Saturday, April 25
Shadow

Duk Labarai

Kungiyar Direbobin Tanka ta koka da shirin Dangote na fara jigilar man fetur dinsa inda tace zai sa su rasa aiki

Kungiyar Direbobin Tanka ta koka da shirin Dangote na fara jigilar man fetur dinsa inda tace zai sa su rasa aiki

Duk Labarai
'Yan kasuwar man fetur da yawa na ganawa bisa yunkurin Matatar Dangote na fara rarraba man fetur dinsa a fadin Najeriya da tankokinsa. A ranar June 15 Matatar Dangote tace tana shirin kawo tankokin dakon man fetur 4000 da zasu fara jigilar man fetur din Dangoten zuwa sassa daban-daban na kasarnan daga ranar 15 ga watan Augusta me zuwa. 'Yan kasuwar sun ce suna tattaunawa kan lamarin dan daukar matakin da ya dace. Sun koka da cewa wannan yunkurin na Dangote zai saka 'yan kasuwa da yawa su karye
Kwanan nan mutane zasu daina yadda da kariyar gwamnati zasu fara tashi tsaye suna kare kansu>>David Mark

Kwanan nan mutane zasu daina yadda da kariyar gwamnati zasu fara tashi tsaye suna kare kansu>>David Mark

Duk Labarai
Tsohon Kakakin majalisar Dattijai, Sanata David Mark ya bayyana cewa, Kwanannan mutane zasu daina yadda da cewa gwamnati zata karesu inda zasu fara tashi tsaye suna kare kansu. Mark ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Paul Mumeh inda yace lamarin tsaro ya kazance. Ya jawo hankalin gwamnati data dauki mataki ko kuma nan gaba kadan mutane zasu fara tashi tsaye suna kare kansu. Ya bayyana hakane a yayin da aka kaiwa jiharsa ta Asali, Benue hari inda aka kashe mutane sama da 100.
Darajar Naira 100 a shekarar da aka baiwa Najeriya ‘yanci watau 1960 a yanzu Naira Miliyan 1.1 ne

Darajar Naira 100 a shekarar da aka baiwa Najeriya ‘yanci watau 1960 a yanzu Naira Miliyan 1.1 ne

Duk Labarai
Kudin Naira kusan za'a iya cewa ya rasa darajarsa baki daya a cikin shekaru 65 da suka gabata. Bincike ya nuna cewa Naira 100 a shekatar da aka baiwa Najeriya 'yanci watau 1960 daidai take da Naira Miliyan 1.1 a yanzu. An alakanta faduwar darajar Nairar da hauhawar farashin kayan masarufi da Karya darajar Nairar da kuma rashin iya gudanar da tattalin arziki. Hakan dai ba karamin ci baya bane ga Najeriya. An samo wadannan bayanai daga World Data ne.
Farashin kayan Masarufi ya sauka a Najeriya>>NBS

Farashin kayan Masarufi ya sauka a Najeriya>>NBS

Duk Labarai
Hukumar kididdi ta Najeriya, NBS tace farashin kayan masarufi ya sauka da kaso 22.97 a watan Mayu idan aka kwatanta da na watan Aprilu da yake kaso 23.71 cikin 100. NBS ta bayyana hakane a sanarwar data fitar ranar Litinin. Idan aka kwatanta da shekarar data gabata, farashin kayan masarufin na yanzu yana kan kaso 10.98% ne cikin 100 wanda shima za'a iya cewa ya sauka idan aka kwatantashi dana shekarar 2024 wanda yake akan maki (33.95%). Yawanci ana tattara farashin kayan abinci ne dana Haya dana ababen hawa wajan fitar da wadannan alkaluma.
Kano: Shugaban ƙaramar hukumar Wudil ya ɗauki nauyin ɗalibai mata 33 su karanci ilimin ungozoma

Kano: Shugaban ƙaramar hukumar Wudil ya ɗauki nauyin ɗalibai mata 33 su karanci ilimin ungozoma

Duk Labarai
Shugabann karamar hukumar Wudil, Abba Muhammad Tukur ya ɗauki nauyin karatun ɗalibai mata 33 domin su karanci aikin ungozoma, da nufin inganta lafiyar mata masu juna-biyu a yankin. Bayan daukar nauyin karatun nasu har su kammala, Tukur ya mikawa ɗaliban takardar samun gurbin karatu ta kwalejin koyar da harkokin aikin ungozoma da ke Kano. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren yada labaran shugaban karamar hukumar, Nura Mu'azu Wudil ya sanyawa hannu, inda ya ce qannan kuma kari ne kan ɗalibai mata 10 da tuni suka fara karatun. Sanarwar ta ce, Tukur ya duba muhimmancin ilimin ƴaƴa mata, inda ya kara da cewa, hakan ne ya sa ya ware kudade masu yawa don ba su Ilimi da kuma kawo karshen yawan samun mutuwar mata masu dauke da juna biyu. Tukur, a cewar Sakataren, ya...
Da Duminsa: Saboda munin hare-haren da aka kai jihar Benue, na dakatar da duk wani aiki da nake zan kai ziyara jihar Benue>>Shugaba Tinubu

Da Duminsa: Saboda munin hare-haren da aka kai jihar Benue, na dakatar da duk wani aiki da nake zan kai ziyara jihar Benue>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sanar da cewa ya dakatar da duk wani aiki da yake zai kai ziyara jihar Benue. Hakan na zuwane bayan da hare-haren da ake zargin fulani makiyaya da kaiwa suka yi sanadiyyar kisan sama da mutane 100 a jihar ta Benue. Zanga-zanga ta barke a jihar inda kuma aka kai jami'an tsaro na musamman. 'Yan Adawa tuni suka fara sukar shugaban kasar saboda zargin rashin nuna kulawa sosai akan lamarin. shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa zai kai ziyyara jihar Benue ranar Laraba. Ya fadi hakane a ranar Litinin a lokacin da yake kaddamar da wani shirin ruwa a Abuja. Ya jawo hankalin mutanen jihar ta Benue da su kai zuciya nesa su rika hakuri da juna.
Hare-haren da ake kaiwa jihar Benue sun kai matakin da ba zamu kauda kai ba>>Atiku Abubakar

Hare-haren da ake kaiwa jihar Benue sun kai matakin da ba zamu kauda kai ba>>Atiku Abubakar

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar yayi Allah wadai da hare-haren da aka kai jijar Benue. Atiku yace hare-haren sun kai matakin da ba za'a iya kauda kai ba. Yace wani abin takaici shine yanda ake harbawa masu zanga-zangar da suka fito suke nuna damuwa kan lamarin barkonin tsohuwa. Yace suna neman a basu tsaron rayuwarsu ne. Yace yana kira ga hukumomi su daina yin Allah wadai kawai su rika tashi tsaye suna daukar mataki. Yace kuma ba jihar Benue bace kadai akwai jihohin Zamfara, Katsina, Plateau, da Taraba dake fama da irin wannan matsala ta tsaro.
Mashaya giya sun yi barazanar fara zanga-zanga muddin gwamnati bata rage farashin giyar ba

Mashaya giya sun yi barazanar fara zanga-zanga muddin gwamnati bata rage farashin giyar ba

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Kungiyar mashaya giya a kasar Ghana sun baiwa gwamnatin kasarsu sati 3 ta sauke farashin giyar ko kuma su tsunduma zanga-zanga. Kungiyar tace membobinta Miliyan 16.65 dake fadin kasar zasu bazama zanga-zanga muddin Gwamnatin bata rage farashin giyar ba. Daya daga cikin membobin kungiyar, Moses Obuah ne ya bayyana hakan inda yace darajar kudin Ghana da ake cewa, Cedi ta karu dan haka suma suna kiran a rage musu farashin giyar dan samun saukin rayuwa. Ya koka da cewa, Abin taka...
An kai Jami’an tsaro na musamman jihar Benue bayan munanan hare-hare

An kai Jami’an tsaro na musamman jihar Benue bayan munanan hare-hare

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Rahotanni sun ce an kai jami'an tsaro na musamman jihar Benue bayan munanan hare-haren da suka faru a jihar. Gwamnan jihar, Hyacinth Alia ne ya bayyana hakan ta bakin kakakinsa, Mr Tersoo Kula a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Makurdi. Ya bayyana cewa yana tare mutanen jihar a takaicin da suke nunawa na harin da aka kai wanda yayi sanadiyyar kisan mutane Akalla 100. Gwamnan yace yana hada kai da jami'an tsaro na tarayya wanda yanzu haka sun kan hanyar zuwa jihar. ...
Bidiyo Da Duminsa: An gano hadimin shugaba Tinubu na munafurtarsa wajan kitsa yanda zai fadi zabe a 2027

Bidiyo Da Duminsa: An gano hadimin shugaba Tinubu na munafurtarsa wajan kitsa yanda zai fadi zabe a 2027

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tsohon hadimin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, Aliyu Audu ya bayyana cewa dalilin da yasa ya sauka daga mukamin me baiwa shugaban kasar shawara ta musamman shine yana munafurtar shugaban kasar. Yace ba zai yiyu ya ci gaba da zama a gwamnatin Tinubu ba bayan yasan cewa, yana kitsa yanda zai fadi zabe a shekarar 2027. Aliyu ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV inda kuma ya nanata cewa lallai zasu kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a za...