Saturday, December 13
Shadow

Duk Labarai

Matashi Ba Taliya Ko Ƴan Kuɗi Yake Buƙata Daga Wajen Ƴan Siyasa Ba Face A Gina Rayuwarsa-Inji Sanata Ahmad Babba Kaita

Matashi Ba Taliya Ko Ƴan Kuɗi Yake Buƙata Daga Wajen Ƴan Siyasa Ba Face A Gina Rayuwarsa-Inji Sanata Ahmad Babba Kaita

Duk Labarai
Daga Comr Nura Siniya Tsohon Sanata mai wakiltar shiyyar Daura a jihar Katsina Sen. Ahmad Babba Kaita, ya bayyana cewa matashin Najeriya ba Taliya ko 'yan kudi yake bukata daga wajen 'yan siyasa face a gina rayuwarsa don gobensa ta yi kyau. A cewar sa, Sanata Kaita rayuwar matasa a Najeriya ba za ta inganta da taliya ko kyautar naira daga hannun ‘yan siyasa ba. Ya kuma ce abubuwan da matasa ke buƙata da gaske sune: tsaro mai kyau, ingantaccen ilimi da kuma samun aikin yi ko sana'ar dogaro da kai. Sanatan ya jaddada cewa waɗannan ginshiƙai su ne tushen da ya gina siyasarsa a kai, kuma yana fatan ci gaba da bin wannan hanya don ganin rayuwar matasa A ƙarshe ya ce Ina siyasa ne don a gina rayuwar matasa. Ba wai domin jama’a su sa ni a dama da su ba. Ina fatan ganin matasan Najeriy...
An gayyaci Sanata Shehu Sani ya shiga cikin wadanda zasu yi Alkalancin budurwar da zata lashe sarauniyar kyau a Najeriya amma yace baya so dan ko tsakanin matansa bai iya yin alkalancin wadda tafi kyau ba

An gayyaci Sanata Shehu Sani ya shiga cikin wadanda zasu yi Alkalancin budurwar da zata lashe sarauniyar kyau a Najeriya amma yace baya so dan ko tsakanin matansa bai iya yin alkalancin wadda tafi kyau ba

Duk Labarai
An gayyaci tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya shiga cikin Alkalan da zasu yanke hukunci kan wadda zata lashe gasar Sarauniyar kyau ta Najeriya amma yace baya so. Tsohon sanata, Ben Bruce ne ya shirya wannan lamari wanda zai wakana a Otal din Federal Palace Hotel dake Legas. Sannan ya gayyaci Sanata Shehu Sani ya zama cikin Alkalai. Saidai a sanarwar da ya fitar ta shafinsa na sada zumunta, Sanata Shehu Sani yace baya son wannan gayyata kuma ba zai iya ba. Yace matansa ba zasu ji dadi ba idan yayi wannan alkalanci saboda ko a tsakaninsu bai iya fitar da wadda ta fi wata kyau ba dan haka ba zai iya alkalanci akan matan da bai sani ba. Saidai yace ya gode da wannan gayyata da aka masa.
Ministan ilimin Najeriya na so a faɗaɗa shirin NYSC zuwa shekara biyu

Ministan ilimin Najeriya na so a faɗaɗa shirin NYSC zuwa shekara biyu

Duk Labarai
Ministan ilimi na Najeriya, Olatunji Alausa ya yi kira da a faɗaɗa shirin yi wa ƙasa hidima, NYSC daga shekara ɗaya zuwa shekara biyu. Mista Alausa ya bayyana haka ne lokacin da ya kai wa babban daraktan hukumar, Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ziyara a ofishinsa ranar Juma'a. Haka kuma ministan ya buƙaci a faɗaɗa tare da inganta shirin koya wa masu yi wa ƙasa hidima sana'o'i. Minista ya kuma yaba wa ayyukan hukumar NYSC, musamman wajen tantance tare da gano matasan da suka je sansanonin NYSC da takardun kammala karatu na bogi. Ya kuma ce ma'aikatarsa za ta ci gaba da aiki tare da da hukumar wajen inganta harkokin ilimi a faɗin ƙasar. Mista Alausa ya kuma yi kira da a riƙa tura masu yi wa ƙasa hidima domin koyarwa a makarantun ƙauyuka da karkara, domin cike giɓin malaman da ...
Kalli Sabbin Hotunan Tsohuwar jarumar fina-finan Hausa, Sadiya Gyale

Kalli Sabbin Hotunan Tsohuwar jarumar fina-finan Hausa, Sadiya Gyale

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Da Yawan Wadanda Suka San Wannan Jarumar Finafinan Hausan A Shekarun Baya, Idan Aka Ce Musu Ita Ce Ta Zama Haka Ba Za Su Yarda Ba. Ko kun gane ta?
Gayyatar Da Rundunar ‘Yan Sanda Suka Yi Wa Sarki Sanusi II Çin Fùška Nè Ga Masarautun Arèwa, Ra’ayin Barista Nuhu Dantani

Gayyatar Da Rundunar ‘Yan Sanda Suka Yi Wa Sarki Sanusi II Çin Fùška Nè Ga Masarautun Arèwa, Ra’ayin Barista Nuhu Dantani

Duk Labarai
Wannan fa cìn mutuncin ne ga ilahirin mutanen Arewa ne ba kawai Kano ba. Hatta sarautar gargajiya na ilahirin Arewa a nawa hangen! Duk dama 'ýan sanda suna da damar gayyatan kowaye a Nijeriya idan dai har ana tuhumar shi da wani laifi amma ya kamata a yi abu cikin adalci da kuma mutunci. Wasu za su yi murna, amma wannan abunda IGP ya keyi cin mutunci ne ga Sarautar Gargajiyarmu. Don haka ina mai rokon shugaban 'yan sanda na kasa da ya sake yin duba da wannan wasikar gayyatar, ya kuma samo wata hanya ta magance wanna matsala.
DA DUMIDUMINSA: Kotu Ta Tura Mawaƙi Surajo Mai Asharalle Zuwa Gidan Yari a jihar Katsina

DA DUMIDUMINSA: Kotu Ta Tura Mawaƙi Surajo Mai Asharalle Zuwa Gidan Yari a jihar Katsina

Duk Labarai
Daga Comr Nura Siniya Wata Kotu ta tura fitaccen mawaƙin Asharalle a jihar Katsina Alhaji Surajo Mai Asharalle zuwa gidan gyaran hali har ya zuwa lokacin da za a cigaba da shari'a akan zargin da ake masa na harbin wasu jami'an hukumar Hisba a jihar Katsina Majiyar tace lauya mai kare Alhaji Surajo mai Asharalle, ya ce kotu ta dage shari'ar zuwa ranar Alhamis 10 ga Aprilu 2025 domin ci gaba da sauraren kara. An dai zargi Alhaji Surajo mai Asharalle da ya'yansa biyar da yin harbi a lokacin rikicinsu da Hukumar Hisba a gidansa dake ƙofar Ƙaura a jihar Katsina.