Friday, May 15
Shadow

Duk Labarai

Allah Sarki Kalli Bidiyon hirar tsohon dan wasan Arsenal, Emmanuel Eboue wanda ya auri baturiya, saidai yanzu yace ta rabashi da ‘ya’yanshi sannan ta kwace duka kadarorin da ya mallaka

Allah Sarki Kalli Bidiyon hirar tsohon dan wasan Arsenal, Emmanuel Eboue wanda ya auri baturiya, saidai yanzu yace ta rabashi da ‘ya’yanshi sannan ta kwace duka kadarorin da ya mallaka

Duk Labarai
Tsohon dan wasan Arsenal, Emmanuel Eboue ya koka da maganar hanashi mu'amala da 'ya'yansa da matarsa ta yi. Matarsa dai 'yar kasar Belgium ce kuma a lokacin da yake ganiyarsa ya aureta, saboda rashin Ilimi ya mika mata ragamar komai na kudinsa. Saidai ta yi amfani da wannan dama wajan arzuta kanta ta mallakawa kanta duka kadarorinsa har kotu aka shiga amma ita tayi nasara sannan kotu ta bata damar kula da 'ya'yansu. Yace a yanzu ta hanashi ganawa da 'ya'yan nashi kuma yana da lambarsu, zai aika musu da sako amma ba zasu aika masa da amsa ba. https://twitter.com/i/status/2047596617172144593
Ya fita wajan cin abinci da Budurwarsa ta ci abincin Naira Miliyan 1 a zama daya

Ya fita wajan cin abinci da Budurwarsa ta ci abincin Naira Miliyan 1 a zama daya

Duk Labarai
Wani me hada mata da maza masu neman aure ya koka da wata da ya hadata da wani mutum. Yace ya hadata da mutumin ne inda a ranar farko da suka fita taci abincin Naira 200,000. Yace a rana ta biyu da suka fita ta kawo abokanta 4 inda suka ci abincin Naira 1,053,000. Saurayin yace zai biya kaso 70 cikin 100 na kudin su kuma su biya sauran amma suka kiya. Daga baya dai saurayin ya tafi ya barsu sai da aka rike motar daya daga cikinsu a gidan abincin.
Siyasa Mugun wasa:Kalli Bidiyon yanda wasu maza suka Tumurmushe wata mata a wajan taron siyasa a Kano

Siyasa Mugun wasa:Kalli Bidiyon yanda wasu maza suka Tumurmushe wata mata a wajan taron siyasa a Kano

Duk Labarai
Bidiyon wajan wani taron siyasa a Kano inda aka ga wata mata a tsakiyar maza tana tafiya da kyar ya dauki hankula. A Bidiyon wasu sun rika kokarin baiwa matar kariya amma da yake mutane sun yi yawa, haka aka rika kutsawa da ita tsakanin mutane ba dadi. Da yawa dai sun ce siyasa ba ta mata bace. https://twitter.com/i/status/2047605175267799168
Kalli Bidiyon: An baiwa wani direba sakon wayar iPhone 16 ta Naira Miliyan 1.2 ya kaiwa wani soja amma ya tsere da wayar, saidai aun bibiyeshi har gida suka kamashi a gaban matarsa

Kalli Bidiyon: An baiwa wani direba sakon wayar iPhone 16 ta Naira Miliyan 1.2 ya kaiwa wani soja amma ya tsere da wayar, saidai aun bibiyeshi har gida suka kamashi a gaban matarsa

Duk Labarai
Wannan wani Direba be da aka kama ya gudu da wayar iPhone 16 da aka bashi ya kaiwa wani soja. Saidai an bibiyeshi har cikin gidan matarsa aka kamashi a gaban matar tasa A cewarsa wai wani abokinshi ya sace wayar. https://twitter.com/i/status/2047539617977549303
Kalli Bidiyon: Suma wasu iyaye a Arewa sun sake yiwa ‘ya’yansu Bikin Birthday da aka kashe kudi sosai, saidai Abinda yafi daukar hankula shine kayan da mahaifiyar yaran ta saka, da yawa sun ce ta nuna tsyraici

Wasu iyaye sun sake bayyana a Arewa inda suka shiryawa 'ya'yansu bikin Birthday Party da aka kashe makudan kudade. Hakan na zuwane bayan da a baya aka yi shigen wannan wanda har Davido aka gayyato. Saidai a wannan karin, abinda yafi daukar hankali shine shigar mahaifiyar yaran. Da yawa sun ce shigarta bata dace ba dan ta nuna tsiraici. https://www.tiktok.com/@danmasanistudioo/video/7631512589347851528?_r=1&_t=ZS-95n3pBMn0oy