An maka Dan Wike a gaban Kotu bisa zarcin cinye kudi dala Miliyan $2.1
Safwan Garba ya maka dan Ministan Abuja, Jordan Wike a Kotu kan cinye masa Kudi Dala Miliyan $2.1 watau kwatankwacin sama da Naira Biliyan biyu da dubu dari bakwai kenan 2.7Bn
Garba ya maka dan Ministan kara a gaban kotu inda yace sun hada kasuwanci dan gina Gidaje a Abuja.
Garba da yake gabatar da korafinsa a gaban Kotu yace a shekarar 2025 ne suka shirya shi da Dan Wike cewa shi dan Wike din zai kawo filaye a Abuja yayin da shi kuma zai kawo kudin da za'a gina filayen da suka kai dala Miliyan $4.2
Garba Yace dan Wike ya nuna masa wasu Filaye a Abuja yace anan ne zasu yi ginin gidajen inda yace zasu raba riba akan shi Garba ya rika karbar kaso 60 cikin 100 shi kuma dan Wike ya rika karbar Kaso 40 cikin 100.
Yace dan Wike ya rika baza masa wuta akan lalai ya bayar da kudin a fa...








