Friday, December 19
Shadow

Duk Labarai

Bidiyo: Ku kwantar da hankalinku Amare kuma zan muku wakar da zata share muku hawaye>>Ali Jita

Bidiyo: Ku kwantar da hankalinku Amare kuma zan muku wakar da zata share muku hawaye>>Ali Jita

Duk Labarai
Tauraron mawakin Hausa, Ali Jita ya bayyana cewa ya samu sakonni bayan fitar da wakarsa ta yabon Uwar gida. Saidai yace an nemi ya yiwa Amarya itama waka. Yace wakar dan nishadi ne yayi ta kuma yana neman a zauna lafiya a gidaje. https://www.tiktok.com/@realalijita/video/7520613137016540421?_t=ZM-8xZ66BriPJg&_r=1 Yace nan gaba kadan Amare su saurareshi zai musu wakarsu suma.
Bani da lafiya a taimaka a barni in je neman magani kasar waje>>Yahya Bello ya roki kotu a yayin da ake shari’a kan zargin satar Naira Biliyan 80.2 da ake masa

Bani da lafiya a taimaka a barni in je neman magani kasar waje>>Yahya Bello ya roki kotu a yayin da ake shari’a kan zargin satar Naira Biliyan 80.2 da ake masa

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello ya roki babbar kotun dake da zama a Abuja data taimaka ta barshi ya je kasar waje neman magani. Yahya Bello ya roki kotun data bashi fasfonsa wanda a baya ya bayar dan cika sharadin bayar da belinsa. Bello ya mika wannan korafinne ta hannun lauyansa, Joseph Daudu (SAN), Ana shari'a ne kan zargin da akewa Tsohon gwamnan na satar Naira Biliyan 80.2 wanda hukumar EFCC ta shigar da kararsa.
Tinubu zai je ziyara yankin Karebiyan da taron BRICS a Brazil

Tinubu zai je ziyara yankin Karebiyan da taron BRICS a Brazil

Duk Labarai
Shugaba Bola Tinubu zai bar Abuja a gobe Asabar domin ziyarar ƙasashe biyu Saint Lucia da Brazil, kamar yadda wata sanarwa da kakakinsa, Bayo Onanuga ta bayyana. Sanarwar ta ce da farko shugaban zai yada zango a Saint Lucia a ziyarar da zai yi domin kyautata dangantaka tsakanin Najeriya da ƙasashen yankin Karebiya. Daga nan kuma shugaban zai tashi ya nufi Brazil domin halartar taron ƙoli na 17 na ƙungiyar ƙasashe masu haɓakar tattalin arziƙi ta BRICS a birnin Rio de Janeiro, daga ranar 6 – 7, ga watan Yuli mai kamawa, 2025. Zai halarci taron ne a matsayin Najeriya na abokiyar tafiyar ƙungiyar. Afirka ta Kudu da Masar da Habasha su ne ƙasashen Afirka da ke zaman mambobin ƙungiyar a Afirka.
Yanzu-Yanzu: Ganduje ya bayyana ainahin dalilin da yasa ya sauka daga shugaban APC

Yanzu-Yanzu: Ganduje ya bayyana ainahin dalilin da yasa ya sauka daga shugaban APC

Duk Labarai
Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga shugabancin jam'iyyar APC a yau, Juma'a. Ya bayyana hakane a wata wasika da ya aikewa jam'iyyar. A cikin wasikar, Ganduje ya bayyana dalilin rashin lafiya a matsayin abinda yasa ya sauka daga mukamin nasa. Tsohon Gwamnan jihar Kanon ya sha suka daga mutanen yankin Arewa maso gabas saboda zargin rashin goyon bayan Kashim Shettima a matsayin abokin takarar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027 me zuwa. An bayyana cewa wani daga cikin mataimakan Gandujenne zai zama shugaban riko na jam'iyyar kamin babban zabenta a watan Disamba me zuwa.
Da Duminsa: Tinubu na son ya dauki Kwankwaso a matsayin mataimaki a 2027 shiyasa ya ya sauke Ganduje daga shugaban APC, ji bayani dalla-dalla

Da Duminsa: Tinubu na son ya dauki Kwankwaso a matsayin mataimaki a 2027 shiyasa ya ya sauke Ganduje daga shugaban APC, ji bayani dalla-dalla

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na shiri daukar Dr. Rabiu Musa Kwankwa a matsayin mataimakinsa. rahoton yace shiyasa ma Shugaban ya matsayawa Ganduje ya sauka daga shugabancin jam'iyyar APC. A yaune dai aka samu rahotannin dake cewa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga mukamin shugaban jam'iyyar APC bayan da fadar shugaban kasa ta nemi yayi hakan. Idan hakan ta tabbata, rade-radin da ake yadawa cewa shugaba Tinubu ba zai tafi da Kashim Shettima ba a zaben shekarar 2027 ta tabbata kenan.
Ji irin Wulakancin da Akawa Ganduje kamin ya sauka daga shugaban APC

Ji irin Wulakancin da Akawa Ganduje kamin ya sauka daga shugaban APC

Duk Labarai
Rahotanni sun tabbata cewa Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga shugaban APC. Wasu bayanai sun ce kamin saukarsa Ganduje, an cire duk wasu kayan aikinsa daga ofishinsa dake hedikwatar jam'iyyar APC dake Abuja. Rahoton yace kuma daga fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu aka umarci Ganduje ya sauka daga mukamin nasa. Wane ne Abdullahi Ganduje? An haifi Abdullahi Umar a ƙauyen Ganduje da ke cikin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano a 1949. Ya fara karatun Ƙur'ani da Islamiyya a ƙauyensu, inda ya samu ilimin addini. Ya shiga firamare ta Dawakin Tofa daga 1956 zuwa 1963. Ganduje ya fara makarantar sakandiren Birnin Kudu a 1964 inda ya kammala a 1968. Ya shiga makarantar horar da malamai da ke Kano tsakanin 1969 zuwa 1972. Tsohon gwamnan jihar Kanon ya samu d...
Ji bayani dalla-dalla: Shugaba Tinubu ne yacewa Ganduje ya sauka daga shugabancin APC

Ji bayani dalla-dalla: Shugaba Tinubu ne yacewa Ganduje ya sauka daga shugabancin APC

Duk Labarai
Shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga muƙaminsa bayan kwashe ƙasa da shekara biyu yana jagorancin jam'iyyar. Wasu majiyoyi daga fadar shugaban Najeriya sun tabbatar wa BBC cewa Ganduje ya ajiye muƙamin ne bayan da fadar shugaban ƙasa ta umarce shi da yin hakan. "Da gaske ne Ganduje ya sauka tun jiya (Alhamis) aka ba shi umarnin ya rubuta takardar murabus, a yau da safe (juma'a) ya miƙa takardar," in ji majiyar. Hakan na zuwa ne bayan wani rudani da aka samu kimanin mako ɗaya da ya gabata a lokacin taron jam'iyyar ta APC na arewa maso gabashin ƙasar. A lokacin taron, wasu daga cikin ƴan jam'iyyar sun nuna fushi kan rashin bayyana sunan mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shettima a matsayin wanda zai mara wa Tinubu baya takarar shugab...
Da Duminsa: A karshe dai Shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga mukaminsa

Da Duminsa: A karshe dai Shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga mukaminsa

Duk Labarai
Rahotanni sun tabbata cewa, shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga mukaminsa. Jaridar Vanguard ta bayyana cewa ta samu tabbacin saukar Ganduje daga mukaminsa. Babu tabbacin dalilin da yasa Ganduje ya sauka daga mukaminsa amma wata majiya daga jam'iyyar ta tabbatar da saukar Ganduje. Rahotanni sun ce kamin saukarsa daga mukamin, an dauke duka wasu abubuwan sa daga ofishin shugaban jam'iyyar dake Abuja.