Saturday, February 21
Shadow

Duk Labarai

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana dalilin da yasa yayi sulhu da ‘yan Bìndìgà

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana dalilin da yasa yayi sulhu da ‘yan Bìndìgà

Duk Labarai
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana dalilin da yasa yayi sulhu da 'yan Bindiga a jiharsa. Gwamnan ya bayyana hakanne a hirar da BBChausa ta yi dashi. Ya bayyana cewa, yayi sulhu da 'yan Bindigar ne saboda ko da mutum daya aka kashe sai Allah ya tambayeshi. Ya kara da cewa, Basu baiwa 'yan Bindigar ko sisi ba sannan kuma sun saki wadanda suka yi garkuwa dasu. Yace harkar kasuwanci da noma na ci gaba da habaka tun bayan lamarin.
Gwamnati na da arzikin da za ta ɗauki nauyin tafiye-tafiyen Tinubu ko mai yawan su – Minista

Gwamnati na da arzikin da za ta ɗauki nauyin tafiye-tafiyen Tinubu ko mai yawan su – Minista

Duk Labarai
Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya ce Najeriya na da arzikin da za ta iya daukar nauyin tafiye-tafiyen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yawan yi zuwa kasashen waje tun bayan hawansa mulki. Tafiye-tafiyen da Tinubu ke yi zuwa kasashen waje na shan suka daga al'ummar ƙasar duba da matsalar tattalin arziki da ake fama da ita. Sai dai da ya ke magana a shirin 'Politics Today' na Channels TV, Tuggar ya ce Tinubu, sabanin korafe-korafen da ake yi, har ma yana bukatar kara tafiye-tafiyen saboda mahimmancin dabarunsa da kuma amfanin da su ke da shi ga kasar. Ministan ya bayyana cewa, Tinubu zai iya karfafa alaka da sauran shugabannin kasashen duniya ne kawai a yunkurinsa na dora kasar nan kan turba mai kyau ta hanyar yin tattaki zuwa ƙasashen.. Ya ce, “Wannan korafe-korafen ba su ...
‘Yan Bìndìgà sun sake kai mummunan hari Abuja

‘Yan Bìndìgà sun sake kai mummunan hari Abuja

Duk Labarai
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, 'yan Bindiga sun sake kai hari Abujar. 'Yan Bindigar wanda ake zargin masu garkuwa da mutanene sun kai harinne a Cikakore dake Kubwa a gundumar Bwari. Kuma sun sace wani mutum da matarsa da dansa da wasu karin mutane 2. Wasu shaidu da suka shaida lamarin sun bayyana cewa, masu garkuwa da mutanen sun kai su 30 rike da bindigar AK47 inda suka shiga gidan Adefija Micheal Akinropo suka saceshi da matarshi da dansa da dan uwansa. Shaidan ya kara da cewa, 'yansanda daga ofishin 'yansandan Byazin police station sun halarci wajan inda yace wanda suka yi garkuwa da mutanen basu tuntubi kowa ba zuwa 'yanzu. Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa ta tuntubi kakakin 'yansandan Abuja, Josephine Adeh kan lamarin inda tace tana kan hanya am...
SANATA BARAU JIBRIL NE YAKE ASSASA DUK WATA FITINA A JIHAR KANO

SANATA BARAU JIBRIL NE YAKE ASSASA DUK WATA FITINA A JIHAR KANO

Duk Labarai
Shahararren ɗan jaridar nan, Jaafar Jaafar ya zargi mataimakin shugaban majalissar dattijai Sanata Barau Jibrin da hannu cikin fitintinu masu nasaba da siyasa da ke faruwa a Jihar Kano. Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito Jaafar Jaafar na zarge-zargen ne ta cikin shirin "Fashin Baƙi" da suka saba gabatarwa mako-mako. A cewar Jaafar "Mutane da yawa suna tunanin Ganduje ne, Wallahi Barau ya fi hannu a wannan masifar. Suna shirya gidoga ne su faɗa wa shugaban ƙasa cewa mutane sun dawo daga rakiyar gwamnati mai ci a Jihar Kano ba sa son ta idan ta yi taro aka gani da jama’a da yawa ya soke wannan zargi. Kusan duk wannan abubuwan da ake ƙullawa Wallahi da hannunsu. Ko ɗansanda za a kawo Kano sai wanda suke so wanda zai kare muradunsu. Muna da bayanan sirri". Jaafar Jaafarya ce. Me zaku ce?...
Kalli Hotuna: Kwamandan Sojojin Najariya da aka kkashe tare da Wasu sojoji sama da 20 a jihar Borno

Kalli Hotuna: Kwamandan Sojojin Najariya da aka kkashe tare da Wasu sojoji sama da 20 a jihar Borno

Duk Labarai
Kwamandan sojojin Najariya na runduna na 149 dake Malam Fatori jihar Borno Lt. Col. TE Alari da aka kashe kenan a ranar 24 ga watan Janairu a wani mummunan hari da ya faru. An kashe shine tare da wasu manyan sojoji 2 da kuma sauran kananan sojoji 17. Ana zargin kungiyar B0k0 Hàràm da ISWAP ne suka kai harin. Saidai rahotanni sun banbanta kan yanda aka kai harin. Inda kafafen yada labarai da yawa sukace an kai harinne kan sansanin sojojin dake garin Malam Fatori dake iyakar Najeriya da Nijar, a bangare guda kuma, shahararren me watsa labarai na tsaro, Zagazola Makama ya ruwaito cewa harin kunar bakin wakene aka kai kan tawagar kwamandan. Saidai abu daya daya tabbata shine an kai harin kuma an kashe sojojin.
Gyaran Najeriya sai Allah>>Inji Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Gyaran Najeriya sai Allah>>Inji Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Duk Labarai
Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, Allah ne kadai da ya halicci Najeriya zai iya gyarata. Ya bayyana hakane a wajan wani taron Jam'iyyar APC da ya gudana a jihar Katsina ranar Asabar data gabata inda masoyansa da yawa suka taru. Wannan kalamai nasa sun jawo suka da Allah wadai musamman daga 'yan jam'iyyun adawa da kungiyoyin fafutuka. Misali kakakin Jam'iyyar NNPP, Ladipo Johnson ya bayyana cewa, Jam'iyyar APC yaudarar 'yan Najeriya ta yi duk da cewa ta san bata san hanyar da zata warware matsalolin Najeriya ba amma ta karbi ragamar aikin. Ya kara da cewa, wannan magana da tsohon shugaban kasar yayi alamace ta cewa APC ta gaza kuma ba zasu iya magance matsalar Najeriya ba inda suka jawowa kasar koma bayan tattalin arziki, ya kuma ce hakan na nuni da cewa ko...