Friday, February 27
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyon: Shima Dan Tiktok, Auwal ya musuluntar da Wadda suke wasan Barkwanci tare, Christy ta koma Fatima

Kalli Bidiyon: Shima Dan Tiktok, Auwal ya musuluntar da Wadda suke wasan Barkwanci tare, Christy ta koma Fatima

Duk Labarai
Dan Tiktok me wasan Barkwanci, Auwal ya musuluntar da wadda suke wasan Barkwanci tare me suna Christy ta koma musulma inda ta zabi sunan Fatima. A Bidiyon da ya wallafa, an ganshi inda suka je masallaci tare da ita. Sannan itama ta tabbatar da cewa, da gaskene ta karbi Addinin Musulunci. https://www.tiktok.com/@auwal.44/video/7559721807893368082?_t=ZS-90ViIEMEJ0L&_r=1
Kalli Bidiyon: Na kasa Fahimtar me nene Shugaban Kungiyar Izala, Bala Lau yace suna tare da Malam Lawal Triumph akai, Kalaman batancin da yayiwa Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ko mene?>>Sheikh Farfesa Ibrahim Maqari ya bayyana

Malamin Addinin Islama, Sheikh Farfesa Ibrahim Maqari ya bayyana cewa, yana mamakin kalaman da Shugaban Izala, Sheikh Bala Lau yayi da yace suna tare da Malam Lawal Triumph. Malam Maqari ya bayyana cewa, abinda ya bashi mamaki shine shin wai akan me Izala take tare da Malam Lawal Triumph akan kalaman batancin da yawa Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ko mene?. Malam ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa da ya dauki hankula sosai inda yake cewa Ibn Taimiyya yace girmama Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) da kambamashi shine ke nuna tsayuwar Addini. https://www.tiktok.com/@hassan.a.hassan.2/video/7559949237786512652?_t=ZS-90VfCQzDGTY&_r=1
Rahotanni sunce Shugaba Tinubu ya fara neman wanda zai nada a matsayin sabon Ministan kudi, bayan da Ministan Kudi Wale Edun ya samu rashin lafiyar Shanyewar rabin jiki

Rahotanni sunce Shugaba Tinubu ya fara neman wanda zai nada a matsayin sabon Ministan kudi, bayan da Ministan Kudi Wale Edun ya samu rashin lafiyar Shanyewar rabin jiki

Duk Labarai
Rahotanni sun ce tuni shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fara neman wanda zai maye ministan Kudi, Wale Edun dashi. Ministan Kudi, Wale Edun ya kwanta rashin lafiya bagtatan inda rahotanni suka ce shanyewar rabin jiki ce ta kamashi. Rahotannin sun ce an garzaya dashi zuwa kasar waje. Hakanan rahotannin sun ce ko da ya warke da wuya ya iya komawa bakin aikinsa. Wannan ne yasa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fara meman wanda zai maye gurbinsa dashi. Rahotanni sun ce Shugaba Tinubu ya baiwa Gwamnan Babban bankin Najeriya, CBN umarnin maye gurbin Ministan kudin a wai taro da za'a yi a kasashen waje.
Ji yanda matar aure a Arewa ta yi yaji saboda Mijinta yana bata Dubu dari a wata a matsayin kudin Cefane,tace sun yi kadan

Ji yanda matar aure a Arewa ta yi yaji saboda Mijinta yana bata Dubu dari a wata a matsayin kudin Cefane,tace sun yi kadan

Duk Labarai
Wata matar aure a Arewa ta yi yaji saboda tace mijinta yana cutar da ita saboda 'ya'yansu 2 amma sai ya rika bata kudin cefanane Tace yana ajiye kayan abinci kamar buhun shinkafa da man girki, amma sai ya bata Naira 100,000 wanda baya isanta yon cefane. Akan hakane suka yi fada ta tafi gidansu. https://twitter.com/_hafsat_paki/status/1977371222385029269?t=NsYHM3ZBZ_rvBAvum_wEbQ&s=19
Wannan wani Gawurtaccen Me Shatar mutanene dan neman kudin fansa wanda yana cikin wadanda shugaba Tinubu yawa afuwa

Wannan wani Gawurtaccen Me Shatar mutanene dan neman kudin fansa wanda yana cikin wadanda shugaba Tinubu yawa afuwa

Duk Labarai
Kelvin Oniarah Ezigbe dan shekaru 44 na daga cikin mutanen da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yawa afuwa. Shugaban wasu gungun 'yan fashine dake garkuwa da mutane An zargeshi da hannu a kisan Sojoji da 'yansanda da dama. An yanke masa hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari saidai saboda nuna nadama da yayi, an rage shekarun zuwa 13.
Da Duminsa: Cutar Shanyewar Rabin jiki ta kama Ministan kudin Najeriya an garzaya dashi asibitin kasar waje

Da Duminsa: Cutar Shanyewar Rabin jiki ta kama Ministan kudin Najeriya an garzaya dashi asibitin kasar waje

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, cutar Shanyewar rabin jiki ta kama Ministan Kudi, Wale Edun inda aka garzaya dashi zuwa asibitin kasar waje Sahara reporters ta bayyana cewa, lamarin yayi tsanani anma yana samun kulawa ta musamman a asibitin da aka kaishi. Rahotan yace ministan yana aiki da yawa ba tare da hutu ko cin abinci yanda ya kamata ba wanda ake ganin hakan ya taimaka sosai wajan rashin lafiyar tasa. Rahoton yace Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Cordoso ne aka wakilta ya maye gurbin ministan zuwa wani babban taron kudi da za'a yi a kasashen waje. Rahoton yace ko da ministan ya warke da wuya ya koma bakin aikinsa inda rahotanni suka ce tuni shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fara neman wanda zai nada a matsayin sabon Ministan kudin. rahoton yace fadar shugaban kasa t...
Da Duminsa: Kungiyar Malaman Jami’a ta ASUU ta tsunduma yajin aikin gargadi na sati biyu

Da Duminsa: Kungiyar Malaman Jami’a ta ASUU ta tsunduma yajin aikin gargadi na sati biyu

Duk Labarai
Ƙungiyar malaman jami'a a Najeriya Asuu ta bai wa mambobinta umarnin fara yajin aiki daga gobe Litinin na tsawon mako biyu. Academic Staff Union of Universities (Asuu) ta ce yajin aikin na gargaɗi ne bayan cikar wa'adin da suka bai wa gwamnatin Najeriya a watan Satumban da ya gabata. Shugaban Asuu Farfesa Chris Piwuna ya faɗa yayin taron manema labarai a Abuja cewa matakin ya zama dole "saboda gazawar gwamnatin wajen biyan buƙatunmu".
Da Duminsa: Tinubu zai tafi Italiya yau Lahadi

Da Duminsa: Tinubu zai tafi Italiya yau Lahadi

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tnubu zai kama hanyar zuwa Italiya a yau Lahadi domin halartar taron Aqaba na shugabannin ƙasashe kan tsaro. Fadar shugaban ƙasar ta ce taron Aqaba Process Heads of State and Government Level Meeting zai mayar da hankali kan matsalar tsaro a Afirka ta Yamma. "Za a fara taron ranar 14 ga watan Oktoba, wanda zai haɗa shugabannin ƙasa, da shugabannin soji daga Afirka domin tattauna ƙalubalen tsaro a Afirka ta Yamma," in ji sanarwar da fadar ta fitar ranar Asabar da dare. Sarkin Jordan Abdullah II ne ya ƙaddamar da taron a 2015 domin yaƙi da ta'addanci, wanda Masarautar Jordan da gwamnatin Italiya ke gudanarwa, a cewar sanarwar. "Shugaba Tinubu zai tattauna da wasu shugabanni a gefen taron domin lalubo hanyoyin magance matsalar tsaro a yankin," kamar yadda fa...