Gwamnonin Jihohin Arewa maso yamma sun bayar da hutun gobe Talata, 15 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu dan jimamin Buhari
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false}
Ƙungiyar gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana kaɗuwarsu kan rasuwar tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari wanda ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin shekarar 2025 a birnin Landan.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, wanda shugabanta, Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda ya fitar, ya ce Buhari tamkar uba yake a gare su.
"Muna miƙa ta'aziyarmu ga Shugaban Najeriya Bola Tinubu da iyalai da ƴanuwa da mutanen jihar Katsina da ma ƴan Najeriya baki ɗaya ...







