Thursday, December 18
Shadow

Duk Labarai

Za mu ƙwato duka dazukan Najeriya daga hannun ɓata-gari -Tinubu

Za mu ƙwato duka dazukan Najeriya daga hannun ɓata-gari -Tinubu

Duk Labarai
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin ƙwato duka wurare da dazukan ƙasar da ƴanbindiga ke ɓuya, ta hanyar girke sabbin dabaru na zamani domin yaƙi da ta'addaci da ƴan fashin daji. Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga jagororin jihar Katsina a lokacin liyafar cin abincin dare da aka shirya masa a gidan gwamnatin jihar ranar Juma'a. ''Dangane da matsalar tsaro, matsala ce da ta addabi ƙasarmu', kuma na yi magana da sojoji, na tabbatar musu cewa za mu yi duk mai yiwuwa don kawo ƙarshen matsalar ƴanbindiga'', in Tinubu. "Za mu samar da kayan aiki na zamani domin ƙwace duka dazukan ƙasarmu daga hannun miyagu, matsalar tsaro ta shafi duka Najeriya ne ba wani yanki ba, kuma mun sani cewa indai muna so ƙasarmu ta ci gaba to dole mu kawa...
Saudiyya: Matan wani dattijo mai shekaru 70 sun samar masa mata mai ƙarancin shekaru ya aura

Saudiyya: Matan wani dattijo mai shekaru 70 sun samar masa mata mai ƙarancin shekaru ya aura

Duk Labarai
Wani dattijo mai shekaru 70 a duniya, Awad Al-Thouaib, wanda ke da mata biyu, ya samu shawarar su da ya karo aure. Al-Thouaib, dan garin Taif a kasar Saudiyya, ya karade kafafen watsa labarai bayan da ya sanar da cewa matan nasa sun bashi shawarar ya auri mata ta uku, har ma su ka ce ya nemi zuƙeƙiyar yarinya mai karancin shekaru ya aura. A cewar sa, matan nasa sun mishi alkawarin biya masana kuɗin da zai dauki amaryar ta sa su je hutun angwanci a duk inda ya ke so. Ya ce su ma matan nasa biyun sun fara tsufa, shi ne su ka bashi shawarar da ya nemo yarinya sabon jini yadda za ta tallafawa rayuwar sa. Shafin Lifeinsaudia.com ya ruwaito cewa tuni matan biyu sun yi shirin biki na mijin nasu da duk wacce ya ga ta yi masa a matsayin mata ta uku.
TIRƘASHI: Añ bankado Natasha na wasa da hankalin jama’a ne kawai game da zargin Akpabio?

TIRƘASHI: Añ bankado Natasha na wasa da hankalin jama’a ne kawai game da zargin Akpabio?

Duk Labarai
TIRƘASHI: Añ bankado Natasha na wasa da hankalin jama'a ne kawai game da zargin Akpabio? Daga Ibrahim Jamiu Adamu, Abuja Da so samu ne ba zan ce uffan game da abin da ke faruwa tsakanin Sanatar da aka tura ta wakilci al’ummar Kogi ta tsakiya Natasha da Shugaban majalisar Sanata Godswill Akpabio ba. Amma bayan dogon nazari sai na gane cewa tabbas wannan turka-turka ta jefa al’ummar da suka tura wannan baiwar Allah ta wakilce su tauye musu hakki. Ga mai bibiyar lamuran da ke faruwa ya san yadda aka kawo inda muke a wanan batu na zarge-zargen Natasha. A waje na ina ganin ƙarara tana nuna ba ta san darajar abin da aka damƙa mata ba. Mu fara da yadda ta watsar da haƙƙin wakilcin da miliyoyin mutane suka damka mata, kowa ya ga yadda take ta kalaman ɓatanci don neman tausayar al’u...
Yunwa da Talauci ne ke jawo matsalar tsaro a Najeriya>>Shugaba Tinubu

Yunwa da Talauci ne ke jawo matsalar tsaro a Najeriya>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaba kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Yunwa da talauci na kan gaba cikin jerin abubuwan dake jawo Talauci a Najeriya. Shugaban ya bayyana hakanne a wajan kaddamar da wasu ayyukan da Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya gudanar a yayin ziyarar kwaki biyu da ya je. Shugaba Tinubu ya jawo hankalin Gwamna Radda dama sauran Gwamnoni da su mayar da hankali wajan gudanar da ayyukansu ba tare da la'akari da masu kushe ba. Yace idan suka yi aiki me kyau shine jama'a zasu gani su yaba.
Shugaba Tinubu ya bar Katsina bayan ziyarar Kwanaki biyu

Shugaba Tinubu ya bar Katsina bayan ziyarar Kwanaki biyu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bar Katsina bayan kammala ziyarar kwanki biyu da ya je jihar. D misalin karfe 3 na yammacin ranar Asabar ne jirgin shugaban kasar ya bar filin jirgin sama na Umar Musa 'Yaradua dake jihar. Shugaba Tinubu a yayjn ziyararsa a jihar Katsina ya ziyarci sojoji inda ya karfafa musu gwiwa sannan ya kaddamar da wasu ayyuka biyu na titi da wata cibiyar ayyukan noma da gwamnatin jihar ta gina. A yau Asabar kuma shugaba Tinubu ya halarci daurin auren diyar gwamnan jihar Dikko Radda kamin barin Katsina.
‘Yan Bìndìgà sun kai hari wani sansanin sojojin Najeriya dake jihar Zàmfara inda suka kori sojojin suka konashi, sojojin sun koka da rashin makamai

‘Yan Bìndìgà sun kai hari wani sansanin sojojin Najeriya dake jihar Zàmfara inda suka kori sojojin suka konashi, sojojin sun koka da rashin makamai

Duk Labarai
Rahoto daga jihar Zamfara na cewa, 'yan Bindiga sun kai wani mummunan hari akan wani sansanin sojojin Najeriya dake Jangebe inda suka koneshi. Sun kai harinne da misalin karfe 3 na daren ranar Asabar. A garin Jangebe ne dai 'yan Bindigar suka taba sace 'yan mata daliban makaranta dake da shekaru tsakanin 10 zuwa 17 a ranar 26 ga watan Fabrairu na shekarar 2021. Harin ya farune a makarantar kwana ta mata me suna Government Girls Science Secondary School. Majiyar tace sojojin basu da kayan aiki kuma ta kara da cewa soja daya ya jikkata kuma an garzaya dashi Asibiti.
‘Yan Bindiga sun kàshè shahararren malamin Addinin Islama a jihar Katsina bayan sun yi garkuwa dashi

‘Yan Bindiga sun kàshè shahararren malamin Addinin Islama a jihar Katsina bayan sun yi garkuwa dashi

Duk Labarai
'Yan Bìndìgà a jihar Katsina sun kashe wani babban malamin Addinin Islama me suna Sheikh Mustapha Aliyu Unguwar Mai Kawo. 'Yan Bindigar dai sun yi garkuwa dashi inda suka ajiyeshi a wajensu na tsawon sati 3. Malamin shine shugaban kungiyar Munazzamatul Fityanul Islam ta karamar hukumar Kankara. Kuma an yi garkuwa dashi ne a garinsu na Unguwar Mai Kawo wanda hakan ke kara bayyana matsalar tsaron da ake fama da ita. Bakatsinene ya bayyana rasuwar tasa da yammacin Ranar Juma'a.