Monday, December 15
Shadow

Duk Labarai

An yiwa Alkalan Najeriya 10 ritayar dole bayan samunsu da rage shekaru dan ci gaba da aiki

An yiwa Alkalan Najeriya 10 ritayar dole bayan samunsu da rage shekaru dan ci gaba da aiki

Duk Labarai
Majalisar koli dake kula da harkar Alkalai ta Najeriya, NJC ta yiwa Alkalai 10 daga jihar Imo ritayar dole bayan samunsu da laifukan rage shekaru. Majalisar ta dauki wannan mataki ne bayan zaman da ta yi bisa jagorancin babbar Alkaliyar Najeriya, Justice Kudirat Kekere-Ekun. Sanarwar da majalisar ta fitar ranar Alhamis tace akwai alkalai 5 a babbar kotu da alkalai 4 a kotun Customary da aka samu da rage shekaru dan su ci gaba da aiki. Alkalan babbar kotun da aka cire sune M.E. Nwagboso, B.C. Iheka, K.A. Leaweanya, Chinyere Ngozi Okereke, da Innocent Chidi Ibeawuchi.  Daga kotun Customary kuma alkalan da aka cire sune, Tennyson Nze, Uchenna Ofoha, Everyman Eleanya, da Rosemond Ibe. Sannan An yiwa Wani alkali me suna Justice T.N. Nzeukwu ritaya saboda bayyana kansa a matsayin ...
‘Yan Najeriya na kashe Dala Biliyan $1.1 wajan zuwa Neman lafiya a kasashen waje duk shekara

‘Yan Najeriya na kashe Dala Biliyan $1.1 wajan zuwa Neman lafiya a kasashen waje duk shekara

Duk Labarai
Bankin African Export-Import Bank ya bayyana cewa, Najeriya na kashe Dala Biliyan $1.1 wajan neman magani da lafiya a kasashen waje duk shekara. Bankin yace hakan ba karamin koma baya bane ga ci gaban harkar Lafiya a Najeriya. Wakiliyar bankin, Mrs Oluranti Doherty ce ta bayyana hakan a Abuja a waja wani taro da aka yi ranar Alhamis. Tace ci gaba da dogaro da neman lafiya a kasashen waje na dakile zuba jari a bangaren Lafiya a Najeriya inda tace kuma hakan na yiwa gaba dayan harkar tattalin arzikin kasar illa.
Gwamnatin tarayya na sayar da kaso 80 na danyen man fetur din Najeriya ga kasashen waje yayin da Matatun man fetur din Najeriya irin na Dangote ke kukan rashin danyen man

Gwamnatin tarayya na sayar da kaso 80 na danyen man fetur din Najeriya ga kasashen waje yayin da Matatun man fetur din Najeriya irin na Dangote ke kukan rashin danyen man

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa kaso 82 cikin 100 na danyen ma da aka hako a Najeriya, kasashen waje ake sayarmawa inda ake sayarwa da matatun man fetur na cikin gida da sauran kason. Hakan na zuwane yayin da matatun man fetur din Najeriya irij na Dangote ke kukan rashin wadataccen danyen man da zasu tace. An samu wadannan alkaluma ne a watanni 3 na farkon shekarar 2025. Hukumar dake kula da lamarin, NUPRC ta bayyana cewa ganga Miliyan 1.57 ce aka hako a tsakanin watanni 3 din kuma an sayarwa da kasashen waje ganga Miliyan 1.29 inda aka sayarwa da matatun cikin gida ganga 280,000. Hukumar ta NUPRC tace wannan kaso da take sayarwa da matatun man cikin gida dan ta karfafa su ne, saidai matatar man fetur din Dangote tace tana dogaro da kasar Amurka ne wajan samun danyen man fetur.
Shugaban ‘yansandan Najeriya ya bayar da umarnin yin bincike kan zargin biyan dansanda Naira Miliyan 2 a matsayin kudin ritaya

Shugaban ‘yansandan Najeriya ya bayar da umarnin yin bincike kan zargin biyan dansanda Naira Miliyan 2 a matsayin kudin ritaya

Duk Labarai
Shugaban 'yansandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin yin bincike dan gano gaskiyar ikirarin wani tsohon dansanda da yace an biyashi Naira Miliyan 2 a matsayin kudin sallama. Hutudole ya ruwaito muku cewa, Bidiyon dansansan ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda ya jawo cece-kuce. Dansandan wanda yayi ritaya da mukamin Superintendent of Police yace ba zai karbi Naira Miliyan 2 ba saboda ta masa kadan bayan shafe shekaru 35 yana aiki a matsayin dansanda. Dansandan wanda yayi ritaya a watan October 1, 2023 yace hukumar kula da fansho na 'yansanda ta sanar dashi cewa kudin sallamarsa Naira Miliyan 2 ne sannan akwai Naira Miliyan daya ta bashin kudin fansho da yake bi. Kakakin 'yansandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi ya bayyana cewa, shugaban 'yansandan ya baya...
Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da wani shirin tabbatar da amfani da gas wurin girki ya shiga yankunan arewacin Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da wani shirin tabbatar da amfani da gas wurin girki ya shiga yankunan arewacin Najeriya

Duk Labarai
Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da wani shirin tabbatar da amfani da gas wurin girki ya shiga yankunan arewacin Najeriya. Karamin ministan man fetur na Najeriya, Ekperikpe Ekpo ne ya ƙaddamar da shirin yau Alhamis a garin Sokoto. Lokacin da yake jawabi a wurin ƙaddamar da shirin, gwamnan jihar Ahmed Aliyu ya ce matakin zai taimaka wajen rage dogaro kan amfani da itace a wajen girki, lamarin da ke cutar da muhalli musamman a jihohin Najeriya da ke iyaka da hamada. Sai dai ya buƙaci masu ruwa da tsaki su yi ƙoƙarin ganin farashin gas ɗin ya yi daidai da ƙarfin talaka. “Matuƙar ana so wannan shiri ya yi tasiri dole ne sai an samar da gas din LPG a wadace kuma cikin rahusa ga mutanen Najeriya masu matsakaicin karfi,” in ji gwamnan.
‘Yansanda a jihar Kano sun kama barayin a daidaita sahu su 4, an kwato keke Napep din sata 6 a hannunsu

‘Yansanda a jihar Kano sun kama barayin a daidaita sahu su 4, an kwato keke Napep din sata 6 a hannunsu

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan jihar Kano sun kama barayin a daidaita su 4. Kuma an kwato Keke Napep din sata guda 6 a hannunsu. Kakakin 'yansandan jihar, DSP Hussaini Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a sanarwar da ya fitar yau Alhamis. Yace a ranar 17 ga watan Yuni sun samu bayanan sirri kan wasu barayin adaidaita Namiji da mace, Auwal Mohammed, 'm', 30 wanda ke zaune a Hotoro, sai kuma Maryam Ibrahim, 'f', 25 wadda 'yar jihar Bauchi ce. Yace sun baiwa wani me adaidaita, Shu'aibu Aliyu kwaya suna kokarin kwace masa Keke Napep dinsa amma zuwan 'yansanda yasa basu yi nasara ba. Yace da bincike yayi tsanani an gano wani me suna Suleiman Lawal, wanda aka fi sani da Aljan da kuma Muhammad Tajuddeen, 'm', 32 wanda suke aiki tare dasu. Yace an kwato a daidaita 6 daga hannunsu kuma...
Najeriya ce ta daya wajan yawan mutanen da basu samun wutar lantarki a Duniya>>Inji Bankin Duniya

Najeriya ce ta daya wajan yawan mutanen da basu samun wutar lantarki a Duniya>>Inji Bankin Duniya

Duk Labarai
A sabon rahoton sa na shekarar 2025, bankin Duniya ya bayyana cewa, 'yan Najeriya Miliyan 86.8 ne ke cikin duhu basa samun wutar Lantarki a Najeriya. Bankin yace wannan shine mutane mafiya yawa da ya zarta na kowace kasar Duniya. Rahoton yace a cikin kasashen 20 da basa samun ingantacciyar wutar lantarki, guda 18 na Afrika ne. Rahoton yace kaso 60 cikin 100 na 'yan Najeriya ne ke samun wutar lantarki sannan kaso 26 cikin 100 na 'yan kasar ne ke amfani da makamashi me tsafta na girki.
Zan cika duka alkawuran da nawa ‘yan Najeriya >>Shugaba Tinubu

Zan cika duka alkawuran da nawa ‘yan Najeriya >>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa zai cika duka alkawuran da yawa 'yan Najeriya. Ya bayyana hakane a ziyarar aiki da ya kai jihar Nasarawa. Shugaban kuma ya bayar da tabbacin baiwa jihar Nasara gudummawar da take bukata wajan ci gaba musamman ta fannin ma'adanai da noma. Ya bayyana hakane yayin ziyarar da ya kaiwa Sarkin Lafiya,Sidi Bage Muhammad sannan ya jinjinawa Gwamna Abdullahi Sule game da ayyukan ci gaba da yayi a jihar.