Sunday, December 14
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyon yanda aka rika jifar Sarki Sanusi Lokacin hawan Fanisau

Kalli Bidiyon yanda aka rika jifar Sarki Sanusi Lokacin hawan Fanisau

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Kano na cewa, an jefi sarki Muhammad Sanusi II a yayin hawan fanisau. Bidiyo ya karade kafafen sada zumunta inda aka ji wasu na fadar cewa an jefi sarkin. https://twitter.com/2027Apc/status/1932738745603928134?t=pHqm2Y0iKqvZSg4Ie3dEMA&s=19 Dubban masoya ne dai suka raka Sarki Sanusi Hawan Fanisau inda a wata majiyar ake cewa sun kai mutane Miliyan 5.
Ji yanda Kwaila ta gayawa Saurayinta Sojan Ruwa cewa Allah ya jefashi ruwa ‘yan ruwa su cinyeshi saboda ta tambayeshi dubu 1 be bata ba

Ji yanda Kwaila ta gayawa Saurayinta Sojan Ruwa cewa Allah ya jefashi ruwa ‘yan ruwa su cinyeshi saboda ta tambayeshi dubu 1 be bata ba

Duk Labarai
Wata kwaila ta dauki hankula a kafafen sada zumunta bayan da muryarta ta bayyana tana yiwa saurayinta wanda sojan ruwane rashin kunya. Kwailar dai ta nemi da ya bata dubu dayane bai bata ba inda tace masa Allah ya jefashi ruwa 'yan ruwa su cinyeshi. https://twitter.com/Ormarfaruq/status/1932346387225543142?t=wB4ld55-XMY7WDBPV4R0_w&s=19 Abin dai ya nishadantar.
Ka Yi Watsi Da Masu Suka, Ka Cigaba Da Ayyukan Cigaban Da Kake Yi, Sakon Tinubu Ga Wike

Ka Yi Watsi Da Masu Suka, Ka Cigaba Da Ayyukan Cigaban Da Kake Yi, Sakon Tinubu Ga Wike

Duk Labarai
Ka Yi Watsi Da Masu Suka, Ka Cigaba Da Ayyukan Cigaban Da Kake Yi, Sakon Tinubu Ga Wike. Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Ministan Abuja, Nyesom Wike, da ya ci gaba da aikinsa na alheri ba tare da sauraron masu suka ba. Tinubu ya bayyana hakan ne yau yayin kaddamar da sabun Dakin Taro na Ƙasa da Kasa da aka gyara kuma aka sake sanya mata suna Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre a Abuja.
A karin farko: Kasashen Canada,UK, Australia da New Zealand zasu kakabawa kasar Israyla takunkumi saboda kìsàn Kiyashin da sukewa Falasdiynawa

A karin farko: Kasashen Canada,UK, Australia da New Zealand zasu kakabawa kasar Israyla takunkumi saboda kìsàn Kiyashin da sukewa Falasdiynawa

Duk Labarai
Kasashen Canada,UK, Australia da New Zealand zasu kakabawa wasu jami'an Gwamnatin kasar Israela 2 takunkumi. Wadanda za'a kakabawa wannan takunkumi sune Itamar Ben Gvir da Betzalel Smotrich wanda 'yan siyasa ne masu rura wutar ci gaba da kisan Falasdiynawa. Rahotanni a baya sun ce duka kasashe masu fada a ji na Duniya sun amince a dakatar da yakin Gaza in banda kasar Amurka. Dubban mutane ciki hadda mata da kananan yara ne aka kashe a Gàzà wanda kasashen Duniya ke cewa an aikata laifukan yaki.
Karka Saurari masu zaginka, Ana samun canji na Alheri sosai a kasarnan>>Sanata Godswill Akpabio ya gayawa shugaba Tinubu

Karka Saurari masu zaginka, Ana samun canji na Alheri sosai a kasarnan>>Sanata Godswill Akpabio ya gayawa shugaba Tinubu

Duk Labarai
Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya bayyanawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu cewa ya daina sauraren masu zaginsa. Yace ana samun canji sosai kuma na Alheri sanadiyyar salon mulkinsa. Ya bayyana hakane a jawabin da yayi a wajan taron kaddamar da gyaran da akawa babban dakin taro na Abuja. Akpabio yace ko da mutane naso ko basa so, majalisar tarayya tana Alfahari dashi.
Jihohin Taraba, Adamawa, Borno da Yobe sun fada duhu bayan da wutar Lantarkinsu ta lalace, ji ranar da za’a gyara

Jihohin Taraba, Adamawa, Borno da Yobe sun fada duhu bayan da wutar Lantarkinsu ta lalace, ji ranar da za’a gyara

Duk Labarai
Jihohi 4 daga cikin 6 na yankin Arewa maso gabas, watau jihohin Taraba, Adamawa, Borno da Yobe sun fada duhu bayan da wutar lantarkinsu ta lalace. Da misalin karfe 10:00 am na safiyar ranar Talata, 10 ga watan Yuni ne wutar ta samu matsala. Kuma ana tsammanin sai nan da Ranar Asabar, da misalin karfe 5:00 pm za'a gyara wutar. Lamarin ya taba harkokin kasuwanci a jihar inda dama saidai su koma amfani da janareta, ko Sola wanda kuma basu da wannan saidai su hakura. Kamfanin Yola Electricity Distribution Company, YEDC yace dauke wutar ya zama dole dan a inganta injinan ko yanayin samar da wutar. Kamfanin ya bayyana jin dadin hakurik mutane da hadin kan da suka bayar kan wannan aiki.
Shugaban karamar hukuma ya rasu makonni bayan hawansa kujerar mulki a Katsina

Shugaban karamar hukuma ya rasu makonni bayan hawansa kujerar mulki a Katsina

Duk Labarai
Sabon zababben shugaban karamar hukumar Bakori da ke jihar Katsina, Hon. Aminu Dan Hamidu, ya rasu kasa da wata biyu bayan karbar rantsuwar kama aiki. Hon. Hamidu, wanda ya hau kujerar shugabancin karamar hukumar a watan Afrilu 2025, ya rasu a ranar Litinin, 9 ga Yuni, 2025. Har yanzu ba a bayyana musabbabin mutuwarsa a hukumance ba. Sai dai rahotanni da ba a tabbatar da su ba na nuna cewa yana fama da rashin lafiya tun kafin rasuwarsa. Kaula Mohammed, sakataren yada labarai ga Gwamna Dikko Umaru Radda, ya tabbatar da wannan lamari a cikin wata sanarwa. A cikin sanarwar, Gwamna Radda ya bayyana alhini da jimamin da ya shiga sakamakon rasuwar Hon. Hamidu, yana bayyana mamacin a matsayin “dan jam’iyya na kwarai, tsohon ma’aikacin gwamnati mai kwarewa, kuma ɗan siyasa na ƙasa da ya s...
Bèllò Tùrjì ya ƙaƙaba harajin Naira Miliyan 50 kan manoma a Zamfara da Neja

Bèllò Tùrjì ya ƙaƙaba harajin Naira Miliyan 50 kan manoma a Zamfara da Neja

Duk Labarai
Bello Turji ya ƙaƙaba harajin Naira Miliyan 50 kan manoma a Zamfara da Neja {"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Mazauna wasu yankunan da dama a jihohin Zamfara da Neja sun sake shiga wani mawuyacin hali, bayan da sanannen jagoran ƴan bindiga, Bello Turji, ya bukaci a biya naira miliyan 50 kafin a basu damar fara aikin noma na bana. LEADERSHIP ta rawaito cewa wannan bukatar ta fito fili ne ta bakin wani mai nazarin tsaro mai suna Bakatsine, wanda ya wallafa bayani a shafinsa na X , inda ya bayyana cewa shugaban ƴan ...
Sanata Lado ya miƙa kyaututtukan gidaje ga waɗanda su ka yi na ɗaya da na biyu a musabaƙar Kur’ani a Kano

Sanata Lado ya miƙa kyaututtukan gidaje ga waɗanda su ka yi na ɗaya da na biyu a musabaƙar Kur’ani a Kano

Duk Labarai
Sanata Lado ya miƙa kyaututtukan gidaje ga waɗanda su ka yi na ɗaya da na biyu a musabaƙar Kur'ani a Kano Sanata Bashir Lado ya miƙa kyaututtukan gidaje ga waɗanda su ka yi na ɗaya da na biyu a musabaƙar Kur'ani da aka kammala kwanannan a jihar Kano. Kyaututtukan sun haɗa da gidaje biyu masu dakuna biyu da falo ga wadanda suka yi na biyu a gasar , da kuma gidaje masu dakuna uku ga wadanda suka yi na ɗaya a musabaƙar. Wadanda suka samu nasarar sun hada da:Maryam Abubakar Mu'az (wacce ta zo ta ɗaya a izifi 60 a mata, Ahmad Shu'aib (wanda ya yi ma daya a izifi 60 a maza), Zainab Hassan Shu'aib (ta biyu a izifi 60 a mata), da Ahmad Kabir Baturi (na biyu a izifi 60 a maza). Da ya ke jawabi jim kadan bayan mika mukullayen gidajen, Sen.Lado, wanda ya shirya gasar, ya ce an gudanar da ...