Gwamnan Jihar Kano ya bayar da Naira Miliyan 15 dan a ci gaba da kulawa da me cutar daji, Halisa Muhd
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Biyawa Halisa Muhd Naira Miliyan 15 Don Ci Gaba da Maganin Cututtukan da ke Damunta
Mai girma Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya sake nuna jajircewarsa wajen tallafawa marasa lafiya masu bukata ta musamman, inda ya biya Naira miliyan 15 domin ci gaba da maganin Halisa Muhd, wadda ke fama da cutar daji (cancer).
Wannan kudin na daga cikin tallafin da Gwamnan ya bayar domin taimakawa Halisa Muhd wajen samun magani mai tsada, bayan da ya riga ya biya kudin aikin farko da aka yi mata.
Fauziyya D. Sulaiman, Babbar Mai Ba Gwamna Shawara kan Harkokin Mabukata da Gajiyayyu, ta bayyana godiyarta ga Gwamnan bisa wannan taimako, tare da jaddada cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da tallafawa marasa lafiya da masu bukata ta musamman a jihar.
Wannan ...







