Saturday, December 20
Shadow

Duk Labarai

A kokarin da masana kimiyya ke yi na Gano karshen Kasar da muke takawa, sun samu ci gaba inda suka yi nisa sosai a hakar da suke yi amma har yanzu basu kai karshen kasar ba

A kokarin da masana kimiyya ke yi na Gano karshen Kasar da muke takawa, sun samu ci gaba inda suka yi nisa sosai a hakar da suke yi amma har yanzu basu kai karshen kasar ba

Duk Labarai
Masana kimiyya sun sanar da samun gagarumar ci gaba a kokarin da suka shafe shekara da shekaru suna yi na ganin sun gano karshen kasar da muke takawa. Masanan dai suna haka ce kamar yanda ake haka rijiya dan gano karshen kasa. A wannan karin sun ce sun yi haka a karkashin kasa da nisanta ya kai mita 1,268, wannan ba karamin ci gaba bane lura da cewa a farko burinsu shine su yi hakar da nisanta bai wuce mita 200 ba. Dalilin su na ci gaba da hakar shine sun ga lamarin yana da dauki ba kamar yanda suka yi tsammanin zasu sha wahala ba Saidai har yanzu basu kai karshen kasa ba. Kasar Amurka ce dai ke daukar nauyin wannan aiki, saidai ta dakatar da bayar da kudin gudanar da aikin wanda hakan ke barazana ga ci gaban aikin.
Hankula sun tashi bayan da Masu kutse suka kwashewa mutane kudinsu a Bankin Union Bank har Naira Biliyan 9.3

Hankula sun tashi bayan da Masu kutse suka kwashewa mutane kudinsu a Bankin Union Bank har Naira Biliyan 9.3

Duk Labarai
Rahotanni sun ce masu kutse sun kwashewa Kwastomomi kudadensu har Naira Biliyan 9.3. Rahoton yace bankin na ta kokarin ganin ya dawo da wadannan kudade da aka sace. Sannan tuni aka rufe wasu asusun ajiya da ake tsammanin na da alaka da satar. Lamarin ya farune ranar 23 ga watan Maris da ya gabata. Bankin a ranar 2 ga watan Afrilu ya nemi kotu ta bashi damar kulle wasu asusun banki da suka ce har yanzu ana amfani dasu wajan satar kudaden. Ba wannan ne karon farko ba, Watanni 15 da suka gabata sai da babban bankin Najeriya CBN ya rushe hukumar gudanarwar bankin kan irin wannan lamari
Sarakunan Inyamurai sun ce Tinubu ne zabinsu a 2027

Sarakunan Inyamurai sun ce Tinubu ne zabinsu a 2027

Duk Labarai
Sarakunan yankin Inyamurai sun yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu alkawarin samar masa akalla kaso 70 cikin 100 na kuri'un da za'a kada a yankunansu. Sarakunan wanda basaraken Abia, Eze Nnamdi yake jagoranta sun bayyana hakane yayin da suka kaiwa mataimakin kakakin majalisar dattijai, Benjamin Kalu ziyara a gidansa dake Abia Sunce babban dalilin ziyararsu shine dan mika godiya ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bisa kafa ma'aikatar raya yankinsu. Sannan sun kuma Godewa Sanata Kalu saboda kokarin da yayi na kafa wannan ma'aikata.
Ji Yadda ma’aikacin banki ya riƙa naɗar bidiyon tsìraìcìn abokan aikinsa mata a Najeriya, ya nadi Bidiyo 400

Ji Yadda ma’aikacin banki ya riƙa naɗar bidiyon tsìraìcìn abokan aikinsa mata a Najeriya, ya nadi Bidiyo 400

Duk Labarai
Yadda ma'aikacin banki ya riƙa naɗar bidiyon tsiraicin abokan aikinsa mata a Najeriya. Rundunar ƴansanda a jihar Legas da ke Najeriya ta ce za ta gurfanar da tsophon ma'aikacin bankin Access wanda ake zargi da ɗaukar hotunan tsiraicin abokan aikinsa mata. Wannan na zuwa ne bayan wata sanarwa da bankin ya fitar a ranar Litinin inda ya bayyana cewa ya miƙa batun zargin ɗaya daga cikin ma'aikatansu a ɓangaren hulɗa da abokan cinikayya, na ɗaukar hotunan tsiraici ga hukumomi. Sanarwar da suka wallafa a shafin sada zumunta ta ce bankin zai bai wa hukumomi haɗin kai, kuma bankin zai ci gaba da kare mutuncin ma'aikatansa. Bayani da ya fita a makon da ya gabata ya nuna cewa wani ma'aikacin bankin Access ya naɗi bidiyoyin abokan aikinsa mata a cikin ban-ɗaki ba tare da saninsu ba....
Kalli Bidiyo: Bayan ya bayar da hakuri kan bidiyonsa da aka gani yana rabawa ‘yansanda kudi, An kuma kara ganin dan Chinar nan yana watsawa ma’aikatansa kudi a wajan hakar ma’adanai

Kalli Bidiyo: Bayan ya bayar da hakuri kan bidiyonsa da aka gani yana rabawa ‘yansanda kudi, An kuma kara ganin dan Chinar nan yana watsawa ma’aikatansa kudi a wajan hakar ma’adanai

Duk Labarai
Dan kasar Chinar nan da kwanakin baya aka ganshi a wani Bidiyo da ya yadu sosai yana rabawa 'yansandan Najeriya kudi wanda har daga baya ya fito ya bada hakiri, ya sake aikata laifin. A wannan karin, ganinsa aka yi yana watsawa ma'aikatansa kudi a kasa suna rububi a wajan hakar ma'adanai. https://twitter.com/thecableng/status/1916889365088784551?t=4ZnGGNlAc-i4iQe5INZGVw&s=19 Wannan dai cin zarafin Naira ne kamar yanda hukumar EFCC ta Haramta yin hakan. Abin jira a gani shine wane hukunci ne hukumomi zasu dauka a kansa.
Ji yanda ta kaya bayan da Na Yi Ido Biyu Da Wanda Suka Yi Gàrkùwà Da Ni A Masallacin garin mu, inji Cmr. Mb Muhammad

Ji yanda ta kaya bayan da Na Yi Ido Biyu Da Wanda Suka Yi Gàrkùwà Da Ni A Masallacin garin mu, inji Cmr. Mb Muhammad

Duk Labarai
Yadda Na Yi Ido Biyu Da Wanda Suka Yi Garkuwa Da Ni A Masallaci, inji Cmr. Mb Muhammad. "Na yi alwala zan yi Sallah a gidan man Shema dake Bakin Ruwa Kaduna, sai na ga daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da ni a masallacin shi ma zai yi sallah. Bayan mun idar a Salla sai na tambaye shi ka gane ni? Yace eh ya gane ni, amma yanzu amma yanzu na tuba na daina wannan mummunar harkar ta ta'aďdancin, yanzu haka ma sana'ar acaba nake yi don na rufawa kaina da iyalina asiri. Sauran abokanan sana'ar mu wasu an kashe su wasu kuma sun tuba inji shi dan ta'aďdan, daga karshe na ce na yafe masa kuma na yi masa alkairi". Shin idan kai ne za ka yafe masa? Daga Madubi H
Ina Son In Sanar Al’ummar Jihar Katsina Da Ku Cewar “Shugaban Kasa Bola Tinubu Zai Zo Jihar Katsina Kuma Ya Kwana, Wanda Bai Taɓa Yi Ba A Cikin Jihohin Najeriya, Bayan Mahaifarsa Jihar Legas, Domin Taya Mu Murna Da Kuma Ƙaddamar Da Ayyuka. Ina Kira Ga Al’ummar Jihar Katsina Su Fito Tarbar Shugaban Kasa”.

Jihar Katsina Za Ta Zama Jiha Ta Farko A Cikin Jihohin Nijeriya Da Shugaba Tinubu Zai Zo Ya Kwana Tun Bayan Rantsar Da Shi, Banda Legas, Cewar Gwamna Dikko Radda Ina Son In Sanar Al'ummar Jihar Katsina Da Ku Cewar "Shugaban Kasa Bola Tinubu Zai Zo Jihar Katsina Kuma Ya Kwana, Wanda Bai Taɓa Yi Ba A Cikin Jihohin Najeriya, Bayan Mahaifarsa Jihar Legas, Domin Taya Mu Murna Da Kuma Ƙaddamar Da Ayyuka. Ina Kira Ga Al'ummar Jihar Katsina Su Fito Tarbar Shugaban Kasa". Daga Jamilu Dabawa, Katsina