Saturday, February 21
Shadow

Duk Labarai

Kalli bidiyon Soja yana kuka da bankwana na karshe kamin a kkasheshi a fagen yaki

Kalli bidiyon Soja yana kuka da bankwana na karshe kamin a kkasheshi a fagen yaki

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Bidiyon wani sojan kasar Congo ya dauki hankula a kafafen sada zumunta inda aka ganshi yana kuka yana neman a taimakawa iyalansa a basu hakkinshi bayan ya mutu. Kalli Bidiyon anan https://www.youtube.com/watch?v=ACuySd7lNTM?si=XjLZLSDaPegjizRY Da alama sojan yana fagen daga ne dan har harbin bindiga da aka masa sai da ya nuna.
Matawalle Ga Amaechi: Jami’an tsaro na sa ido kan ka bisa cewa ƴan Siyasa na yin kisa don samun mulki

Matawalle Ga Amaechi: Jami’an tsaro na sa ido kan ka bisa cewa ƴan Siyasa na yin kisa don samun mulki

Duk Labarai
Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya yi tir da kalaman da tsohon minista kuma tsohon gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya yi kwanan nan. Amaechi ya ce Shugaba Bola Tinubu da sauran ƴan siyasa ba za su mika mulki ga matasa ba tare da an kai ruwa rana ba. A wata sanarwa da daraktan yada labarai na ma’aikatar tsaro, Henshaw Ogubike, ya fitar a jiya Alhamis, Matawalle ya bayyana kalaman Amaechi a matsayin “rura wutar rikici.” “Abin takaici ne kuma babbar barazana ga kasa idan tsohon mai rike da mukamin gwamnati zai yi irin wadannan maganganu,” in ji sanarwar. “A daidai lokacin da gwamnati ke aiki tukuru don inganta hadin kan kasa da tsaro, babu wani shugaba mai kishi da zai rura wutar tashin hankali da rikicin siyasa.”
WATA SABUWA: Mijin Hussaina Seaman Abbas yayi Jawabi yace babu abin da ya faru a tsakaninsa da matarsa Hussaina

WATA SABUWA: Mijin Hussaina Seaman Abbas yayi Jawabi yace babu abin da ya faru a tsakaninsa da matarsa Hussaina

Duk Labarai
Mijin Hussaina Seaman Abbas yayi Jawabi yace babu abin da ya faru a tsakaninsa da matarsa Hussaina. Ya bayyana hakane bayan da bidiyon ta ya bayyana aka ji tana cewa yanzu basa tare kuma tana musanta cewa an bata kudi da mota. Seaman Abbas ya karyata cewa akwai matsalar kudi data taso tsakaninsu. Kalli Bidiyon nasa anan Bidiyon da Husaina ta yi dai bai yiwa Ordinary President dadi ba inda ya bayyana cewa itama ta yadda da zargin da ake cewa an bashi kudi ya ki bata kenan. Kalli bidiyon hussaina nan A bidiyonsa da yayi magana kan lamarin a wajan shirya shirin da yake yi, ya bayyana cewa, shine ya rika kashe kudi akan case din Husaina amma babu wanda ya bashi ko sisi. Kalli bidiyon anan
An shirya gagarumar zanga-zanga ranar 4 ga watan Fabrairu saboda karin kudin kiran waya da kaso 50

An shirya gagarumar zanga-zanga ranar 4 ga watan Fabrairu saboda karin kudin kiran waya da kaso 50

Duk Labarai
Kungiyoyin fafutuka a Najeriya da suka hada dana Kwadago da sauransu sun bayyana aniyar fara zanga-zanga akan karin kudin kiran waya da kaso 50 cikin 100. Sauran kungiyoyin da suka goyi bayan wannan zanga-zangar sun hada da HURIWA,JAF da NASU ta ma'aikatan jami'o'i. Kungiyoyin sun yi kira ga 'yan Najeriya da su shiga wannan zanga-zangar a yi dasu dan nuna rashin jin dadin karin kudin kiran. Hakanan itama kungiyar SERAP ta bayyanawa hukumar sadarwa, NCC cewa zata kai kara kotu kan lamarin. Saidai NCC din ta yi kira ga kungiyoyin da su zo a yi zaman fahimtar juna dan ta yi bayanin dalilin da yasa aka yi wancan karin.
Munafurci da rashin aikin yi ne ke damunka>>Shehu Sani ya Gayawa El-Rufai kan caccakar Gwamnatin Tinubu

Munafurci da rashin aikin yi ne ke damunka>>Shehu Sani ya Gayawa El-Rufai kan caccakar Gwamnatin Tinubu

Duk Labarai
Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya soki tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai saboda sukar Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu. A martanin da yawa El-Rufai ta shafin X, Shehu Sani yace rashin aikin yi da kuma damuwa da munafurcine suka dabaibaye El-Rufai. Yace a lokacin yana gwamnan Karaduna, El-Rufai bai dauki 'yan adawa a matsayin komai ba, amma wai yau shine yake nuna yana tare da 'yan adawa. Yace kawai dan ba'a bashi mukami a Gwamnatin Tinubu bane abin ke damunshi yake ta bi yana bata Gwamnatin. A baya dai, El-Rufai ya bayyana cewa jahilaine a cikin gwamnatin Bola Ahmad Tinubu. Shehu Sani ya kara da cewa a yanzu El-Rufai yana ta bine duk wani taron dattawa a Arewa yana yada manufar bangaranci da raba kai.
Magidanci ya kkashe diyarsa me shekaru 15 saboda yin TikTok

Magidanci ya kkashe diyarsa me shekaru 15 saboda yin TikTok

Duk Labarai
Wani magidanci a kasar Pakistan ya kashe diyarsa saboda ta na yin Bidiyon TikTok wanda baya so. Mutumin me suna Anwar ul-Haq bai dade da komawa kasarsa ta Pakistan ba daga kasar Amurka tare da diyarsa wadda ya haifa a can. Rahotanni daga kafar yada labarai ta kasar Pakistan Geo News sun ce Anwar ya harbe diyar tasa ne a kan titi a Balochistan’s Quetta ranar Talata. Jami'in dansanda, Zohaib Mohsin yace an kama Anwar inda da farko yayi ikirarin cewa wani dan Bindiga ne da ba'a san kowanene ba ya kashe diyar tasa amma daga baya ya amsa cewa shine. A kasar Pakistan dan dangi kan kashe mata idan suka jawo musu abin kunya.
Babbar Kotun Birnin Tarayya da ke Kuje ta dage gurfanar da tsohon Sakataren NHIS, Farfesa Usman Yusuf, zuwa ranar 3 ga Fabrairu, 2025

Babbar Kotun Birnin Tarayya da ke Kuje ta dage gurfanar da tsohon Sakataren NHIS, Farfesa Usman Yusuf, zuwa ranar 3 ga Fabrairu, 2025

Duk Labarai
EFCC ta kama Yusuf bisa zargin aikata almundahana kuma an shirya gurfanar da shi a ranar 30 ga Janairu, amma kotu ta jinkirta shari'ar don bai wa masu gabatar da kara damar gyara tuhume-tuhumen da ke kansa. An ki amincewa da bukatar Bada beli, inda alkalin kotu ya umarci a ci gaba da tsare shi a hannun EFCC har zuwa ranar da za a sake gurfanar da shi. Menene ra'ayinku?
Bata gari sun sake kaiwa wutar lantarkin Najeriya hari

Bata gari sun sake kaiwa wutar lantarkin Najeriya hari

Duk Labarai
Rahotanni daga kamfanin kula da wuta na kasa, TCN sun bayyana cewa, wasu bata gari sun sake kaiwa wutar lantarkin Najeriya hari. Rahoton yace an kaiwa Tangarahon wutar ne dake kan titin Ugwuaji zuwa Makurdi a jihar Benue hari. Me kula da yada labarai ta kamfanin, Ndidi Mbah ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba. Tace an yi barnar ne a ranar Asabar, 25 ga watan Janairu na shekarar 2025. Tace da misalin karfe 3 na darene aka kai harin saidai mazauna garin sun ankara da maharan kamin su aikata wannan barna inda suka kai musu wawa, an kama mutum daya inda sauran suka tsere. Sun mika wanda suka kama din ga 'yansanda kamar yanda Mbah ta bayyana. Tace suna yabawa mutanen kauyen na Watuolo bisa wannan kokari inda ta yi kira ga sauran garuruwan da irin wad...