Monday, May 11
Shadow

Duk Labarai

An kama Sanata Elisha Abbo saboda zargin Aikata Alfasha da wata me kananan shekaru

An kama Sanata Elisha Abbo saboda zargin Aikata Alfasha da wata me kananan shekaru

Duk Labarai
Hukumomin 'yansanda sun kama sanata Elisha Abbo Saboda zargin aikatawa wata yarinya Fyade. Rahoton yace Tsohon sanatan wanda ya wakilci Adamawa ta Arewa ya mika kansa wajan 'yansanda a Abuja bayan da aka zargeshi da yiwa yarinya me shekaru 13 fyade. Iyayen yarinyar sun yi zargin cewa, sanata Senator Aishatu Dahiru Ahmed (Binani) ta je har gidansu inda ta rokesu da kada su fitar da maganar. Hakanan shima sanata Elisha Abbo ya rika aikawamahaifin yarinyar kudade da shirin kulle musu baki. Dan Rajin kare hakkin bil'adama kuma Lauya, Deji Adesogan ne ya bayyana hakan sannan yace har yanzu sanata Elisha Abbo na daure a hannun 'yansanda. Wannan dai ba shine karin farko da Sanata Elisha Abbo ya shiga karma-karma ba, a baya ya taba cin zarafin wata mata a ofishin sayar da kayan biya...
Bansan wace irin harka ‘yan Matan Fim din Hausa suke suna samun kudaden sayen mota da gidaje ba amma maganar gaskiya kudin Fim basa sayen irin wannan abubuwa>>Inji Isa Bello Jan

Bansan wace irin harka ‘yan Matan Fim din Hausa suke suna samun kudaden sayen mota da gidaje ba amma maganar gaskiya kudin Fim basa sayen irin wannan abubuwa>>Inji Isa Bello Jan

Duk Labarai
Dajjito a masana'antar fina-finan Hausa, Isa Bello jaa ya bayyana cewa, kudin aikin fim basu kai suka kawo ba a yanda za'a ce mutum har zai iya mallakar wata kadara dasu ba. An tambayeshi ne game da wanda ke sayen gidaje da motoci musamman 'yan mata. Malam Isa yace bai san wace harka suke yi suna samun wadannan kudade ba. Yace amma su masu shirya fim din sukan samu Miliyoyin kudade a matsayin riba saboda kudi suka zuba suka shirya fim din. Kalli Hirar da aka yi dashi a kasa: https://www.tiktok.com/@juicylifestyle7/video/7553410801923558674?_t=ZS-90Dhl1DXO7N&_r=1
Ba gaskiya bane, Ban ce zan janye wa kowa daga takarar shugaban kasa ba>>Atiku Abubakar

Ba gaskiya bane, Ban ce zan janye wa kowa daga takarar shugaban kasa ba>>Atiku Abubakar

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya musanta rahotanni dake yawo cewa wai yace zai janye wa matashi yayi takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC. Atiku ta bakin me magana da yawunsa, Paul Ibe yace wannan magana ba gaskiya bace. Yace a hirar da yayi da BBC babu inda yace zai janyewa wani dan takara, yace abinda ya fada shine idan aka yi zaben fidda gwani kuma matashi yayi nasara a zaben zai goya masa baya. Atiku yayi kira ga 'yan Jarida su daina fassara labari ba yanda ya kamata ba.
Ku hadani da Yahya Haifan, Naji yana cika bakin a cikin mintuna 5 zai iya kare Malam Lawal Triumph>>Inji Malama Jamila Abubakar

Ku hadani da Yahya Haifan, Naji yana cika bakin a cikin mintuna 5 zai iya kare Malam Lawal Triumph>>Inji Malama Jamila Abubakar

Duk Labarai
Malama Jamila Abubakar ta nemi a hadata da Malam Yahya Haifan su yi maqabala. Malama ta bayyana hakane inda take tuhumar Haifan kan cewa a cikin mintuna 5 zai warware zargin da akewa Malam Lawal Triumph. Malama Jamila ta zargi 'yan Izala da Ta'addanci. Kalli Bidiyon jawabinta anan https://vt.tiktok.com/ZSDK5XaTt
Soke Faretin Sojoji na ranar ‘yanci ya bani damar yin bacci da cin abincin safe da kyau>>Inji Shugaba Tinubu

Soke Faretin Sojoji na ranar ‘yanci ya bani damar yin bacci da cin abincin safe da kyau>>Inji Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, soke faretin sojoji na ranar 'yanci ya bashi damar yin bacci da kyau da kuma in abincin safe da kyau. Shugaban ya bayyana hakane yayin bude wani dakin kimiyyar zane-zane da aka sakawa sunan Wole Soyinka. Fadar Shugaban kasa tun kamin ranar 'yanci ta sanar da cewa, babu faretin sojoji da aka saba yi.