Monday, December 15
Shadow

Duk Labarai

Shugaba Tinubu Bai Sauke Ministocin Tsaron Nijeriya Ba – In ji Fadar Shugaban Ƙasa

Shugaba Tinubu Bai Sauke Ministocin Tsaron Nijeriya Ba – In ji Fadar Shugaban Ƙasa

Duk Labarai
Shugaba Tinubu Bai Sauke Ministocin Tsaron Nijeriya Ba - In ji Fadar Shugaban Ƙasa Mai magana da yawun shugaban kasar Bayo Onanuga ya ce masu yada irin wannan labarin na bogi, masu laifi ne da ya kamata a hukunta su ba tare da bata lokaci ba Wata kafar yada labarai ta zamani Phoenix browser ce dai ta fitar da labarin inda ta ce Shugaba Tinubu ya sallami minsitocin tsaro da kuma ministan lantarki
Sanata Natasha Akpoti ta kasa kawo hujjar cewa na nemeta da lalata shiyasa ta fara bani Hakuri, kumama inda zaku san sharri ne irin nasu na mata ta kulla min, bayan tace ne nemeta da lalata ta bini min je taruka da yawa har kasashen waje kuma har hotunan Selfie ta rika dauka dani>>Sanata Godswill Akpabio

Sanata Natasha Akpoti ta kasa kawo hujjar cewa na nemeta da lalata shiyasa ta fara bani Hakuri, kumama inda zaku san sharri ne irin nasu na mata ta kulla min, bayan tace ne nemeta da lalata ta bini min je taruka da yawa har kasashen waje kuma har hotunan Selfie ta rika dauka dani>>Sanata Godswill Akpabio

Duk Labarai
Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa Sanata Natasha Akpoti ta kasa kawo hujjojin kan zargin da take masa na cewa, ya nemeta da lalata. Ya bayyana hakane ta bakin lauyansa, Dr Olisa Agbakoba (SAN) yace dalili ma kenan na yin magamganin da ta yi kwanannan. Yace wani karin abin mamaki shine, Sanata Natasha Akpoti ta goge rubutun da ta yi na zargin da take masa a shafinta na sada zumunta. Yace wani karin abin dubawa shine Sanata Natasha Akpoti tace a shekarar 2023 ne Ya nemeta da lalata, amma bayan nan, ta bishi sun je taruka da yawa a ciki da wajen Najeriya a shekarar 2024. Yace a wajan wasu tarukan ma har hotunan Selfie take daukarsu tare kuma ta dora a kafafen sadarwa. Dan haka ya nemi Sanata Natasha Akpoti ta janye zargin da take masa.
Kalli Bidiyo: An zargi Gwamnati da hannu a tashin Gobarar kasuwar Taminus ta garin Jos

Kalli Bidiyo: An zargi Gwamnati da hannu a tashin Gobarar kasuwar Taminus ta garin Jos

Duk Labarai
A daren da ya gabata ne dai aka samu tashin Gobara a kasuwar Taminus ta garin Jos na jihar Filato. Daya daga cikin abinda mutane da yawa ke kokawa akai shine yanda jami'an kashe Gobara basu kai musu dauki da wuri ba. https://www.tiktok.com/@abasjos/video/7498904556814798085?_t=ZM-8vxlxzbBlSR&_r=1 Hakanan an koka kan yanda jami'an tsaro suke korar mutane daga wajan gobarar. Wani Bidiyo da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta an ji wasu na zargin cewa akwai hannun gwamnati a lamarin.
Okowa dan gashi gareshi, shi ne dalilin da yasa Atiku ya fadi zabe a 2023>>PDP

Okowa dan gashi gareshi, shi ne dalilin da yasa Atiku ya fadi zabe a 2023>>PDP

Duk Labarai
Shugaban marasa Rinjaye na majalisar Dattijai Abba Moro ya bayyana cewa, Tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa da ya koma APC ne silar faduwar PDP zaben shugaban kasa a 2023. Yace Okowa ko jiharsa bai ci ba, inda yace da wani aka dauko daga kudu ba Okowa ba da za'a iya samun Nasara. Ya fadi wannan maganane a matsayin ga Ifeanyi Okowa da yace yayi dana sanin yin takarar neman shugabancin kasa da Atiku. Moro yace Ifeanyi Okowa idi rufe ya je PDP yana neman a bashi takarar mataimakin shugaban kasa inda yace babu wanda ya tursasashi.
Gyaran matatar man fetur din Fatakwal, Warri da Kaduna yaudarace ba gyaran ake ba>>Inji Masana

Gyaran matatar man fetur din Fatakwal, Warri da Kaduna yaudarace ba gyaran ake ba>>Inji Masana

Duk Labarai
Wani masani a fannin makamashi kuma me sharhi akan al'amuran yau da kullun, Kelvin Emmanuel ya bayyana cewa gyaran matatun man fetur din Najeriya, Fatakwal, Warri da Kaduna duk yaudarace. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a channels TV. Hakan na zuwane yayin da sabbin rahotanni ke cewa matatar man Warri da aka ce ta dawo aiki, wata daya ta yi tana aiki ta tsayawa tun watan Janairu da ya gabata. Matsalar rashin aikin mamatun man fetur din Najeriya matsala ce da ta dade ana fama da ita wadda gwamnatoci da yawa suka kasa shawo kanta.
Hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya ta yi hasashen samun Gajimare da tsawa a fadin kasar

Hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya ta yi hasashen samun Gajimare da tsawa a fadin kasar

Duk Labarai
Hukumar sararin samaniya ta Najeriya, (NiMet) ta yi hasashen samun Gajimare da rana a wasu sassan Najeriya daga ranar Laraba har zuwa Juma'a. A sanarwar data fitar ranar Talata a Abuja, Hukumar tace za'a samu rana a jihohin Arewa daga ranar Laraba zuwa Juma'a. Tace amma za'a iya samun hadari a sararin samaniyar jihohin Kaduna, Adamawa, Sokoto, Kebbi, Zamfara da Taraba da kuma tsawa. Hakanan tace a jihohin Benue, Plateau, Niger, Kwara da Kogi ma abinda ake tsammanin zai faru kenan. A jihohin Delta, Cross River, Akwa Ibom, Rivers da Bayelsa kuma sun ce za'a samu hasken rana da safe inda suma ana tsammanin Hadari da tsawa. A jihohin Kebbi, Taraba, Borno da Adamawa kuwa hukumar tace za'a tashi ranar Alhamisbda tsawa.
Dodar Ta tabbata, Kowa ya shaida mulkin Adalci na Shugaba Tinubu dan haka 2027 zai zarce>>Ganduje

Dodar Ta tabbata, Kowa ya shaida mulkin Adalci na Shugaba Tinubu dan haka 2027 zai zarce>>Ganduje

Duk Labarai
Shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa Mulkin Adalci na shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yasa 'yan jam'iyyar PDP ke ta komawa APC. Ya bayyana hakane a Asaba, babban birnin jihar Delta yayin karbar gwamnan jihar, Sheriff Oborevwori da ya koma APC. Ganduje yace cin zaben 2027 ya tabbata ga Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Ya kuma ce akwai karin gwamnonin PDP da zasu koma APC.
Likitoci sun mana kadan matuka duk sun tsere kasashen waje>>Jihar Kwara ta koka

Likitoci sun mana kadan matuka duk sun tsere kasashen waje>>Jihar Kwara ta koka

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Kwara ta koka da karancin Likitoci a jihar inda hukumomin jihar sukace duk likitoci da yawa sun tsere kasashen waje. Shugaban hukumar kula da asibitoci na jihar, Abdulraheem Abdulmalik ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar. Yace a yanzu likitocin da suke dasu guda 99 ne maimakon 180 zuwa 200 da jihar Ke bukata. Yace suna neman likitoci su dauka amma babu, yace a kwankin baya likitoci 3 da suka tsere daga jihar sun koma bakin aiki bayan da aka yi karin Albashi. Yace babbar hanyar magance wanan matsala itace a samu a rika daukar nauyin dalibai suna koyan aikin likitanci inda daga baya sai su dawo su yiwa jihar aiki.
Ra’ayinane ba tsoron EFCC ba yasa na koma APC, kuma idan dai ana son Najeriya ta dore a matsayin dunkulalliyar kasa sai an zabi Tinubu a 2027>>Okowa

Ra’ayinane ba tsoron EFCC ba yasa na koma APC, kuma idan dai ana son Najeriya ta dore a matsayin dunkulalliyar kasa sai an zabi Tinubu a 2027>>Okowa

Duk Labarai
Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa, Ifeanyi Okowa da ya koma jam'iyyar APC daga PDP yace ba tsoron EFCC ne yasashi komawa APC ba. A baya dai Hukumar EFCC ta fara binciken Okowa akan zargin batan Naira Tiriliyan 1.3 wanda daga baya kuma sai gashi ya koma jam'iyya me mulki ta APC. Hakana a baya tsohon shugaban jam'iyyar, Adams Oshiomhole ya taba fadar cewa duk dan siyasar da ya shiga APC an yafe laifinsa. Wannan yasa mutane ke tunanin cewa dalili kenan da Okowa ya koma APC, amma ya musata hakan. Ya kara da cewa, zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a shekarat 2027 shine zai sa kasanan ta dore a matsayin dunkulalliyar kasa.
Idan kace zaka yi aikin Gwamnati tsakani da Allah a Najeriya na zaka kare da ko sisi ba>>Inji Shugaban Kungiyar kwadago, NLC, Joe Ajaero

Idan kace zaka yi aikin Gwamnati tsakani da Allah a Najeriya na zaka kare da ko sisi ba>>Inji Shugaban Kungiyar kwadago, NLC, Joe Ajaero

Duk Labarai
Shugaban kungiyar Kwadago, NLC, Joe Ajaero ya bayyana cewa, duk wanda yace zai zama m'aikaci na gari ya rika zuwa aiki kullun to ba zai tsira da ko sisi ba a cikin Naira dubu 70 din da ake biya a matsayin mafi karancin Albashi. Ya bayyana hakane a Abuja wajan wani taro da aka gudanar. Yace amma duk da Dubu 70 din ma bata isa, a haka wasu jihohin baa biyan dubu 70 din a matsayin mafi karancin Albashi. Yace ma'aikata da yawa sun samu ragi ne ma daga abinda suke karba kamin karin Albashin inda yace hakan ya farune saboda hauhawar farashin kayan abinci da kuma harajin da ake cirewa. Ya kara da cewa, wasu jihohin kuma Naira dubu 5 kawai suka karawa ma'aikatan.