Tuesday, March 31
Shadow

Duk Labarai

Kotu ta daure matasa 2 a gidan yari tsawon shekaru 5 saboda shirya yiwa Gwamnatin jihar Borno gàngàmì

Kotu ta daure matasa 2 a gidan yari tsawon shekaru 5 saboda shirya yiwa Gwamnatin jihar Borno gàngàmì

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Borno na cewa, Kotu ta daure wasu matasa 2 a gidan yari tsawon shekaru 5 saboda shirya yiwa Gwamnatin jihar Borno zanga-zanga. Matasan da aka daure sune Mohammed Bukar (Awana)da brahim Mohammed (Babayo). Rahoton yace mai shari'a Justice A.M Ali ne ya musu wannan hukunci ranar June 30, 2025. An samesu da laifin shirya yin zanga-zanga da daukar muggan makamai a kafar WhatsApp.

Goodluck Jonathan ba zai iya kayar da Bola Ahmad Tinubu zabe ba a 2027>>Inji APC

Duk Labarai
Jam'iyyar APC ta bayyana cewa, tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ba zai iya kayar da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zabe ba a 2027. Jam'iyyar APC reshen jihar Legas ce ta bayyana hakan ta bakin me magana da yawunta, Mr Seye Oladejo inda yace an wuce da irin siyasar da Goodluck Jonathan ya saba da ita Yace a tarihi idan aka tuna, Goodluck Jonathan ya bar Najeriya da matsaloli da yawa A shekarar 2015 ne dai Goodluck Jonathan ya sha kaye a hannun tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Ji yanda lauya ya maka Gwamnan jihar Legas a kotu saboda yayi blocking dinsa a shafin sada zumunta na X

Ji yanda lauya ya maka Gwamnan jihar Legas a kotu saboda yayi blocking dinsa a shafin sada zumunta na X

Duk Labarai
Lauya me rajin kare hakkin bil'adama, Festus Ogun ya maka gwamnan jihar Legas, Babajide Sonwo Olu a kotu saboda ya yi blocking dinsa a X. Lauyan ya gabatar da karanne a babbar kotun tarayya dake Legas. Ya nemi kotu tasa Gwamnan Legas ya cire Blocking din da yayi masa saboda hakan take hakkinsa ne a matsayinsa na zababben gwamna wanda aka zaba a turbar Dimokradiyya. Ya kuma nemi kotun data sanya Gwamnan Legas ya bashi hakuri.
Kalli Bidiyo: Ba’awa musulman kasarnan Adalci ba ace mu Kirista muna da hutu ranar Lahadi amma ranar Juma’a a rika zuwa aiki, ya kamata ranar Juma’a ta zama ranar hutu kamar ranar Lahadi>>Inji Reno Omokri

Kalli Bidiyo: Ba’awa musulman kasarnan Adalci ba ace mu Kirista muna da hutu ranar Lahadi amma ranar Juma’a a rika zuwa aiki, ya kamata ranar Juma’a ta zama ranar hutu kamar ranar Lahadi>>Inji Reno Omokri

Duk Labarai
Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri yace ya kamata a mayar da ranar Juma'a ranar hutu. Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da ya saki a shafinsa na sada zumunta. Yace babu adalci ace Kirista na da ranar Lahadi a matsayin ranar hutu amma ranar Juma'a ace sai an je aiki. Yace ko dai a mayar da ranar Juma'a ranar hutu ko kuma a rage awannij da ake aiki a ranar juma'ar a rika tashi daga aiki da karfe 12 na rana. https://twitter.com/renoomokri/status/1961430478516261340?t=Q9frzbRKhKR2XfcpMANTkA&s=19
Sanata Kabiru Marafa ya fice daga jam’iyyar APC, kalli Bidiyon jawabinsa

Sanata Kabiru Marafa ya fice daga jam’iyyar APC, kalli Bidiyon jawabinsa

Duk Labarai
Tsohon Dakta Janar na yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a jihar Zamfara Sanata Kabiru Marafa ya fice daga jam'iyyar APC. Tsohon Sanatan ya bayyana cewa watsi da waɗanda suka taimaki shugaba Tinubu na daga dalilin da yasa ya fice daga jam'iyyar. Wane fata zaku yi masa? https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1961314229559951402?t=a6UUyHaZzHPEwDWCm_jwkg&s=19
Me kamfanin sayar da mota yace zai baiwa Nafisa Abdullahi data lashe gasar Turanci ta Duniya kyautar Naira Dubu dari biyar

Me kamfanin sayar da mota yace zai baiwa Nafisa Abdullahi data lashe gasar Turanci ta Duniya kyautar Naira Dubu dari biyar

Duk Labarai
Me kamfanin sayar da motar Manga Motors ya sha Alwashin baiwa Nafisa Abdullahi data lashe gasar Turanci ta Duniya kyautar Naira 500,000. Hakan na zuwane bayan da gwamnatin tarayya ta baiwa Nafisa Abdullahi kyautar Naira 200,000 wanda hakan ya jawo cece-kuce. Da yawa dai na ganin kudin da Gwamnatin tarayya ta baiwa Nafisa sun yi kadan matuka musamman lura da cewa kwanannan aka baiwa 'yan kwallo mata kyautar dala $100,000 kowannensu.
Da Duminsa: Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa wai ba zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027 ba

Da Duminsa: Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa wai ba zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027 ba

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya musanta rahoton dake cewa ba zai tsaya takarar shugaban kasa ba a shekarar 2027. Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakane ta bakin dan uwansa, Azibaola Robert inda yace Jonathan bai ce zai tsaya takarar shugaban kasa ba ko ba zai tsaya ba. Hakan na zuwane yayin da PDP ke cewa tana son tsayar da ko dai Goodluck Jonathan ko Peter Obi takarar shugaban kasa a 2027. Rahotanni sun ce tuni Goodluck Jonathan ya fara tuntubar manyan mutane a kasarnan kan tsayawa takarar shugaban kasar.
Matatar man fetur ta Dangote tasa matatun man kasashen Turai dole suna kullewa saboda kasashen Afrika sun daina sayen man su, na Dangote suke saye

Matatar man fetur ta Dangote tasa matatun man kasashen Turai dole suna kullewa saboda kasashen Afrika sun daina sayen man su, na Dangote suke saye

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, matatun man fetur na kasashen Turai sun fara kullewa saboda kafuwar matatar man Dangote da kuma yanda kasashen Afrika suka koma sayen man fetur a hannun matatar man ta Dangote maimakon sayowa a kasashen turai. Rahoton ya bayyana cewa a baya kamin zuwan matatar Dangote, matatun man kasashen Turai na samar da man fetur ganga miliyan 4.207 amma yanzu saboda zuwan matatar man fetur din Dangote, ganga Miliyan 4.104 suke fitarwa. Hakan ya farune sanadiyyar rufewar matatun man fetur irin su, Grangemouth refiner dake Scotland, da Prax’s da sauransu.

Ji abin mamaki ga rayuwar dan daba daya addabi Kaduna, Watau Habu dan Damusa da aka kashe

Duk Labarai
Habu dan Damusa da ya rigamu gidan gaskiya ya gamu da ajalinsa ne a hannun jami'an tsaro kamar yanda rahotanni suka bayyana. Wasu sun rika murna da mutuwarsa inda wasu kuma suka rika jimami da nema masa rahama. Saidai sabon bayani da ya fito game dashi shine, ashe gadon daba yayi, mahaifinsa ma dan dabane, kuma shima an kasheshi ne ranar da aka haifi Habu Dan Damusa. Hakanan ga habu shima an kasheshi kwana daya bayan da aka haifa masa diyarsa. https://twitter.com/Sarki_sultan/status/1960989309206466569?t=cNfVTM0kI8AqjUnrJ_cgQg&s=19
Kalli Bidiyo: ‘Yan darika an kunyata, An yi rawar Maulidi, Maulidi bashi da tushe a addini>>Inji Sheikh Sani Yahya Jingir

Kalli Bidiyo: ‘Yan darika an kunyata, An yi rawar Maulidi, Maulidi bashi da tushe a addini>>Inji Sheikh Sani Yahya Jingir

Duk Labarai
Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana cewa, 'yan Darika sun ji kunya, Sun yi rawa a wajan Maulidi. Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da aka ganshi yana wa'azi. Malam ya nanata cewa, Maulidi bashi da Asali a addini. https://www.tiktok.com/@i_am_saeed01/video/7543574023129615622?_t=ZS-8zHMj7MJAuX&_r=1