Saturday, December 13
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyo: Gidana ya hadu sosai ta yanda babu bangaren da zaka kalla kace ni Talaka ne>>Inji Naziru Sarkin Waka

Kalli Bidiyo: Gidana ya hadu sosai ta yanda babu bangaren da zaka kalla kace ni Talaka ne>>Inji Naziru Sarkin Waka

Duk Labarai
Tauraron Mawakin Hausa, Naziru Sarkin Waka ya bayyana cewa, gidansa ya hadu sosai ta yanda babu bangaren da mutum zai kalla yace shi talaka ne. Naziru ya kara da cewa, shi Allah ya yishi mutum ne me son ,aman gida dan haka ya kayata gidansa yanda ya kamata. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi. https://www.tiktok.com/@naziru.sarkin.wak443/video/7533212900316417286?_t=ZS-8yUjw0kOVQf&_r=1
Sabon Rikici: Tsohon Mataimakin shugaban jam’iyyar ADC, Nafi’u Bala ya fito yace shine sabon shugaban jam’iyyar ba David Mark ba

Sabon Rikici: Tsohon Mataimakin shugaban jam’iyyar ADC, Nafi’u Bala ya fito yace shine sabon shugaban jam’iyyar ba David Mark ba

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar ADC, Nafi’u Bala wanda kuma dan takarar gwamna ne na jam'iyyar a jihar Gombe ya fito yayi ikirarin cewa shine ahugaban riko na jam'iyyar. Ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar da tsakar dare. Yace ba zasu amince da David Mark a matsaykn shugaban jam'iyyar na riko ba inda yace an karya doka da aka baiwa wadanda ba asalin 'yan jam'iyyar ragamar shugabancin jam'iyyar ba. Hakan na zuwane bayan da aka mikawa David Mark shugabancin jam'iyyar na riko.
Da Duminsa: Shugaba Tinubu ya karawa shugaban Kwastam wa’adi

Da Duminsa: Shugaba Tinubu ya karawa shugaban Kwastam wa’adi

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya karawa shugaban Kwastam, Bashir Adeniyi yawan wa'adinsa. Me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis. Sanarwar tace shugaban kwastam din, Mr. Bashir Adewale Adeniyi, MFR ya kamata ya ajiye aiki nan da 31 ga watan Augusta 2025. Amma an kara masa wa'adi zuwa shekara daya. Sanarwar tace an kara masa wa'adinne dan ya ci gaba da ayyukan gyara Najeriya sannan shugaba Tinubu ya yaba da aikinsa.
Gwamnati ta fara yiwa ‘yan ADC tayin Mukamai dan su yi watsi da jam’iyyar

Gwamnati ta fara yiwa ‘yan ADC tayin Mukamai dan su yi watsi da jam’iyyar

Duk Labarai
Tsohon shugaban jam'iyyar Hadakata ta ADC, Ralph Nwosu ya bayyana cewa Gwamnatin tarayya ta masa tayin mukamin Minista har sau 3 dan ya bar jam'iyyar amma yaki. Ya bayyana hakane a ranar Talata a yayin da aka mikawa David Mark shugabancin jam'iyyar a hukumance. Yace kokarin na gwamnati yana son dakile kaifin duk wasu 'yan adawa ne dan mayar da Najeriya tsarin tafarkin jam'iyya daya. Yace an masa tayin kujerar Minista guda 3 ne dan ya dauki daya yayi kyauta da guda 2. Saidai yace ya zabi Dimokradiyyar Najeriya da ci gabanta. Ya kara da cewa, Najeriya ba zata zama kasa me jam'iyya daya ba bayan kokarin da aka yi na ganin an kawar da tsarin mulkin kama karya na soja. Yace tun bayan bayyana hadakatar 'yan Adawa a jam'iyyar ta ADC membobin jam'iyyar sun karu zuwa mutane Miliyan...
Idan Peter Obi ya dawo PDP ya tsaya takarar shugaban kasa, babu wani dan takara daga Arewa da zai iya kayar dashi>>Inji Farfesa Jerry Gana

Idan Peter Obi ya dawo PDP ya tsaya takarar shugaban kasa, babu wani dan takara daga Arewa da zai iya kayar dashi>>Inji Farfesa Jerry Gana

Duk Labarai
Farfesa Jerry Gana ya bayyana cewa idan Peter Obi ya koma PDP ya tsaya takarar shugaban kasa, babu dan takarar shugaban kasa daga Arewa da zai iya kayar dashi. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi. Yace suna kan kokarin ganin sun jawo hankalin Peter Obi ya klma jam'iyyar su ta PDP. Yace kuma bayan Peter Obi din, akwai wani ma wanda yafi Peter Obi nagarta da karbuwa da suke kokarin kawowa PDP ya musu takara.
Wata Sabuwa: Kalli Bidiyon yanda Mai Wushirya ya yiwa wasu ‘yan Tiktok da ‘yan Kannywood dake Màdìgò tonon Silili, yace ko sallah basa yi

Wata Sabuwa: Kalli Bidiyon yanda Mai Wushirya ya yiwa wasu ‘yan Tiktok da ‘yan Kannywood dake Màdìgò tonon Silili, yace ko sallah basa yi

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Mai Wushirya ya yiwa wasu jaruman Kannywood da Tiktok mata wankin babban bargo inda ya zargi cewa suna lashe junansu. Ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa da ya watsu sosai inda aka ga yana cewa ko Sallah basa yi. Yace maza na kokarin neman na kansu su je su auresu amma sun lalata rayuwarsu har anko suke yi. Saidai har yayi ya gama fadansa bai kira suna ba. https://www.tiktok.com/@maiwushiryabackup/video/7532988026306186502?_t=ZS-8yTvjLes4nZ&_r=1 Hakan na zuwane yayin da kafar Tiktok din ta dauki dumi ake cece-kuce aka wani fada da ya barke a tsakanin wasu jarumai da ake zargi da Madigo.
Gwamnoni na farin ciki da cire tallafin man fetur kuma in ku baku jin dadi, su suna jin dadin cire tallafin>>Inji Me magana da yawun shugaban kasa, Daniel Bwala

Gwamnoni na farin ciki da cire tallafin man fetur kuma in ku baku jin dadi, su suna jin dadin cire tallafin>>Inji Me magana da yawun shugaban kasa, Daniel Bwala

Duk Labarai
Me magana da yawun shugaban kasa, Daniel Bwala ya bayyana cewa, Gwamnonin Najeriya na jin dadin cire tallafin man fetur da aka yi. Yace a yanzu babu Gwamnan da baya iya biyan ma'aikatan jiharsa Albashi. Yace maimakon a baya wanda gwamnoni kusan sama da 20 ne basa iya biyan Albashi. Daniel Bwala ya bayyana hakane a yayin zantawar da aka yi dashi a gidan Talabijin na chan TV. Ya kuma ce gwamnonin a yanzu suna samun kudaden gudanar da ayyuka a jihohinsu ba kamar a baya ba.
Akwai yiyuwar in koma jam’iyyar APC, dan majalisa, Abdulmumin Jibrin bayan ganawa da Shugaba Tinubu

Akwai yiyuwar in koma jam’iyyar APC, dan majalisa, Abdulmumin Jibrin bayan ganawa da Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Dan majalisar tarayya daga jihar Kano, Abdulmumin Jibrin ya gana da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a jiya. Bayan ganawar tasu a yayin da yake ganawa da manema labarai an tambayeshi ko haka na nuna cewa zai koma APC ne? Sai ya kayar da baki yace Yanzu ba lokacin wannan maganar bane, ya je ya gaishe da shugaba Tinubu ne sannan aun gana akan lamuran kasa, saidai yace abune mai yiyuwa ya iya komawa APC din. Ya kara da cewa hadin kai da zaman lafiyar Najeriya shine gaba da komai kuma ba abin mamaki bane ganinsa a fadar shugaban kasar.
Ku Daina Zagin Mahaifinsa in kuna yi bana jin dadi>>Inji Dan Gidan tsohon Gwamnan Kaduna, Bashir El-Rufai

Ku Daina Zagin Mahaifinsa in kuna yi bana jin dadi>>Inji Dan Gidan tsohon Gwamnan Kaduna, Bashir El-Rufai

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Dan Gidan Tsohon Gwamnan Kaduna, Bashir El-Rufai ya roki mutane da su daina zagin mahaifinsa inda yace idan ana yi baya jin dadi. Bashir Ya bayyana hakane a shafinsa na X. https://twitter.com/BashirElRufai/status/1950779372383723541?t=jVCVrXrS5CNdm0pMP-44Ng&s=19 Malam Nasiru Ahmad El-Rufai na daga cikin 'yan siyasar da suka fi shan suka a Najeriya.