Telan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a yayin da yake aunashi ya dauki hankula.
An ga Bidiyon yana yawo a kafafen sada zumunta.
https://twitter.com/Choji_ES/status/1929601307658121501?t=d87gdwN5ICKzFfHtodzAIw&s=19
Da yawa dai sun ce suna neman Telan.
Sanata Orji Uzor Kalu dake wakiltar mazabar Abia North a majalisar Dattijai ya bayyana cewa wasu 'yan siyasa ne da manyan ma'aikatan Gwamnati da 'yan Kasuwa ke daukar nauyin ayyuka Kungiyar Bòkò Hàràm.
Ya bayyana hakanne a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels TV.
Yace kuma masu yin hakan suna yi ne dan kawai su hana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu iya gudanar da Gwamnatinsa yanda ya kamata.
Yace amma ba ta haka bane ake karbar mulki, yace yawanci suna yi ne dan su kwace mulki daga hannun Tinubu ba kudi bane a gabansu.
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta fara amincewa da batun biyan bashin Naira Tiriliyan 2 na wutar lantarki da akw binta.
Hakan kokarine na samar da ingantacciyar wutar Lantarki a Najeriya.
Na kusa da me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar makamashi, Eriye Onagoruwa ce ta bayyana hakan a wajan wani taron masu ruwa da tsaki na harkar wutar da aka gudanar.
Tace gwanatin na duba muhimmancin hakan wajan samar da wutr Lantarki me karfi. Inda tace gwamnatin na kokarin ganin ta samar da wata hanya ta bashi dan biyan wannan bashi musaman lura da karancin kudin da gwamnatin ke fama dashi.
Girgizar kasa ta faru a kasar Turkiyya inda mutane 69 suka jikkata.
Yawanci wadanda suka jikkatar sun diro ne daga benaye saboda fargabar kada gidan da suke ciki ya rushene.
Saidai mutum daya ya mutu.
Karfin girgizar kasar ya kai maki 6.2 kamar yanda masana suka sanar.
https://twitter.com/geotechwar/status/1929690994091741373?t=qa7qPmG2xXaNo2yyCcmrog&s=19
Kasar Turkiyya dai na daga cikin kasashe masu yawan fuskantar Ambaliyar ruwa.
Rahotanni daga jihar Naija na cewa, sama da mutabe 700 ne suka rasu a ambaliyar ruwan data auku a Mokwa dake jihar.
Rahoton BBC ne ya bayyana hakan inda kuma yace mutane da dama ne suka bace.
Gidaje da yawa sun rushe sannan 'yan uwa da yawa na ta binne mamatansu.
Muna fata Allah ya jikan Musulmai.
Rahotanni sun ce wani dan Bindiga me suna Dan Sadiya ya bayyana inda aka bayyana shi da cewa yafi Bello Tùrji illa.
Rahoton yace ya jagoranci kai hare-hare a jihar Zamfara wanda suka yi sanadiyyar kashe fararen hula da kuma kona kauyuka.
A cikin wasu Bidiyon da ya saki an ga ya nuna motar APC ta sojojin Najeriya da ya kwace wadda ake amfani da ita ana harbo jirgin sama.
An yi kira ga jami'an tsaro da su gaggauta daukar mataki akansa.
https://twitter.com/Edrees4P/status/1929462831486804314?t=oL_F3FzI0FsqZR9Rrwi0EQ&s=19
Ko kuna ganin wane mataki ya kamata a dauka akansa?
Rahotanni daga kasar Spain na cewa kasar ta bi sahun kasar Afrika ta Kudu wajan kai karar kasar Israyla kotun Duniya saboda zargin kisan kiyashi da Israyla kewa Falasdinawa.
Kasar Sifaniya dai ta dade tana kira ga kasashen Turawa da su kakabawa kasar Israyla takunkumi saboda kisan da takewa falasdinawa.
A kwanannan ne dai Birnin Barcelona na kasar ya yanke dukkan wata hulda da kasar Israela saboda kisan da sukewa Falasdiynawa.
Kasar Afrika ta kudu itace kasa ta Farko a Duniya data fara kalubalantar kasar Israela saboda kisan da takewa Falasdiynawa.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa, shine kashin bayan nasarar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi nasarar zama shugaban kasa a shekarar 2023.
Ya kuma bayyana aniyarsa ta goyon bayan shugaba Tinubun a zaben shekarar 2027.
Saidai hakan baiwa jam'iyyun adawa dadi ba inda suke ta sukarsa. Jam'iyyun da suka soki Wike kan bayyana ci gaba da goyon bayan shugaban kasa Bola Tinubu sun hada da NNPC, PDP, CUPP.
Wike ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a Abuja ranar Litinin.
Wike yace bai aikata laifin yiwa jam'iyyarsa ta PDP zagon kasa ba inda ya kalubalanci jam'iyyar da cewa idan kuma ya aikata laifin to su dakatar dashi.
Saidai mataimakin shugaban matasa na jam'iyyar PDP na kasa, Timothy Osadolor ya gayawa '...
Rahotanni dake fitowa daga tattaunawar kasar Iran da kasar Amurka akan shirin mallakar makamin kare dangi na kasar Iran din na cewa an samu sauyi.
Rahoton yace, a yanzu kasar Amurka ta amince kasar Iran ta ci gaba da inganta makamashin Uraniyum da zai bata damar mallakar makamin Nokiliya.
Saidai sharadi shine kada ta rika yin hakan da gaggawa kamar yanda take yi a yanzu.
Hakan na zuwane bayan da labarai suka bayyana cewa kasar ta Iran ta inganta makamin Uraniyum zuwa matakin kaso 60 cikin 100 wanda kiris ya rage mata ta kai matakin 90 cikin 100 wanda shine zai bata damar mallakar makamin kare dangi.
Hakanan a baya, kasar Iran ta rika yin watsi da bukatocin kasar Amurka na cewa ta daina inganta makamashin Uraniyum.
Wannan dai ba karamar nasara bace ga kasar Iran musamman i...
Mutumin Bauchi Zai Kai Ragon Sallah Gidan Tinubu A Legas Bayan Yunkurin Da Bai Kai Ga Nasara Ba.
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false}
Khamis Musa Darazo, wani masoyin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu daga jihar Bauchi, ya shirya kai wa shugaban kasa ragon Sallah a Legas a matsayin alamar godiya bisa amincewar da ya yi da lasisin hakar mai a Kolmani.
A wata hira da aka yi da shi ranar Litinin, Khamis ya shaida wa Vanguard cewa bayan tattaunawa da dattawa, ya yanke shawarar kai ragon zuwa jiharsa ta asali — Legas, da f...