Friday, December 19
Shadow

Duk Labarai

Wallahi Ban taba sanin namiji ba, kuma za’a iya gwadawa a gani, mijin aure nake nema>>Budurwa ‘yar shekaru 46 da bata taba aure ba ta koka

Wallahi Ban taba sanin namiji ba, kuma za’a iya gwadawa a gani, mijin aure nake nema>>Budurwa ‘yar shekaru 46 da bata taba aure ba ta koka

Duk Labarai
Wata mata me shekaru 46 da bata taba aure ba ta koka da cewa maza na gudunta suna cewa ta tsufa. Tace yawanci mazan dake zuwa wajanta mazan aurene kuma ba aure ke kaisu wajanta ba, suna nemanta da lalata ne. Tace da yawa idan suka ganta sai su ce ta tsufa. Ta koka da cewa ba ita kadai bace a wajan mahaifiyarta ba amma ita kadai ce bata yi aure ba. Matar tace wallahi bata taba sanin Namiji ba, kuma idan mutum na da yanda zai gwada, yana iya gwadawa ya gani. Ta bayyana hakane a wata hira da aka yi da ita a wani gidan rediyo me suna Agidigbo FM inda tace tana neman taimakon a samo mata mijin aure.
A karshe dai shugaba Tinubu ya sakawa sabbin dokokin Haraji hannu, Ji Bayani dalla-dalla abinda suka kunsa

A karshe dai shugaba Tinubu ya sakawa sabbin dokokin Haraji hannu, Ji Bayani dalla-dalla abinda suka kunsa

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan sababbin dokokin haraji huɗu a wani mataki na sauya fasalin tsarin karɓa da tattara haraji na ƙasar. Gwamnatin ta ce sabbin dokokin za su sauƙaƙa tsarin, da rage wahalhalun haraji kan ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni, da kuma taimakawa wajen inganta karɓar haraji. "Sauye-sauyen za su taimaki masu ƙaramin ƙarfi tare da tallafa wa ma'aikata ta hanyar ƙara yawan abin da suke samu,'' kamar yadda Shugaba Tinubu ya bayyana a watan da ya gabata lokacin bikin cika shekara biyu a kan mulki. Ya ƙara da cewa: "Sauye-sauyen sun cire muhimmman abubuwa kamar abinci da ilimi da kula da lafiya daga tsarin biyan harajin VAT. Haka nan, sabon tsarin ya keɓe karɓar rance da sufuri da makamashin da ba ya gurɓata muhalli, duka wadannan ba za su biya harajin...
Mummunan rikici ya barke a jam’iyyar PDP

Mummunan rikici ya barke a jam’iyyar PDP

Duk Labarai
Kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP (BoT) ta yi watsi da matakin da shugaban jam’iyyar Iliya Damagum, ya dauka na soke taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) karo na 100 da aka shirya gudanarwa a ranar Litinin, 30 ga Yuni, 2025. Haka nan kwamitin ya ce matakin da Damagum ya ɗauka na mayar da Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar ba shi da tushe a kundin tsarin mulki na PDP. A wata sanarwa da shugaban kwamitin amintattun, Sanata Adolphus Wabara ya fitar, ya bayyana cewa "kundin tsarin mulkin PDP na shekarar 2017 ya bayyana ƙarara cewa babu wani mutum ko ɓangare da ke da ikon soke ko ɗage taron shugabannin jam'iyya da aka yanke shawarar gudanarwa a taro na 99 da aka yi a ranar 27 ga Mayu, 2025". Saboda haka, matakin soke taron da Damagum ya ɗauka ya saɓa wa kundin tsarin jam’...
Ya kamata ku fahimci cewa, babu dan siyasar da ‘yan Adawa zasu hada kai su taso suna son kayar dashi mulki irin yanda ake min kuma yayi shiru yaki magana>>Shugaba Tinubu

Ya kamata ku fahimci cewa, babu dan siyasar da ‘yan Adawa zasu hada kai su taso suna son kayar dashi mulki irin yanda ake min kuma yayi shiru yaki magana>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, babu dan siyasar da 'yan Adawa zasu hada kai su taso suna son kayar dashi mulki kamar yanda ake masa, amma yayi shiru yaki yin magana. Shugaban ya jawo hankalin 'yan Najeriya da cewa su daina baiwa 'yan siyasar dake son kayar dashi zabe a 2027 muhimmanci. Ya bayyana hakane a yayin ziyarar da ya kai jihar Nasarawa inda ya kaddamar da wasu ayyukan raya kasa da gwamnatin jihar ta gudanar.
Ji bayani dalla-dalla yanda Ministan Abuja Nyesom Wike ya baiwa dansa filiye dubu arba’in a Abuja wanda kudinsau sun kai dala Biliyan $3.6, yace so yake ‘ya’yansa su zamana sun fi kowa yawan filaye a Abuja

Ji bayani dalla-dalla yanda Ministan Abuja Nyesom Wike ya baiwa dansa filiye dubu arba’in a Abuja wanda kudinsau sun kai dala Biliyan $3.6, yace so yake ‘ya’yansa su zamana sun fi kowa yawan filaye a Abuja

Duk Labarai
Ana zargin ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike da baiwa dansa wani babban fili a Abujan wanda darajarsa ta kai Dala Biliyan $3.6. Kafar Peoplesgazette ce ta ruwaito labarin inda ta bayyana wasu kafofin da suka tabbatar mata da faruwar hakan wanda aka ce sabawa dokane. Wike wanda tun watan Augusta na shekarar 2023 yake akan mukamin Ministan Abuja, ya baiwa dan nasa me suna Joaquin Wike filin da ya kai girman Hecta 2000, kamar yanda rahoton ya bayyanar. Rahoton yace Wike bai bi doka ba wajan baiwa dan nasa wannan makeken fili ba sannan kuma bai ma biya kudaden da ya kamata a biya ba. Sannan ya baiwa dan nasa Filayen ne a manyan unguwannin Abuja da suka hada da Maitama, Asokoro, Guzape, Bwari, da Gaduwa. Yawan filayen sun kai Dubu 40. Wani Hadimin Wiken yace s...
Yanzu na kammala canja komai a jikina na zama cikakkiyar mace>>Inji Dan Daudu, Idris Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky

Yanzu na kammala canja komai a jikina na zama cikakkiyar mace>>Inji Dan Daudu, Idris Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky

Duk Labarai
Shahararren dan Daudu, Idris Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky ya bayyana cewa, a yanzu ya kammala canja komai na jikinsa inda ya zama cikakkiyar mace. Bobrisky ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na sada zumunta. Yace yana son a yanzu a rika kiransa da sunan Afolashade Amope. Yace shima yanzu za'a iya yin jima'i dashi kamar yanda ake yi da kowace mace. Ya lokaci yayi da mutane zasu amince da hakan inda ya taya kansa murna. Kuma yacw yana Alfahari da kansa.
Cristiano Ronaldo ya sabunta Kwantirakinsa da Kungiyar Al Nasr, Ji damar da suka bashi ta ban mamaki

Cristiano Ronaldo ya sabunta Kwantirakinsa da Kungiyar Al Nasr, Ji damar da suka bashi ta ban mamaki

Duk Labarai
Tauraron dan kwallon Portugal, Cristiano Ronaldo ya sabunta kwantirakinsa da kungiyar Al Nasr ta kasar Saudiyya. Daga cikin damarmakin da aka bashi shine yana da bakin magana akan duk dan wasan da kungiyar zata siya. Ronaldo dan shekaru 40 ya amince da ci gaba da zama a kungiyar ta Al Nasr har zuwa shekarar 2027. Tun a shekarar 2023 ne dai Ronaldo ya je kungiyar ta Al Nasr.
‘Yan Kwaya sun karu a Najeriya>>Gwamnatin Tinubu ta koka

‘Yan Kwaya sun karu a Najeriya>>Gwamnatin Tinubu ta koka

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Gwamnatin tarayya ta koka da cewa, 'Yan kwaya sun karu a Najeriya. Hakan na zuwane yayin da ake tunawa da zagayowar ranar yaki da shan kwaya da safararta a Duniya. Gwamnatin ta yi kiran hada kai dan yakar wannan matsala. Babbar sakatariya a ma'aikatar lafiya ta tarayya, Daju Kachollom, cee ta bayyana hakan a ganawa da manema labarai. Tace matsalar ta'ammuli da miyagun kwayoyi ba matsalar mutum daya bace ko kuma masu sha kawai, matsala ce ta kowa da kowa dan haka hadin kai...