Sunday, February 15
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyon: ina cikin malaman da aka rika biya kudi suna tallata takarar Muslim Muslim

Kalli Bidiyon: ina cikin malaman da aka rika biya kudi suna tallata takarar Muslim Muslim

Duk Labarai
Malam ya bayyana cewa yana cikin malaman da aka rika biya kudi suna tallata takarar Muslim Muslim. Yace har so suke a rika tafiya dasu saboda akwai alawus kuma su sun yi ne tsakani da Allah dan babu Musulmi da za'a kawowa 'yan takarar Muslimi da Musulmi yace baya sonsu. Malam ya zargi manyan malamai da suka rika tallata Muslim Muslim din da yin shiru inda yace su kana ne aka bari suna magana. Yace amma ga gwamnatin nan tsare-tsaren ta na wahalar da al'umma ne. https://twitter.com/i/status/2009801514387419283
Akon Ya je kallon wasan Senegal da Mali: Kalli Bidiyon yanda ya rika murna bayan da Senegal ta ci kwallo

Akon Ya je kallon wasan Senegal da Mali: Kalli Bidiyon yanda ya rika murna bayan da Senegal ta ci kwallo

Duk Labarai
Tauraron mawakin Kasar Senegal, Akon ya harlarci wasan da kasarsa ta buga da kasar Mali. Wasan ya kare Senegal na cin 1-0. An ga Akon ya tashi yana murna bayan da Ndiaye yaciwa Senegal Kwallon da ta basu nasara inda ya rika cewa dama ya fada. https://twitter.com/i/status/2009755389764555007 Bayan Wasan an ga Akon da Sadio Mane suna gaisawa inda Akon ke cewa, zai kasance tare dasu har su yi nasara. https://twitter.com/i/status/2009899112754184389
Kalli Bidiyon: An bayyana wani Abu marar dadi da kasar Amùrķà zatawa shugaba Tinubu

Kalli Bidiyon: An bayyana wani Abu marar dadi da kasar Amùrķà zatawa shugaba Tinubu

Duk Labarai
Malamin Kirista, Primate Ayodele ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi hattara dan kuwa zai gamu da kalubale da yawa Ya bayyana cewa, Kasar Amurka zata shirya abubuwa da zarge-zarge akan Tinubu din. Yace kuma Gwamnonin dake ta komawa APC zasu ci amanar shugaban kasar. Ya bayyana hakane ga mutanen cocinsa. https://twitter.com/i/status/2009587959490637969
‘Yar Najeriya ta farko ta samu Mukamin Brigadier General a gidan sojan kasar Amurka

‘Yar Najeriya ta farko ta samu Mukamin Brigadier General a gidan sojan kasar Amurka

Duk Labarai
Amanda Azubuike wadda ke aiki da sojan Amurka, ta zama mace ta farko kuma 'yar Najeriya data kai matsayin Brigadier General. Shekarunta 57 kuma hakan ya sa ta zama wata abin koyi ga mata masu neman su zama jajrirtattu a fanno ni daban-daban na rayuwa. Mahaifin ta dan Najeriya ne inda mahaifiyarta kuma 'yar kasar Zimbabwe ce, Mahaifanta sun hadu ne a kasar Ingila inda suka yin aure. Saidai daga baya sun rabu inda mahaifiyarsu ta daukesu suka koma kasar Amurka da zama.
Ji matakin da dan Kwankwaso ya dauka akan komawar Abba Kabir Yusuf APC

Ji matakin da dan Kwankwaso ya dauka akan komawar Abba Kabir Yusuf APC

Duk Labarai
Rahotanni daga Kano sun bayyana cewa, dan jagoran Kwankwasiyya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso me suna, Mustapha wanda kwamishinan matasa da wasannine zai ajiye aikinsa. Hakan na zuwane bayan da Abban ke shirin komawa jam'iyyar APC. Rahoton yace ba Mustapha Kwankwaso ne kadai zai ajiye aikin nasa ba, hadda karin wasu kwamishinoni dake aiki tare da gwamnatin Kanon. Rahotanni sun bayyana cewa, Dangantaka ta yi tsami tsakanin Abba da Kwankwaso tun bayan data bayyana a zahiri cewa Abba zai koma jam'iyyar APC.
Jam’iyyun NNPP, PDP, da ADC na tattauna yanda zasu hade dan kayar da Tinubu a 2027

Jam’iyyun NNPP, PDP, da ADC na tattauna yanda zasu hade dan kayar da Tinubu a 2027

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyun Adawa na NNPP da PDP da ADC na tattaunawa dan hadewa waje daya su kayar da shugaba Tinubu zabe a shekarar 2027. Hakan ya fito ne daga bakin me magana da yawun jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi. Ya bayyana cewa yanayin mulkin da APC ke yi a Najeriya baya bayar da sakamakon da ake bukata. Fan hakane ake bukatar hada kai dan kayar da ita mulki a 2027. https://twitter.com/i/status/2009710056368156994
Kalli Bidiyon: Ji Sabon Sunan da Kwankwaso ya sakawa Abba

Kalli Bidiyon: Ji Sabon Sunan da Kwankwaso ya sakawa Abba

Duk Labarai
A yayin da siyasar Kano ta Dauki Dumi. Shugaban tafiyar Kwankwasiyya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya fara mayar da martani a yayin da ake tsammanin gwamnab Kano, Abba Kabir Yusuf zai koma jam'iyyar APC. A wajan wani taro, Kwankwaso yace duk wanda ya bar tafiyarsu ta Kwankwasiyya, sunan siyasarsa 'yar Wada. https://twitter.com/i/status/2009515958189080598 Kwankwaso a baya dai ya bayyana cewa, Kamata yayi Abha ya ajiye musu kujerarsu kamin ya koma APC.