Shadow

Duk Labarai

Za mu ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da suka zama dole – Tinubu

Za mu ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da suka zama dole – Tinubu

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da bijiro da sauye-sauyen "da suka zama dole" domin gina ƙasar. Tun daga hawa mulkinsa wata 19 da suka gabata, an ga yadda Tinubu ya cire tallafin mai, ya sauya kasuwar canjin kuɗaɗen waje, ya gabatar da sabbin dokokin haraji, ya ƙaddamar da tallafin karatu, ya ƙara mafi ƙanƙantar albashi. "Za mu ci gaba da bijiro da sauye-sauyen da suka zama dole domin tabbatar da cigaba mai ɗorewa da yalwa a ƙasarmu," in ji shi cikin saƙonsa na sabuwar shekara. "Muna kan hanya mai kyau ta gina Najeriya wadda za ta kyautata wa kowa da kowa. Kada mu bari wasu 'yan tsirari daga cikinmu da ke amfani da siyasa da addini da ƙabilanci su kawar da hankalinmu."
Wahalhalun ‘yan Najeriya ba za su tashi a banza ba – Tinubu

Wahalhalun ‘yan Najeriya ba za su tashi a banza ba – Tinubu

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce wahalhalu da "sadaukarwar" da 'yan ƙasar suka yi ba su tashi a banza ba tun bayan hawa mulkinsa a watan Mayun 2023. Da yake bayani cikin saƙonsa na sabuwar shekara da fadar shugaban ƙasa ta fitar, Tinubu ya ce sabuwar shekarar "za ta kusanta mu da kakkyawar Najeriya da muke ta hanƙoro". A cewarsa: "Gare ku 'yan ƙasa, sadaukarwar da kuka yi cikin wata 19 da suka wuce ba ta tashi a banza ba. Ina tabbatar muku cewa kuma ba za ta tashi a banza ba nan gaba. Mu ci gaba da aikin gina ƙasa tare." Tinubu ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta ƙara mayar da hankali wajen aiwatarwa da kuma "bijiro da sauye-sauyen da suka zama wajibi" domin haɓaka tattalin arzikin Najeriya
Ya kamata Tinubu ya janye ƙudurin dokar haraji – NLC

Ya kamata Tinubu ya janye ƙudurin dokar haraji – NLC

Duk Labarai
Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, NLC ta buƙaci shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya janye ƙudurin dokar haraji da ya gabatar ga majalisar dokokin ƙasar domin bayar da dama kan sake yin nazari. Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a cikin saƙonta na sabuwar shekara, wanda shugabanta Joe Ajaero ya fitar a yau Laraba. Saƙon ya ce “domin samar da tsarin dimokuraɗiyya mai tabbatar da ci gaban ƙasa, dole ne mu gina tsari kan tubalin tattaunawa, da bai wa masu ruwa da tsaki damar tsoma baki a harkar gina ƙasa. “A kan haka ne muke sake yin kira ga gwamnatin tarayya da ta janye ƙudurin harajin da yanzu haka ke a gaban Majalisar dokoki domin bai wa duk ɓangarorin da suka dace bayar da gudumawa a kansa”. Sanarwar ta ce ƙungiyar, ita ma za ta so ta taimaka wajen samar da kyakkyawan tsarin haraji wanda zai ...
Laraba ce 1 ga watan Rajab a Najeriya – Fadar sarkin Musulmi

Laraba ce 1 ga watan Rajab a Najeriya – Fadar sarkin Musulmi

Duk Labarai
Fadar Sarkin Musulmi a Najeriya ta ayyana yau Laraba 1 ga watan Janairu a matsayin 1 ga watan Rajab na shekarar Hijira ta 1446. Wata sanarwa da Wazirin Sokoto Farfesa Sambo Wali ya fitar a daren da ya gabata ta ce Sarkin Musulmi Sa'ad Abubukar III ne ya bayyana hakan bayan ganin jaririn watan. Rajab shi ne wata na bakwai a kalandar Musulunci, wanda Hausawa ke yi wa laƙabi da watan Azumin Tsofaffi.
PDP ta nemi Tinubu ya yi bincike kan tiriliyan 25 da ta zargi ‘yan APC da sacewa

PDP ta nemi Tinubu ya yi bincike kan tiriliyan 25 da ta zargi ‘yan APC da sacewa

Duk Labarai
Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta PDP ta nemi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙaddamar da bincike kan kuɗaɗe naira tiriliyan 25 da ta zargi 'yan jam'iyyarsa ta APC da sacewa. PDP ta yi wannan kira ne a saƙon da ta wallafa na sabuwar shekara, wanda kakakinta na ƙasa Debo Ologuagba ya sanya wa hannu ranar Talata. "Ya kamata shugaban ƙasa ya wanke kansa game da yaƙi da cin hanci da rashawa ta hanyar ba da umarnin yin bincike da kuma dawo da sama da tiriliyan 25 da aka ce shugabannin APC da jami'an gwamnati sun sace," in ji sanarwar. Jam'iyyar ta kuma nemi shugaban ya bayyana adadin kuɗaɗen da gwamnatinsa ta tara daga cire tallafin man fetur da ya yi a watan Mayun 2023. Haka nan, PDP ta nemi Tinubu ya kawo ƙarshen matsalar tsaro, da yunwa, da kuma ƙarancin man fetur "domin sauƙaƙa ...
Direba ya kashe Amurkawa 10 da motarsa yayin bikin sabuwar shekara

Direba ya kashe Amurkawa 10 da motarsa yayin bikin sabuwar shekara

Duk Labarai
Aƙalla mutum 10 ne suka mutu a birnin New Orleans da ke Amurka lokacin da wata mota ta kutsa cikin dandazon mutane da asubahin ranar farko ta sabuwar shekara. Aƙalla mutum 35 ne suka samu rauni a lamarin. Ƴansanda sun ce wani mutum ne ya tuƙa wata motar a-kori-kura a guje cikin dandazon mutane a guje, da niyyar kaɗe mutane da dama. Haka nan direban motar ya buɗe wuta kan ƴansanda bayan motar tasa ta tsaya, lamarin da ya sa ya raunata jami'ai biyu. Wani jami'in Hukumar bincike ta FBI ya ce an kuma samu wani abu da ake zaton abin fashewa ne a wurin da lamarin ya faru, sai dai ya ce ba hari ba ne na ta'addanci - duk kuwa da cewa magajin garin birnin ya yi zargin hakan. An gargadi mutane su ƙaurace wa wurin da lamarin ya faru.
Harin da ya kashe mutum 10 a New Orleans ba na ta’addanci ba ne – FBI

Harin da ya kashe mutum 10 a New Orleans ba na ta’addanci ba ne – FBI

Duk Labarai
Jami'ar hukumar tsaro ta FBI a Amurka, Alethea Duncan, ta ce ta karɓe ragamar bincike kan harin da wani direba ya kai wa masu bikin sabwar shekara a birnin New Orleans. Yayin jawabin da ta yi, ta ce "wannan ba harin ta'addanci ba ne", abin da ya saɓa da kalaman magajin garin. Zuwa yanzu ba a san dalilin da ya sa aka samu mabambantan bayanai ba game da lamarin da ya jawo mutuwar mutum 10. Duncan ta ce akwai yiwuwar wani abin fashewa da aka gano a wurin kuma ana binciken gano gaskiyar hakan. Ta ce mutane za su ƙaurace wa wurin "har sai mun gano abin da ke faruwa".
Ƙasashen Nijar, Mali da Burkina za su kafa tashar talabijin

Ƙasashen Nijar, Mali da Burkina za su kafa tashar talabijin

Duk Labarai
Kafofin yaɗa labarai a Nijar da Mali da Burkina Faso sun ruwaito a ranar Litinin cewa ƙasashen za su kafa wata tashar talabijin ta intanet da zimmar "ƙarfafa haɗin kai da kuma yaƙi da labaran ƙarya" a yankinsu na Sahel. Ƙasashen uku da sojoji ke mulki, sun kafa ƙawance da suka kira Alliance of Sahel States, wanda suke kira da Aes a Faransanci. "Ana sa ran tashar za ta inganta harkokin sadarwa tsakanin ƙasashen Sahel kuma a samu tasiri mai ɗorewa bisa muradin shugabannin ƙasashen biyu," in ji rahoton shafin Actu Niger. An ƙulla ƙawancen ne a 2023 bayan sun sanar da aniyarsu ta ficewa daga ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas, wadda suka zarga da yi wa ƙasashen Yamma aiki. Nijar da Mali da Burkina duka sun yanke alaƙa da ƙasashen Yamma kamar Faransa...
Sojojin Najariya sun ce sun kashe ‘yan Bindiga 10,937 da kama guda 12,538 a shekarar 2024

Sojojin Najariya sun ce sun kashe ‘yan Bindiga 10,937 da kama guda 12,538 a shekarar 2024

Duk Labarai
Sojojin Najaria sun bayyana gagarumar nasarar da suka samu a shekarar 2024 inda suka ce sun kashe 'yan Bindiga guda 10,937 inda suka kama guda 12,538. Kakakin sojin Major General Edward Buba ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar yayin ganawa da manema labarai a Abuja inda yake bayani kan ayyukan da sojojin suka gudanar a shekarar 2024. Hakanan yace sojojin sun kubutar da jimullar mutane 7,063 da aka yi garkuwa dasu. Sannan aun kwace jimullar makamai 8,815 da Albarusai 228,004.