Saturday, February 21
Shadow

Duk Labarai

Banson kasata Ingila ta zama kamar matalauciyar kasa Najeriya>>Inji Kemi Badenoch

Banson kasata Ingila ta zama kamar matalauciyar kasa Najeriya>>Inji Kemi Badenoch

Duk Labarai
Shugabar Jam'iyyar 'yan ra'ayin mazan jiya ta kasar Ingila, UK Conservative Party, Kemi Badenoch ta sake sukar 'yan Najeriya duk da cewa ita 'yar asalin Najeriyar ce. Da take magana ta farko a shekarar 2025 a wajan wani taro na musamman ranar Alhamis, Kemi tace bata son ingila ta zama kamar Najeriya, tace ta ga yanda danginta masu hali suka tsiyace saboda rashin gwamnati me kyau da tsadar rayuwa da ta yi yawa. Kemi na 'yar shekaru 16 ta bar Najeriya zuwa kasar Ingila da kudin babanta na karshe wanda basu wuce fan £100 ba. Kemi ta kara da cewa, tana aiki tukuru domin ganin wahalar da ke Najeriya bata maimaitu a kasar Ingila ba. A baya, Kemi ta zagi 'yan Najeriya da cewa 'yan fashi da makami ne.
Kuma Dai: Kalli Bidiyon tsìraìcì na wata ‘yar Tiktok ya bayyana

Kuma Dai: Kalli Bidiyon tsìraìcì na wata ‘yar Tiktok ya bayyana

Duk Labarai
A yayin da a baya bidiyin tsiraici na 'yan Tiktok yayi tashen bayyana, an samu saukin lamarin. A baya dai bidiyon 'yan Tiktok irin su Babiana, Hafsat Baby da sauransu ya bayyana wanda ya dauki hankula a kafafen sada zumunta. A yanzu ma na wata da ake cewa Shalelene ya bayyana. Shalele dai ta yi suna wajan sukar mutane da yawa a shafin nata na TikTok wanda hakan ne yasa wasu ke kurnar ganin bidiyon ta itama ya bayyana. https://www.tiktok.com/@juniorsadeq7/video/7460639878242405637?_t=ZM-8t8dRHhXZRd&_r=1 Kazancewar Bidiyon ya nuna tsiraici da yawa ne yasa shafin hutudole.com ba zai iya wallafashi ba.
Ana zargin shugaban bankin First Bank da satar Naira Biliyan 12.3

Ana zargin shugaban bankin First Bank da satar Naira Biliyan 12.3

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar yaki a rashawa da cin hanci, EFCC zata gurfanar da tsohon shugaban bankin First Bank Stephen Onasanya a gaban kotu bisa zargin satar Naira Biliyan 12.3. Babbar kotun tarayya dake Legas ta saka ranar 20 ga watan Janairu dan fara sauraren karar da EFCC ke yi akan Onasanya da shugaban kamfanin Flourmills Group, Oba Otudeko. Akwai kuma Soji Akintayo wanda shima yana cikin wadanda ake zargi da kuma wani kamfani me suna Anchorage Leisure wanda duka ake zargin sun hada hannu wajan yin wannan sata.  Ana zargin sun aikata satarne a tsakanin shekarun 2013 zuwa 2014.
Gwamnatin Tarayya ta ware N252.89bn dan ci gaba da gyaran titin Abuja zuwa Kano tace cikin watanni 12 za’a kammalashi

Gwamnatin Tarayya ta ware N252.89bn dan ci gaba da gyaran titin Abuja zuwa Kano tace cikin watanni 12 za’a kammalashi

Duk Labarai
Gwamnatin ta sanar da amincewa da fitar da Naira N252.89bn dan ci gaba da gyaran titin Abuja zuwa Kano. Ministan Ayyuka, Dave Umahi ne ya tabbatar da hakan inda yace za'a gabatar da wannan magana a gaban majalisar zartaswa ta kasa dan amincewa da ita. Kamfanin da aka baiwa kwangilar wannan aiki shine Infoust Nigeria Limited. Ministan yace za'a yi amfani da fasahar zamani dan gyaran titin wanda ke saukaka tafiye-tafiye da cinikayya tsakanin kudu da Arewa.
Bankin Duniya yace Tattalin arzikin Najeriya zai karu da kaso 3.6

Bankin Duniya yace Tattalin arzikin Najeriya zai karu da kaso 3.6

Duk Labarai
Bankin Duniya ya bayyana cewa, tattalin arzikin Najeriya zai karu da kaso 3.6 tsakanin shekarar 2025 zuwa 2026. Bankin yace hakan zai farune bayan da Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta dauki matakan tada komadar tattalin arziki. Bankin yace bangarorin da suka fi samun tagomashi sune na kudi da kuma sadarwa. Matakan da gwamatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ta dauka sun hada da cire tallafin man fetur da karya darajar Naira da sauransu.
Wahalar rayuwa a Najeriya tasa mata sun fara aikin Jari Bola

Wahalar rayuwa a Najeriya tasa mata sun fara aikin Jari Bola

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, wahalar rayuwa a Najeriya tasa mata sun fara aikin jari Bola wanda aiki ne da aka fi sanin maza da yi. An ga matan na aikin Jari Bola ne a Jihar Legas inda jaridar Vanguard tace yawancinsu matan aurene. Wasu daga cikin matan da jaridar ta yi hira dasu sun bayyana cewa, Mazajensu ne suka rasu wasu kuma sun bayyana cewa an kori mazajensu daga wajan aiki ne da dai sauran matsalolin rayuwa. Tun bayan hawan mulkin Shugaba Bola Ahmad Tinubu kuma ya cire tallafin man fetur a ranar farko da ya karbi mulkin, kasar ta fada cikin matsin tattalin arziki wanda har yanzu ba'a warware ba.
Aminu Ado Bayero Ya Daina Bari Lauyoyi Suna Damfararsa Domin Ko An Koma Kotu Ma Sanusi II Ne Sarki, Inji Lauya Femi Falana

Aminu Ado Bayero Ya Daina Bari Lauyoyi Suna Damfararsa Domin Ko An Koma Kotu Ma Sanusi II Ne Sarki, Inji Lauya Femi Falana

Duk Labarai
Babban Lauya Femi Falana SAN, wanda kuma babban Lauya ne mai kare hakkin Dan Adam, ya kuma yi kira ga kungiyar Lauyoyi ta kasa da ta ladabtar da Lauyoyin da suke yaudaran bangaren Aminu Ado Bayero akan zuwa kotun koli. Kuma ya ja hankalin Lauyoyi da su dinga fadawa kan su da wanda suke wakilta gaskiyar al’amari. Me za ku ce?
Bazan goyi bayan Gwamnatin Tinubu ba>>Sarki Sanusi II

Bazan goyi bayan Gwamnatin Tinubu ba>>Sarki Sanusi II

Duk Labarai
Me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa ba zai taimakawa Gwamnatin Tinubu da shawarwarin gyaran tartalin arzikin Najeriya ba. Ya bayyana hakane a wajan taron tunawa da babban lauya, Gani Fawenhinmi a jihar Legas. Yace gwamnatin ta kasa samun wanda zai fito yawa mutanen Najeriya jawabi akan alfanu da dalilin tsaretsaren da ta kawo dake jefa mutane a matsalar matsin rayuwa. Sarki Sanusi yace mutanen dake cikin gwamnatin abokansa ne amma kuma basu nuna girmama abotar tasu ba dan haka ba zai taimakawa gwamnatin ta hanyar tayar da komadar tattalin arzikin kasarnan ba.
Matatar Man Fetur din Dangote ta dakushewa fetur din kasashen Turai kasuwa

Matatar Man Fetur din Dangote ta dakushewa fetur din kasashen Turai kasuwa

Duk Labarai
Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur, OPEC ta bayyana cewa, matatar man fetur ta Dangote tasa farashin man fetur ya karye a kasuwar kasashen Turai. Rahoton yace, Matatar man ta Dangote ta fitar da Man fetur, da man jirgin sama da Gas da sauransu. Rahoton ya kara da cewa, a baya Najeriya ta dogara ne kacokan wajan shigo da man fetur daga kasashen waje amma yanzu lamarin ya canja. Hakanan matatar man ta Dangote ba kasashen Africa kadai take sayarwa da Man fetur din ba, hadda kasashen Asia da sauransu. Ana sa ran a yayin da karfin mamatar da yawan kasashen da take fitarwa da man fetur ke karuwa, zata ci gaba da dakushewa kasuwar man fetur ta kasashen Turai Armashi.
Wani Mutum ya rasu a Abuja a hotel lokacin da suke tare da budurwarsa data taso tun daga jihar Jigawa ta kai masa ziyara

Wani Mutum ya rasu a Abuja a hotel lokacin da suke tare da budurwarsa data taso tun daga jihar Jigawa ta kai masa ziyara

Duk Labarai
Innalillahi Wa Inna Ilaihir Rajiun Wani Mutum ya rasu yau a Abuja a hotel lokacin da suke aikata zina shida budurwar sa da suka hadu a social media Bincike ya tabbatar da cewa Ƙwayoyin kara karfin maza ne yayi sanadiyar mutuwar tasa, ita budurwar tasa ƴar jahar Jigawa ce Ƙaramar Hukumar Dutse, tayi karya taje har Abuja ta same shi Allah ya tsare mu da mummunar kaddara. Cikakken Bayani: MARYAM TA JE ABUJA KARBAN iPhone 16 KO? LISSAFI YA KWABE!, DARASIN RAYUWA! Dazu da safe, Manajan gidan hotel na Palasa dake yankin Gwagwalada Abuja ya kai kara ofishin 'yan sanda na Gwagwalada bayan wani mutum ya mutu a dakin hotel din da ya kama shi da wata karuwa Sunan wanda ya mutu Lawal Ibrahim, sunan karuwarsa kuma Maryam Abba daga birnin Dutsen Jihar Jigawa, wanda sun hadu a social...