Wasu Daga Cikin Falalar Goman Farko Na Watan Zulhijja
Wasu Daga Cikin Falalar Goman Farko Na Watan Zulhijja.
…jama'a mu yada (sharing) wannan sako domin amfanar sauran jama'a
1) Allah Ya yi rantsuwa da su a cikin alQurani. Qur'an 89:2.
2) Sune Ayyamun Ma'alumat da Allah ya umurci ayi ambaton sa a ciki a suratul Hajj Qur'an 22: 28.
3) Aiki a cikin su yafi falala da lada da soyuwa ga Allah akan duk sauran kwanakin shekara. Bukhari no.926.
4) Ana so a yawaita Subhanallah, Walhamdulilllah, wallahu Akbar wa Lailaha illallah da karatun al-Qurani. Bukhari ya ruwaito.
5) Ana so a bayyana ambaton Allah a ciki domin a tunawa wanda yamanta. Abdullahi Ibn Umar da Abu-Hurairah sun kasance suna shiga kasuwa suna kabbara jamaa na kabbara da kabbarar su. Bukhari ya ruwaito .
6) Aikin Hajji yana cikin Ayukka mafi falala a cikin wadann...








