Monday, March 23
Shadow

Duk Labarai

Shin da Gaske Sheikh Isa Ali Pantami ya koma jam’iyyar ADC? Ji bayani dalla-dalla

Shin da Gaske Sheikh Isa Ali Pantami ya koma jam’iyyar ADC? Ji bayani dalla-dalla

Duk Labarai
Rahotanni nata yawo a kafafen sada zumunta cewa babban malamin Addinin Islama, Sheikh Isa Ali Pantami ya koma jam'iyyar ADC daga jam'iyyar APC. A kwanannan dai ana ta ganin shuwagabannin jam'iyyun siyasa na ta zawarcin Pantami inda suke kai masa ziyara gida. Lamarin ya dauki hankula inda ake ta muhawara masu zafi. Saidai har yanzu shi Pantami ko wata kafa me zaman kanta bata fito ta tabbatar da komawarsa jam'iyyar ADC ba.
Da Duminsa: WhatsApp zasu daina Amfani da lambar waya inda zasu koma amfani da Username kamar sauran Social Media

Da Duminsa: WhatsApp zasu daina Amfani da lambar waya inda zasu koma amfani da Username kamar sauran Social Media

Duk Labarai
Manhajar sada zumunta ta WhatsApp zasu daina amfani da lambar waya wajan gane mutum. WhatsApp zasu koma amfani da Username inda hakan wani mataki ne na baiwa mutane sirri. Tuni Rahotanni suka bayyana cewa, an fara gwajin hakan amma ba'a bayyanashi ga sauran Al'umma ba. Nan gaba kadanne ake tsammanin kowa zai fara amfani da wannan sabon tsari da zarar an kammala gwajinsa.
Ana Binciken karamin yaro me shekaru 17 saboda sayen fili Hectares dubu goma sha hudu (14,000 Hectares) a jihar Edo

Ana Binciken karamin yaro me shekaru 17 saboda sayen fili Hectares dubu goma sha hudu (14,000 Hectares) a jihar Edo

Duk Labarai
Gwamnan jihar Edo Monday Okpebholo ya sanar da cewa suna binciken wani karamin yaro me shekaru 17 bayan da ya sayi filaye masu girman Hectares dubu goma sha hudu(14,000 Hectares). Yaron dai ya biya kudin filayen da ya siya. Gwamnan yace suna binciken inda matashin ya samu wadannan kudade. Sannan yace an dakatar da C of O da akewa filayen da yaron ya siya.
Da Duminsa: Majalisar kasar Peru ta tsige shugabar kasar biyo bayan Shekye mutane sama da dubu shidda a kasar

Da Duminsa: Majalisar kasar Peru ta tsige shugabar kasar biyo bayan Shekye mutane sama da dubu shidda a kasar

Duk Labarai
Majalisar kasar Peru ta tsige shugabar kasar me suna Dina Boluarte saboda yawaitar kisa a kasar. Rahotanni sun ce majalisar ta gayyaci shugabar kasar da ta gurfana a gabanta amma ta ki amsa gayyatar da aka mata. Dalili kenan ranar 10 ga watan Oktoba aka tsigeta. Yawan mutanen da aka kashe a kasar tsakanin watan Janairu zuwa tsakiyar watan Augusta sun kai mutane 6000. Duka 'yan majalisar 124 sun amince da tsige shugabar kasar ba tare da ko guda daya yace bai yadda ba. Shugaba Dina Boluarte ce aka bayyana wadda tafi bakin jini a Duniya.
Wada Mutuniyar Maiwushirya tace taga an daina mata like da comment da share a videos din da take yi, dan haka tana neman a dawo a ci gaba da yi dan darajar Annabi(sallallahu Alaihi Wasallam)

Shahararriyar Wada wadda suka rika sheke aya tare da Idris Mai Wushirya ta bayyana cewa ta ga an daina mata likes da comment da kallon Bidiyon da take wallafawa. Tace tana nema dan darajar Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) a dawo a ci gaba da yi mata. Ta bayyana hakane a wani Bidiyon ta da ya watsu sosai kuma hakan na zuwane bayan da aka kama abokin burmin nata watau mai wushirya inda yake can a tsare. Kalli Bidiyon jawabinta anan
Kalli Bidiyo: Ni a wajena babu Malamin da na taba ji ya Zhaghi Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)>>Inji Aminu J Town

Kalli Bidiyo: Ni a wajena babu Malamin da na taba ji ya Zhaghi Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)>>Inji Aminu J Town

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Aminu J. Town ya bayyana cewa, shi duk takaddamar da ake yi, bai taba jin wani malami ya zaghi Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba. Yace matsalar 'yan Izala itace rashin Nuna Ladabi yayin magana akan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) Su kuma 'yan Darika abu ko da na karyane indai na bajintane aka jingina na Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) sai su tabbatar da shi. J. Town yace, Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba sai an yi karya akan karamarshi ba, duk abinda zaka fada akanshi ya wuce nan. https://www.tiktok.com/@aminujtown/video/7559332568961649938?_t=ZS-90QTwlfi5Ev&_r=1
Kalli Bidiyo: Yayin da ake tsare da Maiwushirya, Wadar sa suke Bidiyon tare ta samu wani sun ci gaba

Kalli Bidiyo: Yayin da ake tsare da Maiwushirya, Wadar sa suke Bidiyon tare ta samu wani sun ci gaba

Duk Labarai
A yayin da shahararren dan Tiktok, Maiwushirya ke can a tsare a jihar Kano, saboda Bidiyon da ya rika yi da wata wada yana kamata. Ita kuwa tuni ta samu wani sun ci gaba da Bidiyon tare. Rahotanni sunce jami'an tsaro na neman wadar ruwa a jallo inda ta yi batan dabo. Saidai Kwatsam sai gata an ganta a wani Bidiyo ta ci gaba da harkokinta abinta. https://www.tiktok.com/@pharooq_/video/7555264629266468097?_t=ZS-90QQW2hzkqf&_r=1
Kalli Bidiyon: Tauraruwar Tiktok wadda a baya Bidiyon Tsyrycinta ya bayyana har Hisbah suka kamata, a yanzu ma ta sake sakin Bidiyon da ya nuna tsyrycinta da ya jawo cece-kuce sosai

Kalli Bidiyon: Tauraruwar Tiktok wadda a baya Bidiyon Tsyrycinta ya bayyana har Hisbah suka kamata, a yanzu ma ta sake sakin Bidiyon da ya nuna tsyrycinta da ya jawo cece-kuce sosai

Duk Labarai
Tauraruwar Tiktok, Hafsat Baby wadda a baya Bidiyon tsiraicinta ya bayyana wanda har sai da Hisbah suka kamota ta sake sakin Bidiyon da ya nuna tsiraicinta. Sabon Bidiyon data dora a shafinta na Tiktok ya nuna ta sanye da kaya shara-shara da cikinta a waje. Saidai ta kulle comment inda hakan ya hanata mutane damar bayyana ra'ayoyinsu akan Bidiyon nata. Saidai duk da haka an rika Tafka Muhawara akan Bidiyon. https://www.tiktok.com/@hafsatbaby011/video/7557806942962355467?_t=ZS-90PwUPfYlQP&_r=1