Orji Kalu Ya Zama Jarumin Gusau.
Mai Martaba Sarkin Gusau A Jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Bello Ya Naɗa Tsohon Gwamnan Jihar Abia Sanata Orji Uzor Kalu, Sarautar Jarumin Gusau, Yau Litinin.
Daga Jamilu Dabawa
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false}
ABIN TAUSAYI: Tun Yaron Yana Dan Watanni Hudu Da Haihuwa Suka Rabu Da Mahaifiyarsa, Hakan Ya Sa Bayan Girma Yake Fita Da Shi Aikin Achaba Saboda Babu Mai Kula Masa Da Shi
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu; Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike; Karamar Ministan Abuja, Mariya Mahmoud, da Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, da sauran manyan baki a yayin kaddamar da aikin inganta cibiyar rarraba ruwan sha ta babban birnin Abuja a yau Litinin.
Ministan Tsaro, Badaru Ya Wakilci Tinubu A Taron Nazari Kan Kundin Tsarin Mulki.
Mai girma ministan tsaron Najeriya, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, CON, MNI, a yau Litinin, 16 ga watan Yuni, 2025, ya wakilci mai girma shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a wajen taron nazari kan kundin tsarin mulki a tsakanin masu ruwa da tsaki kan dokoki dangane da tsarin tsaron ƙasa, wanda aka gudanar a cibiyar daƙile ayyukan ta’addanci da ke ofishin babban mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, Abuja.
Taron wanda kwamitin nazari kan kundin tsarin mulkin ƙasa na majalissar wakilai ya shirya tare da haɗin gwiwar ofishin babban mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro da sauran hukumomin tsaro, ya samu halartar manyan jami’an tsaro da ƙwararrun masana kan dokoki da tsare-tsare.
...
Wani mummùñan lamari ya faru a filin wasan kwallo na Shagari Quarters dake cikin garin Kano, inda wasu bata-gari suka kàśhe wani matashi mai suna Baba, ɗan asalin Jos, a cikin filin wasa.
Yadda lamarin ya auku shine, wanda aka kaśhe, Baba, yana cikin wasa ne lokacin da ya ci kwallo, sai jikinsa ya bige wani yaro da ake kira Bello (Belloty). Alkalin wasa bai busa ketar ba, wanda hakan bai yi wa Belloty dadi ba. Bayan an kammala wasan, Belloty ya bi Baba da zargin me ya sa ya bige shi, hatsaniya ta barke tsakaninsu.
Abokin Belloty, wanda ake kira Hafizu (wanda aka fi sani da “Mata”), ya miƙa masa almàķashi, inda Belloty ya caka wa Baba cìkin źùçiya, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa a nan take.
Belloty (wanda ya caka almakashi) da Hafizu “Mata” (wanda ya mika almakashiñ) dukkan...
Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da rahoto kan kasashen dake fuakantar ibtila'in yunwa su 13.
Rahoton yace kasashen Gaza, Sudan, South Sudan, Haiti,da Mali na fuskantar yunwa nan take idan ba an kai musu dauki ba.
Rahoton yace rashin tsaro, Rashin tabbas na tattalin arziki da canjij yanayi ne ya kawo lamarin yunwar.
Rahotanni ya bayyana matsalar tsaro a Arewacin Najeriya wanda yace zai iya kara kazancewa.
Rahoton yace matsalar tsaron Arewar zai kara jefa mutane cikin yunwa saboda za'a raba mutane da yawa da muhallinsu.
A yayin da dambarwa da rade-radi suka kunno kai cewa, za'a iya canja mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima kamin zaben 2027.
'Yan Fim sai fitowa suke suna nuna suna goyon bayan Kashim Shettima.
Rahama Sadau ta fara fitowa ta nuna goyon baya ga kashim daganan kuma sai Shamsu Dan iya.
A yanzu kuma Mansurah Isah itama ta fito ta nuna tana tare da Kashim Shettima.
Mansurah Isah ta wallafa hoton kashim inda ta kirashi uba kuma shugaba na gari.
Mataimakin shugaban jam'iyyar APC shiyyar Arewa maso gabas, Mustapha Salihu yayi karin haske kan rashin kiran sunan Shettima da yayi a wajan taron jam'iyyar APC na masu ruwa da tsaki daga yankin Arewa maso gabas.
Lamarin dai ya jawo hatsaniya sosai.
A hirarsa da Channels TV, Mustapha Salihu yace kamin ya bayyana Tinubu a matsayin zabinsu na dan takarar APC a 2027, dai da ya gama yabon Kashim Shettima.
Yace Kuma a dokar jam'iyya Shugaban kasa kadai yake yin zaben fidda gwani ba tare da mataimaki ba, sai idan an kammala zabene sai ya dauko wanda yake so ya mai mataimaki.
https://twitter.com/channelstv/status/1934690994139591081?t=XDjrbwb3Vn5SVTYWSwAhGg&s=19
Cikin wadanda basu ji dadin wannan abu ba, hadda Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum.
Sunce ta karewa Adam A Zango baya da kowa sai gashi har aljanu ke cika mana asibiti wajen dubiyar ganinsa saboda yawan jama'a ko aljanun sai sunyi kwana biyu suke samun damar ganinsa, komai zamanka celebrity a Kannywood sai kayi hakurin bata lokaci a waje kafin ka samu shiga dubiyar Adamu Zango a dakinsa, idan baka yi hakurin ba saidai ka fita
Bantaba ganin celebrity a wannan yankin namu wanda yake da masoyan gaskiya ( Fan) ba irin Adamu Zango, masoyansa ba wanda ya siya da kudi ko karya ko da yarjejeniya sai don kauna da soyayyar gaskiya a tsakaninsa da masoyansa
Adamu Zango bawan Allah, muna rokon Allah ya kara baka lafiya Boss.
Daga Saifullahi Safzor