Sunday, January 12
Shadow

Duk Labarai

Kasar Nijar ta koro karin ‘yan Najeriya 392 zuwa gida

Kasar Nijar ta koro karin ‘yan Najeriya 392 zuwa gida

Duk Labarai
Kasa da mako daya bayan da kasar Nijar ta dawo da 'yan Najeriya su 310 zuwa gida Najeriya, kasar ta sake taso keyar wasu karin mutane 392 zuwa Najeriya. Hakan ya kawo jimullar 'yan Najeriya da aka dawo dasu gida daga kasar Nijar zuwa 702 a cikin sati daya. Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki a lamarinne suka tarbi 'yan Najeriyar da aka koro daga Nijar a Titin Airport Road dake Kano. Hukumar ta NEMA ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar ta shafinta na X.
Tsageran ESN Sun kashe sojojin Najeria biyu daya ya bace, sun kuma tsere da makaman sojojin

Tsageran ESN Sun kashe sojojin Najeria biyu daya ya bace, sun kuma tsere da makaman sojojin

Duk Labarai
Hukumar sojojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar sojojin ta 2 bayan harin da kungiyar ESN dake karkashin kungiyar IPOB ta kai mata. A sanarwar data fitar ranar Asabar, Hukumar sojojin ta bayyana cewa, lamarin ya farune a garin Osina dake karamar hukumar Ideator ta Arewa dake jihar Imo a yayin da wata tawagar sojojin ke dawowa daga wani dauki da suka kai a yankin Osina bayan kiran da aka musu cewa kungiyar ta ESN ta kai hari garin. Hakanan sanarwar tace sojojin sun fafata da ESN a yankin Nkwachi inda suka kashe mutum daya daga ciki sauran suka tsere sannan kuma an kwato bindiga daya aga hannunsu.
A karin Farko a Tarihi, Sunan Muhammad ya shiga cikin sunaye 10 na farko da aka fi sakawa Jarirai sabbin haihuwa a birnin New York City na kasar Amurka

A karin Farko a Tarihi, Sunan Muhammad ya shiga cikin sunaye 10 na farko da aka fi sakawa Jarirai sabbin haihuwa a birnin New York City na kasar Amurka

Duk Labarai
A karin farko a tarihin birnin New York na kasar Amurka, sunan Muhammad ya shiga cikin sunaye 10 na farko da aka fi sakawa jarirai sabbin haihuwa a birnin. Sunan Muhammad shine ya zo a matsayi na 9 da aka fi sakawa jarirai a birnin na new York city a shekarar 2023 da ta gabata. Ba a birnin New York City bane kadai aka fi sakawa jarirai sunan na Muhammad, hadda ma biranen kasar Ingila da Wales sunan Muhammad na kan gaba da aka fi sakawa jarirai sabbin haihuwa. Sunayen Emma da Liam ne suka fi shahara a birnin na New York City inda aka sakawa jarirai mata 382 sunan Emma sannan aka sakawa jarirai maza 743 sunan Liam. Wadannan sunaye sun dade suna a matsayi na daya na sunayen da aka fi sakawa jarirai maza da mata a birnin inda sunan Emma tun shekarar 2017 shine a matsayi na daya da ...
Bidiyon Wata Minista ya bayyana tsiràrà

Bidiyon Wata Minista ya bayyana tsiràrà

Duk Labarai
Bidiyon ministar mata da yara da tallafi ta kasar Fiji, MP Lynda Tabuya ya fita inda aka ganta tsirara haihuwar uwarta. Ministar tace wannan bidiyo ta yi shi ne ta aikawa mijinta amma bata da masaniyar yanda aka yi ya watsu a kafafen sada zumunta. Tuni dai Firaiministan kasar, Sitiveni Rabuka ya sauke ta daga mukaminta dalilin wannan badakala. Saiai tace ita bata aikata laifin komai ba dan kuwa mijinta ta aikawa bidiyon amma bata san yanda aka yi bidiyon ya watsu a kafafen sada zumunta ba. Ta gargadi masu watsa bidiyon da su yi hankali dan tasa a yi bincike dan gano wanda suka watsa shi kuma zata dauki hukuncin shari'a akansu. Mataimakin Kwamishinan 'yansandan kasar, Livai Driu ya bayyana cewa, suna kan binciken lamarin bayan korafin da Ministar ta kai musu.
Kasar Pakistan ta kaiwa Afghanistan hari inda mutane 46 suka mutu

Kasar Pakistan ta kaiwa Afghanistan hari inda mutane 46 suka mutu

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Pakistan na cewa, kasar Afghanistan ta kai mata hari da jiragen yaki na sama wanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 46. Wadanda suka mutun wanda yawanci matane da kananan yara kamar yanda gwamnatin kasar ta Afghanistan ta tabbatar. Hakanan akwai karin mutane 6 da suka mutu sanadiyyar karin wasu hare-haren da kasar ta Pakistan ta kai a kasar ta Afghanistan. Ma'aikatar harkokin kasashen waje ta Afghanistan tuni ta kira wakilin jakadan Pakistan dake kasarta inda ta yi Allah wadai da lamarin tare da shan Alwashin kai harin ramuwar gayya. Kafar Reuters tace kasar Pakistan ta kaiwa 'yan Bindigar TTP harine biyo bayan harin da suka kai a kudancin Waziristan daya kashe sojojin Pakistan din guda 16. TTP ta hada kai da Kungiyar Taliban amma tana kai harin...
Karanta Jadawalin Alkawuran da Gwamnatin Shugaba Tinubu ta yi wanda bata cikasu ba a shekarar 2024

Karanta Jadawalin Alkawuran da Gwamnatin Shugaba Tinubu ta yi wanda bata cikasu ba a shekarar 2024

Duk Labarai
A yayin da ya rage saura kwanaki kadan mu shiga shekarar 2024, mun kawo muku jadawalin alkawuran da Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta yi wadanda bata cikasu ba a wannan shekarar. Alkawarin cire haraji akan kayan Abinci Cire Haraji akan kayan Abinci dan samarwa talakawa hanyar saukin rayuwa abune da gwamatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta alkawarta ta bakin Ministan Noma, Abubakar Kyari. Yace za'a cire haraji akan Alkama, Shinkafa, Masara da sauransu dan samarwa mutane saukin rayuwa. A ranar 14 ga watan Augusta, Hukumar Kwastam ta sanar da izinin data samu daga fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dan cire tallafin. Hukumar kwastam tace cire harajin zai fara aiki ne daga 15 ga watan July zuwa 15 ga watan Disamba. Saidai da ba'a ga an cire harajin ba, an ...