Mutane miliyan 31 za su faɗa ƙangin yunwa a Najeriya – MDD
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutum miliyan 31 ne ke fuskantar ƙarancin abinci a Niajeriya, wanda hakan ne mafi yawa a tarihi, sanadiyyar rage kudin tallafi da Amurka da sauran ƙasashen Yamma ke bayarwa.
Matsalar yunwar ta fi ƙamari ne a arewa maso gabashin ƙasar inda aka yi ƙiyasin cewa iyalai miliyan 2.3 suka tarwatse a cikin shekara 16 na rikicin Boko Haram.
A baya Amurka ce take bayar da kashi 60 cikin ɗari na tallafin jin-ƙai a Najeriya, sai dai shugaba Donald Trump ya dakatar da tallafin.
A yanzu ƙasashen Yamma sun mayar da hankali wajen kashe kudi kan tsaro sanadiyyar barazana daga Rasha.
A sanadiyyar haka, ala tilas Najeriya ta zabtare kudin da take kasaftawa na tallafin jin-ƙai daga dala miliyan 910 zuwa dala miliyan 300.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikici...








