Friday, March 20
Shadow

Duk Labarai

Da Duminsa: EFCC na neman Timipre Sylva ruwa a jallo

Da Duminsa: EFCC na neman Timipre Sylva ruwa a jallo

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC na neman tsohon karamin Ministan man fetur kuma tsohon Gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva ruwa a jallo. EFCC a wata sanarwa data fitar tace tana neman Sylva ne bayan umarnin wata kotu a Legas ranar 6 ga watan Nuwamba inda ake zarginshi da yin canjin Dala $14,859,257 ba bisa ka'idaba. EFCC tace duk wanda ya ganshi ya gaggauta sanar da ofishinta mafi kusa ko kuma ofishin 'yansanda. Timipre dai ne ake zargin ya dauki nauyin yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Jhuyin mulki wanda aka dake a kwanannan.
Ya kamata jami’o’i masu zaman kansu su shiga ASUU – Shugaban NLC

Ya kamata jami’o’i masu zaman kansu su shiga ASUU – Shugaban NLC

Duk Labarai
Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC, Joe Ajaero ya yi kira da a janyo jami'o'in Najeriya masu zaman kansu su shiga cikin ƙungiyar ASUU. Ajaero ya buƙaci ƙungiyar ASUU ta fara tattaunawa da shugabannin jami'o'in na Najeriya domin fahimtar da su buƙatar shiga ƙungiyar domin a gudu tare a tsira tare, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. Ajaero ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a lokacin da yake jawabi a lokacin da aka tattaunawa da shugaban ASUU, Farfesa Christopher Piwuna a shirin Toyin Falola. Shugaban na NLC ya ce "dole a daina cin zarafi tare da yi wa mambobin ASUU," in ji shi, sannan ya bayyana mamakinsa kan yadda gwamnatin ta gaza wajen tabbatar da alƙawarin da ta sa hannu tun a shekarar 2009. Ya ce asali an ƙirƙiri ASUU ne domin raba kan NLC, sanan a ...
Abin na min Takaici matuka idan aka ce wai in an kama Tsageran dashi a kare hakkinsa na Bil’adama, Kawai ni a nawa ra’ayin a shyekye dan banza dan baiwa amfani>>Inji Sanata Ali Ndume

Abin na min Takaici matuka idan aka ce wai in an kama Tsageran dashi a kare hakkinsa na Bil’adama, Kawai ni a nawa ra’ayin a shyekye dan banza dan baiwa amfani>>Inji Sanata Ali Ndume

Duk Labarai
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa, Abin takaici ne matuka yanda wai idan aka kama 'yan tà'àddà dake Khashewa da Gharkuwa da mutane da yiwa mata fyade ace wai suna da wani hakki na bil'adama da za'a kare musu. Sanata Ndume yace ai kawai irin wadannan Khashyesu kawai ya kamata a yi. Yace su ina hakkin mutanen da suke lalatawa rayuwa? Sanata Ndume ya bayyana hakane a wata hira da yayi da manema labarai wadda ta watsu sosai a kafafen sada zumunta. https://twitter.com/TheBeninBlogger/status/1987744772480479397?t=okCmVbbFFDvvJDAX1_fP7Q&s=19
Na bar Gidanmu ina da kananan Shekaru sosai kuma banda Ko Sisi amma yanzu Allah ya min daukaka da Arziki>>Inji Rahama Sadau

Na bar Gidanmu ina da kananan Shekaru sosai kuma banda Ko Sisi amma yanzu Allah ya min daukaka da Arziki>>Inji Rahama Sadau

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta bayyana cewa tana da kananan shekaru sosai ta bar gidansu ta shiga harkar film a lokacin bata da ko sisi. Tace Amma cikin Ikon Allah sai gata ta samu Daukaka da Arziki har ta dauki wasu aiki. Ta bayyana hakane a wani Bidiyo inda take karfafa 'ya'ya mata su bi burin zuciyarsu sannan su nuna jajircewa. https://www.tiktok.com/@rahamasadaufanspage0/video/7570452687980907794?_t=ZS-91HlFZW2Ajp&_r=1
Wallahil Azim Buhari ya zo min a mafarki, da fararen kaya da Dogon gashi, Fuskarsa cike da annuri yace min ya gode da addu’o’in da nake masa>>Inji tsohuwar Hadimar Buhari, watau Baby Buhari

{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wata tsohuwar hadimar tsohon shugaban kasa da ake kira da Beby Buhari ta yi ikirarin cewa, Marigayi tsohon shugaban kasar ya bayyana gareta a mafarki. Ta wallafa a shafinta na X cewa, ta ga Buhari a mafarki da fararen kaya da Dogon gashi fuskarsa cike da annuri yace mata ya gode da addu'o'in da take masa. Tace lamarin ya bata mamaki matuka. https://twitter.com/baby_done1/status/1987806516519309398?t=wN6Xt6jDkyTdHmi-dqnabw&s=19
Bharazanar Trump tasa mun gane wadanda basa kishin kasa da Munafukan cikinmu>>Inji Sheikh Gumi

Bharazanar Trump tasa mun gane wadanda basa kishin kasa da Munafukan cikinmu>>Inji Sheikh Gumi

Duk Labarai
Malamin addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa, Barazanar da shugaban kasar Amurka, Donald Trump yawa Najeriya tasa an gano marasa kishin kasa da Makiya. Ya bayyana hakane a shafinsa na Facebook. A baya dai malam yayi kira ga Shugaba Trump da ya janye kalamansa akan Najeriya sannan kuma ya bayar da hakuri inda yace Shugaba Tinubu ya yanke hulda da Amirka idan Trump din yaki yin hakan.
Na yi mafarkin an sake yin Muslim Muslim a Najeriya, El-Rufai ya zama shugaban kasa, Rauf Aregbesola ya zama mataimakinsa>>Inji Dan majalisa, Nuhu Sada

Na yi mafarkin an sake yin Muslim Muslim a Najeriya, El-Rufai ya zama shugaban kasa, Rauf Aregbesola ya zama mataimakinsa>>Inji Dan majalisa, Nuhu Sada

Duk Labarai
Tsohon Dan majalisa na majalisar jihar Kaduna daya wakilci Zaria, Hon. Nuhu Sada ya bayyana cewa, idan yayi mafarki, mafarkin yakan zama gaskiya. Yace kuma yayi mafarkin tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya zama shugaban Najeriya kuma Rauf Aregbesola ya zama mataimakinsa.
Shugaban Amurka Trump yace zai yi Amfani da kudaden Harajin da ya samu daga kasashen Duniya wajan rabawa ‘yan kasar Dala $2000 kowannensu

Shugaban Amurka Trump yace zai yi Amfani da kudaden Harajin da ya samu daga kasashen Duniya wajan rabawa ‘yan kasar Dala $2000 kowannensu

Duk Labarai
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, zai Rabawa mutanen kasarsa dala $2000 kowanne daga kudin Harajin da ya tara daga hannun kasashen Duniya. Ya bayyana hakane a shafinsa na Truth social inda yace kasarsa ce kasa da aka fi girmamawa a tsakanin kasashen Duniya Sannan ya yi alkawarin yin amfani da kudin Harajin wajan biyan bashin da ake bin kasar Amurka. Saidai da yawa 'yan kasar ta Amurka na shakka akan wannan ikirari nasa.