Magoya bayan kungiyar Kwallon kafa ta Barcelona sun yi taro a Kano.
Wannan taro suna yinsa duk shekara dan nuna goyon baya ga kungiyar tasu.
Kalli Bidiyon anan:
https://www.youtube.com/watch?v=do414VtATCw?si=U2RjBKik3md9HBpU
'Yan majalisar Dattijai sun tafi hutun watanni biyu da suka saba yi duk shekara.
Sai nan da watan Satumba 23 sannan zasu dawo daga hutun.
Saidai kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa, sauran kwamitin majalisar zasu ci gaba da aiki a yayin da ake hutun.
https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1948374536266580176?t=DTCiNO-EVCw7S31bP4O4IA&s=19
Sabon shugaban jam'iyyar APC, Nentawe Yilwatda, ya ɗau alwashin ɗaukar matakai don ganin ya ƙara janyo gwamnonin babbar jam'iyyar adawa ta PDP zuwa cikin jam'iyyar mai mulki.
Yilwatda ya bayyana haka ne yayin tattaunawa a cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, jim kaɗan bayan zama shugaban APC.
Ya ce baya ga ƴan jam'iyyar PDP da zai janyo zuwa APC, har da wasu ƴaƴan jam'iyyun adawa.
"Abun da na fi mayar da hankali a yanzu shi ne ganin haɗin kan jam'iyyar mu," in ji shi - inda ya ce zai tabbatar da cewa jam'iyyar ta yaɗa manufofinta yadda ya kamata.
Sabon shugaban jam'iyyar ta APC ya ce duba da irin tarihi da yake da shi a fannoni daban-daban, yana da ƙwarewar da ta kamata wajen jagorantar jam'iyyar mai mulki.
A yau ne aka rantsar da sabon shugaban jam'iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda inda kuma tuni har ya shiga Ofis.
https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1948415556605898875?t=gw-pn-u4m5zu3TEXcKWSGw&s=19
Bayan da aka rantsar dashi an ga yanda magoya bayansa a Jos ke ta murna da shewar nasararsa.
Tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya caccaki gwamnatin Bola Ahmad Tinubu.
Kwankwaso yace Tinubu ya mayar da hankali wajan kai abubuwan ci gaba kudu yayi watsi da Arewa.
Kwankwaso ya bayyana bakane a yayin taron masu ruwa sa tsaki na jihar Kano inda ake tattauna batun gyaran kundin tsarin mulki.
Yace da ya je Abuja ta jirgi ya so ya dawo amma sai aka samu matsala ya dawo ta Mota, yace titin Abuja zuwa Kaduna bashi da kyau ko kadan
Kwankwaso yace amma Gwamnatin Tinubu na gina titi daga jihohin Yarbawa zuwa jihohin Inyamurai.
Yace basa sukar yiwa jama'a aiki a kowane sashe na Najeriya amma a mayar da hankali wajan yiwa wani bangare aiki yayin da aka yi watsi da wani bangare hakan bai kamata ba.
Malamin Addinin Islama da akewa lakabi da Albanin Gombe ya goyi bayan Sheikh Musa Asadussunnah kan ikirarin da yayi cewa ko da wanda aka zalinta bai yafe ba Allah na yafewa.
Sheikh Musa Asadussunnah ya bayyana cewa Allah na yafe hakki ko da me hakki bai yafe ba inda take magana akan masu cewa Basu yafewa Buhari ba.
Shima dai Albanin Gombe yace Annabi yace idan aka samu wanda basa shirka mutum 40 sukawa mutum Sallah, Allah yana yafewa matacce.
Kalli Bidiyon anan
https://www.tiktok.com/@janbiro_s4704ii/photo/7530456341895482680?_d=secCgYIASAHKAESPgo81wvmZLZhOW%2FalYNmSADG68FO1wPuQ%2BrxyO%2FgDW7AESJ1AhQBvOedrJgndnoxjTvEKhr7uopg8fsgo6X%2BGgA%3D&_r=1&_svg=1&aweme_type=150&checksum=200f6657f05b5a8e62a0977611db0df16620ec45b9becff5a913e6329659b214&link_reflow_popup...
Rahotanni daga Jos babban birnin jihar Flato na bayyana cewa, an barke da murna bayan da aka tabbatar da Professor Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam'iyyar APC.
A yau ne dai aka bayyana Professor Nentawe Yilwatda a matsayin shugaban APC wanda ya maye gurbin Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1948410580412330452?t=I4o5VkpTFz11AhTXPakAmg&s=19
https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1948408360300163227?t=xnbcHp8N-7vTnVDC_j7UKw&s=19
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya baiwa gwamnonin Najeriya umarnin su yiwa talakawa yayyafin Alheri saboda a cewarsa ana ta korafi.
Shugaban kasar ya bayyana cewa shine ke jagorantar kawo Chanji a Najeriya sannan kuma zasu ci gaba da yiwa 'yan Najeriya aiki tukuru.
https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1948399213571612900?t=VBsNxPK2FkRkrD-zPNnggA&s=19
https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1948382291501158620?t=JPwMiXjVE8kYlCeL9TdQVg&s=19
Jam’iyyar APC ta naɗa Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa, bayan taron da aka gudanar a Abuja tare da shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin jam’iyyar.
Yilwatda, wanda ya fito daga jihar Filato, ya maye gurbin Dr. Abdullahi Umar Ganduje wanda ya yi murabus a watan Yuni 2025 saboda dalilan lafiya. Kafin naɗinsa, Yilwatda na rike da mukamin Ministan Jin ƙai da Rage Talauci a gwamnatin Tinubu.
Farfesa Nentawe ya kasance ɗan takarar gwamna a jihar Filato a zaɓen 2023 karkashin APC. Hakanan, ya taba zama kwamishinan zaɓe na hukumar INEC daga 2017 zuwa 2021, inda ya jagoranci harkokin zaɓe a jihohi da dama.
Naɗin nasa ya zo ne da nufin ƙarfafa haɗin kai da dai...