Zan iya yin mulki a karo na 3>>Donald Trump ya fada cikin Raha
Zababben shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa zai iya yin mulkin kasar a karo na 3.
Trump ya bayyana hakane yayin ganawa da 'yan majalisar Republican.
Inda yace ba zai iya sake tsayawa takara ba sai idan sune 'yan majalisar suka ga cewa yayi kokari suka bashi dama.
An fashe da dariya a yayin da yayi maganar.
Bayan zaman nasu, da aka tambayi 'yan majalisar sun ce maganar Trump yayi ta ne cikin raha.