Monday, February 23
Shadow

Duk Labarai

An yi Gàrkùwà da mutane da yawa a kusa da Barikin Sojoji a Abuja

An yi Gàrkùwà da mutane da yawa a kusa da Barikin Sojoji a Abuja

Duk Labarai
Rahotanni daga babban birnin Tarayya Abuja na cewa, masu garkuwa da mutane sun sace mutane da yawa a kusa da barikin sojoji ta Abacha Barracks dake Guzape. Lamarin ya farune da daren ranar Talata. Lamarin ya farune da misalin karfe 11:31pm kuma ya saka tsoro a zukatan mutane Mazauna Abuja. Hakan na zuwane biyo bayan garkuwa da mutane data faru a unguwannin Bwari, Kuje, da Gwagwalada wanda cikin wadanda aka yi garkuwar dasu hadda kananan yara da mata. Hukumar 'yansandan Birnin na Abuja sun tabbatar da faruwar lamarin inda suka ce sun kai dauki wajan da lamarin ya faru kuma sun gano motoci biyu wanda ake tsammanin mutanen ciki ne aka yi garkuwa dasu. Ciki hadda Hon. Shagala Samuel. 'Yansandan sunce sun bincike dazukan dake kusa da inda aka yi garkuwa da mutanen amma basu ga wa...
Matar data fi kowace mace kudi a Najeriya da Afrika, Folorunso Alakija ta makance

Matar data fi kowace mace kudi a Najeriya da Afrika, Folorunso Alakija ta makance

Duk Labarai
Matar da tafi kowace mace kudi a Najeriya da Afrika, Folorunso Alakija ta makance kwata-kwata inda ta daina gani gaba daya. Rahoton hakan ya fito ne daga kafar Sahara Reporters inda suka ce ta samu wannan matsalane dalilin hawan jini. Lamarin ya farane a yayin da suke tafiya tare da mijinta a cikin jirgi inda jirgin ya so samun tangarda. Daga nan ne dai sai ta fara ganin hazo-hazo, wasu na kusa da ita sun bayyana cewa bata dauki wani matakin neman magani da muhimmanci ba kan lamarin wanda hakanne yasa ta kai ga makancewa gaba daya.
Kalli Hotunan Gawurtaccen me Gàrkùwà da mutane da jami’an tsaro suka kama

Kalli Hotunan Gawurtaccen me Gàrkùwà da mutane da jami’an tsaro suka kama

Duk Labarai
Jami'an tsaro sun kama masu garkuwa da mutane dan karbar kudin Fansa su biyu a Barkin Ladi dake Jihar Plateau. Rahoton yace an kama su ne bayan da wasu da aka kama a baya suka bayar da bayanai akan maboyarsu. Kuma an kamasu ne a kauyen Lugere Sho. Hakanan an kara kama wani me garkuwa da mutanen a Kauyen Kwok duk dai a Barkin Ladi kuma yana bayar da bayanai game da ta'asar da yayi a baya ciki hadda garkuwa da mutane a jiharta Filato da Nasarawa. Hakanan ya bayar da bayanai akan wadanda suke aiki tare da maboyarsu inda jami'an tsaro tuni suka bazama dan nemosu.
Gwamnatin Shugaba Tinubu na shirin karbi bashi har sau shidda daga bankin Duniya a wannan shekarar

Gwamnatin Shugaba Tinubu na shirin karbi bashi har sau shidda daga bankin Duniya a wannan shekarar

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na shirin karbo bashi har sau shidda daga bankin Duniya da jimullar kudin suka kai Dala Biliyan $2.23 a wannan shekarar da muke ciki ta 2025. Bayanai daga bankin Duniyar ya nuna cewa hakan zai kawo yawan kudaden da Bankin ya baiwa Najeriya bashi zuwa jimullar Dala Biliyan $9.25 a cikin shekaru 3 da suka gabata. Hakan na kara nuni da yanda Najeriya ke dogaro da bashi wajan gudanar da ayyukan Gwammati. Rahotanni sun bayyana cewa, a mulkin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu an samu karin yawan bashin da ake bin Najeriya, wanda ko da a shekarar data gabata, shugaban ya ciwo bashi sosai. Hakan na zuwane duk da kiran da shugaban Kungiyar Kwadago ta NLC, Joe Ajaero yayi ga bankin Duniyar na cewa su daina baiwa shuwag...
Hotunan dan shekaru 60 daya nemi auren ‘yar shekaru sha shida sun dauki hankula, wasu dai sun ce kudi gareshi shiyasa

Hotunan dan shekaru 60 daya nemi auren ‘yar shekaru sha shida sun dauki hankula, wasu dai sun ce kudi gareshi shiyasa

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wani mutum dan shekaru 60 da wata da aka bayyanata a matsayin 'yar shekaru 16 sun bayyana a kafafen sada zumunta suna soyayya. An ga yanda mutumin ya saka mata zobe a hannu yana nunawa alamar ta amince da soyayyarsa. Lamarin dai ya jawo cece-kuce, musamman kasancewarsu kirista inda da dama ke cewa da musulmai ne da ba karamin zagi zasu sha ba.
Ana rade-radin Budurwar Jude Bellingham Kàrùwàcè, gashi kuma har magana ta yi nisa tsakaninsu ya kaita ta gaishe da iyayensa

Ana rade-radin Budurwar Jude Bellingham Kàrùwàcè, gashi kuma har magana ta yi nisa tsakaninsu ya kaita ta gaishe da iyayensa

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Rahotanni sun bayyana cewa Budurwar tauraron dan Kwallon Real Madrid Jude Bellingham watau Ashlyn Castro Karuwace. Dalili kuwa shine an ga ta bude shafi a dandalin yanar gizo na Karuwai a kasar Ingila. Hakanan ana zargin Ashlyn da cewa ta yi karyar Shekaru. Bayanan da ake dasu shine, an haifi Ashlyn a December 17, 1997 a Long Beach dake California wanda a watan Janairu da ya gabata ta cika shekaru 27 kenan. Saidai wata Majiya ta bayyana cewa asalin Shekarun Ashlyn 32 ne. ...
Wata Sabuwar cuta da ba’a taba ganin irin ta ba ta kkàshè mutane 50

Wata Sabuwar cuta da ba’a taba ganin irin ta ba ta kkàshè mutane 50

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Congo sun bayyana cewa, wata sabuwar cuta da ba'a santa ba ta kashe mutane akalla 50. Hukumar lafiya ta Duniya, WHO ce ta bayyana hakan inda tace cutar na kuma ci gaba da yaduwa. Mahukunta a kasar na hada kai da hukumar ta WHO dan yin bincike akan wannan sabuwar cuta. Zuwa yanzu, cutar ta kama mutane 431 wanda kuma daga ciki mutane 53 sun mutu. Rahoton yace an fara ganin cutar ne a jikin wasu yara 'yan kasa da shekaru 5 su 3 wadanda suka fara nuna alamun cutar bayan cin mataccen Jemage. Alamomin cutar sun hada da Ciwon kai, Zazzabi, Zawo, da kasala. Kuma yawanci cutar na kisa ne kwana biyu bayan an kamu da ita. Yanayin garuruwan da mutanen ke kamuwa da cutar wanda babu wadatattun asibitoci ne yasa ake samun saurin yaduwar cutar inji WHO.
Ba za’a iya samun zaben gaskiya ba a Najeriya>>Inji Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan

Ba za’a iya samun zaben gaskiya ba a Najeriya>>Inji Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan

Duk Labarai
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayyana cewa, ba za'a iya samun zaben gaskiya ba a Najeriya. Goodluck Jonathan ya bayyana hakane a wajan wani taro da aka gudanar inda yace babbar matsalar itace akwai masu zabe da ake amfani dasu wadanda babu su a zahiri. Jonathan yace sai an samu shuwagabannin hukumar zabe masu nagarta wadanda da su yi magudi kara su sauka daga mukaminsu kamin a samu abinda ake so. Yace ba hujja bace shugaban hukumar zabe yace wai matsa masa aka yi yayi magudi ba, idan aka matsama sai kace gara ka sauka daka aikata ba daidai ba.
An daure malamai 2 da sukawa dalibansu mata Fyàde

An daure malamai 2 da sukawa dalibansu mata Fyàde

Duk Labarai
Babbar kotun jihar Ekiti ta sanar da hukuncin daurin shekaru 44 ga wasu malamai da aka kama da laifin yiwa dalibansu fyade. Malaman sune Ajibola Gbenga dan shekaru 43 sai kuma Olaofe Ayodele dan shekaru 52. Daya daga cikin yaran da sukawa fyaden me shekaru 17 ta bayyana cewa akwai ranar da daga makaranta ya bata kudi naira 200 yace ta je gaban wani gidan mai ta jirashi. Tace tana tsaye sai ga wata dalibar itama ta je wajan inda tace malamin nasu ne itama yace ta jirashi a wajan Tace suna tsaye sai malamin nasu ya karaso shi da abokinsa ya tafi dasu zuwa wani Otal. Inda anan ne aka kaisu dakuna daban-daban aka yi lalata dasu. Tace daga nan sai malamin ya rika damunta da yawa. Daga nan ta ce sai ta fara sanarwa da mahaifiyarta saboda abin ya dameta. Lauyan yaran ya ...
Akwai matsin tattalin arziki a kasarnan dan haka kada ku tsayawa sana’a ko aiki daya, ku raba kafa dan samun saukin rayuwa>>Shugaba Tinubu

Akwai matsin tattalin arziki a kasarnan dan haka kada ku tsayawa sana’a ko aiki daya, ku raba kafa dan samun saukin rayuwa>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya baiwa 'yan Najeriya shawarar cewa su raba kafa, kada su tsayawa sana'a daya. Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na ChannelsTV. Yace ba zai yiyu mutum ya tsayawa sana'a ko aiki daya ba. Yace misali idan akwai gona a kusa da inda kake, sai ka dan yi noma dan samun saukin rayuwa. Ya karkare da cewa ya kamata mutane su samarwa kansu mafita.