Monday, March 2
Shadow

Duk Labarai

Da Duminsa: Wike ya bayyana cewa ranar 18 ga watan September Gwamnan Jihar Rivers, Simi Fubara da majalisar jihar zasu koma bakin aiki

Da Duminsa: Wike ya bayyana cewa ranar 18 ga watan September Gwamnan Jihar Rivers, Simi Fubara da majalisar jihar zasu koma bakin aiki

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa, nan da ranar 18 ga watan Satumba Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara zai koma bakin aikinsa tare da 'yan majalisar jihar. Wike ya bayyana hakane bayan ya kada kuri'ar sa a zaben kananan hukumomi da ake a jihar ta Rivers Ranar Asabar. Wike ya kada kuri'ar sa a rumfar zabe me lamba 7 a mazabar ,ward 9 dake yankin Rumuepirikom na karamar hukumar Obio-Akpor. Wike yace an yi zaben lami lafiya. Yace nan da ranar 18 ga watan Satumba mulkin karta kwana zai kare kuma Gwamnan jihar Simi Fubara da 'yan majalisar jihar zasu dawo bakin aiki
Mun warware matsalolin aure aƙalla 600 a shekara ɗaya – HISBAH

Mun warware matsalolin aure aƙalla 600 a shekara ɗaya – HISBAH

Duk Labarai
A jihar Kano, hukumar Hisba ta sanar da cewa ta warware korafe-korafe ko rigingimu tsakanin ma’aurata har dari shida da ashirin da daya cikin shekara daya. Mutuwar aure gagarumar matsala ce da ke shafar mutane, kama daga matan da ake saki da mazan da ‘ya’yan, sanadiyyar wani sabani ko rashin jituwa. Wannan dalili ne yasa hukumar ta HISBA ta ke kokarin sulhunta ma’aurata don su ci gaba da rayuwa cikin fahimtar juna tare da ‘ya’yansu.
Kalli Bidiyo: G-Fresh Al-amin ya baiwa Rotimi Amaechi tabbacin shi shahararren ne a Arewa kuma zai tallatashi gurin mutanen Arewa ya zama shugaban kasa a 2027

Kalli Bidiyo: G-Fresh Al-amin ya baiwa Rotimi Amaechi tabbacin shi shahararren ne a Arewa kuma zai tallatashi gurin mutanen Arewa ya zama shugaban kasa a 2027

Duk Labarai
Shahararren dan Tiktok, G-fresh Al-Amin ya bayyana cewa, tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi kuma tsohon Gwamnan jihar Rivers ya gayyaceshi a cikin shahararrun mutanen da yake son su tallatashi. A wani Bidiyo da Gfresh ya wallafa, an ganshi tare da Rotimi Amaechi yana bashi tabbacin cewa shi shahararrene kuma zai tallatashi a wajan 'yan Arewa. https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7543356208229469448?_t=ZS-8zIzDg6AOfp&_r=1 https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7544012668470889746?_t=ZS-8zJ0cQyFO0f&_r=1 Me zaku ce anan?
Ji Yanda ‘yansanda suka yi ta maza suka kashe Habu Dan Damisa duk da kokarin hanasu da wasu masu kumbar susa suka yi

Ji Yanda ‘yansanda suka yi ta maza suka kashe Habu Dan Damisa duk da kokarin hanasu da wasu masu kumbar susa suka yi

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Habu Dan Damisa da aka kashe ya mutu ne a hannun 'yansanda. Habu Dan Damisa sanannen dan daba ne dake kashe mutane da yi musu zalinci kala-kala amma saboda ana ganin yana da daurin gindi a wajan wasu 'yan siyasa yasa yaki tabuwa. Mutuwarsa ta zowa mutane da yawa da mamaki musamman jin cewa, a hannun 'yansandan ya mutu. Rahotanni sunce an yi kokarin hana 'yansanda kashe Dan Damisa amma suka ki sauraren wannan kiraye-kirayen musamman la'akari da irin barnar da yake yi a cikin al'umma suka aikashi lahira.
Kotu ta daure matasa 2 a gidan yari tsawon shekaru 5 saboda shirya yiwa Gwamnatin jihar Borno gàngàmì

Kotu ta daure matasa 2 a gidan yari tsawon shekaru 5 saboda shirya yiwa Gwamnatin jihar Borno gàngàmì

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Borno na cewa, Kotu ta daure wasu matasa 2 a gidan yari tsawon shekaru 5 saboda shirya yiwa Gwamnatin jihar Borno zanga-zanga. Matasan da aka daure sune Mohammed Bukar (Awana)da brahim Mohammed (Babayo). Rahoton yace mai shari'a Justice A.M Ali ne ya musu wannan hukunci ranar June 30, 2025. An samesu da laifin shirya yin zanga-zanga da daukar muggan makamai a kafar WhatsApp.

Goodluck Jonathan ba zai iya kayar da Bola Ahmad Tinubu zabe ba a 2027>>Inji APC

Duk Labarai
Jam'iyyar APC ta bayyana cewa, tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ba zai iya kayar da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zabe ba a 2027. Jam'iyyar APC reshen jihar Legas ce ta bayyana hakan ta bakin me magana da yawunta, Mr Seye Oladejo inda yace an wuce da irin siyasar da Goodluck Jonathan ya saba da ita Yace a tarihi idan aka tuna, Goodluck Jonathan ya bar Najeriya da matsaloli da yawa A shekarar 2015 ne dai Goodluck Jonathan ya sha kaye a hannun tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Ji yanda lauya ya maka Gwamnan jihar Legas a kotu saboda yayi blocking dinsa a shafin sada zumunta na X

Ji yanda lauya ya maka Gwamnan jihar Legas a kotu saboda yayi blocking dinsa a shafin sada zumunta na X

Duk Labarai
Lauya me rajin kare hakkin bil'adama, Festus Ogun ya maka gwamnan jihar Legas, Babajide Sonwo Olu a kotu saboda ya yi blocking dinsa a X. Lauyan ya gabatar da karanne a babbar kotun tarayya dake Legas. Ya nemi kotu tasa Gwamnan Legas ya cire Blocking din da yayi masa saboda hakan take hakkinsa ne a matsayinsa na zababben gwamna wanda aka zaba a turbar Dimokradiyya. Ya kuma nemi kotun data sanya Gwamnan Legas ya bashi hakuri.
Kalli Bidiyo: Ba’awa musulman kasarnan Adalci ba ace mu Kirista muna da hutu ranar Lahadi amma ranar Juma’a a rika zuwa aiki, ya kamata ranar Juma’a ta zama ranar hutu kamar ranar Lahadi>>Inji Reno Omokri

Kalli Bidiyo: Ba’awa musulman kasarnan Adalci ba ace mu Kirista muna da hutu ranar Lahadi amma ranar Juma’a a rika zuwa aiki, ya kamata ranar Juma’a ta zama ranar hutu kamar ranar Lahadi>>Inji Reno Omokri

Duk Labarai
Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri yace ya kamata a mayar da ranar Juma'a ranar hutu. Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da ya saki a shafinsa na sada zumunta. Yace babu adalci ace Kirista na da ranar Lahadi a matsayin ranar hutu amma ranar Juma'a ace sai an je aiki. Yace ko dai a mayar da ranar Juma'a ranar hutu ko kuma a rage awannij da ake aiki a ranar juma'ar a rika tashi daga aiki da karfe 12 na rana. https://twitter.com/renoomokri/status/1961430478516261340?t=Q9frzbRKhKR2XfcpMANTkA&s=19
Sanata Kabiru Marafa ya fice daga jam’iyyar APC, kalli Bidiyon jawabinsa

Sanata Kabiru Marafa ya fice daga jam’iyyar APC, kalli Bidiyon jawabinsa

Duk Labarai
Tsohon Dakta Janar na yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a jihar Zamfara Sanata Kabiru Marafa ya fice daga jam'iyyar APC. Tsohon Sanatan ya bayyana cewa watsi da waɗanda suka taimaki shugaba Tinubu na daga dalilin da yasa ya fice daga jam'iyyar. Wane fata zaku yi masa? https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1961314229559951402?t=a6UUyHaZzHPEwDWCm_jwkg&s=19
Me kamfanin sayar da mota yace zai baiwa Nafisa Abdullahi data lashe gasar Turanci ta Duniya kyautar Naira Dubu dari biyar

Me kamfanin sayar da mota yace zai baiwa Nafisa Abdullahi data lashe gasar Turanci ta Duniya kyautar Naira Dubu dari biyar

Duk Labarai
Me kamfanin sayar da motar Manga Motors ya sha Alwashin baiwa Nafisa Abdullahi data lashe gasar Turanci ta Duniya kyautar Naira 500,000. Hakan na zuwane bayan da gwamnatin tarayya ta baiwa Nafisa Abdullahi kyautar Naira 200,000 wanda hakan ya jawo cece-kuce. Da yawa dai na ganin kudin da Gwamnatin tarayya ta baiwa Nafisa sun yi kadan matuka musamman lura da cewa kwanannan aka baiwa 'yan kwallo mata kyautar dala $100,000 kowannensu.