Jihohin Arewacin Najeria ba su nuna aniyar yin rajistar zaɓe sosai ba a makon farko, Jihohin Kudu sun fi nuna Aniya
Bayanan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya - Inec - ta fitar kan alƙaluman makon farko na mutanen da suka nuna aniyar yin rajistar zaɓe ta intanet sun nuna cewa al'umma ba su fito sosai ba a yankin arewacin ƙasar domin yin rajistar.
Alƙaluman da hukumar ta Inec ta fitar a jiya Litinin sun nuna cewa jihar Osun ce ta fi yawan mutanen da suka nuna aniyar yin rajistar, inda take da yawan mutane 393,269, jihar Legas ke biye mata da mutum 222,205 sai kuma jihar Ogun mai yawan masu son yin rajista 132,823.
A arewacin Najeriya, Abuja, babban birnin tarayyar ƙasar ne ke da mafi yawan mutanen da suka nuna aniyar yin rajista, inda take da mutum 107,683, sai jihar Kaduna mai mutum 61,512 yayin da jihar Kogi ke biye mata da mutum 58,546.
...








