Na cikawa Al’ummar Kano yawancin Alkawuran dana musu>>Gwamna Abba Gida-Gida
Na cika kashi 85% na alƙawuran da na ɗauka a lokacin yakin neman zabe na – Gwamna Yusuf.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ce gwamnatinsa ta aiwatar da kashi 85 cikin 100 na alkawuran da ta dauka wa al’ummar jihar, inda ya rage kashi 15 cikin 100 yayin da yake shiga shekara ta biyu na wa’adin mulkinsa na farko.
Daily Trust ta rawaito cewa gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke rantsar da sabon Shugaban Ma’aikata na Jihar, Dr Sulaiman Wali Sani; Darakta Janar na Hukumar Ayyuka na Musamman, Manjo Janar Sani Muhammad (mai ritaya), da kuma Masu Ba da Shawara na Musamman guda 11, a ranar Alhamis.
Ya bayyana cewa wannan nasara ta kasance sakamakon tantancewar da aka yi kan ayyukan gwamnatinsa a cikin shekaru biyu da suka gabata.
“Na yi farin ciki cewa makon da ya g...








