Friday, December 5
Shadow

Duk Labarai

Likitocin jihar Yobe basu shiga yajin aikin NLC ba

Likitocin jihar Yobe basu shiga yajin aikin NLC ba

Siyasa
Likitocin jihar Yobe karkashin kungiyarsu ta (NMA) basu shiga yajin aikin kungiyar kwadago ta NLC ba a ranar Litinin. Shugaban kungiyar na jihar, Dr Abubakar Kawu Mai Mala ne ya bayyana hakan inda yace duk da yake 'yan uwa ne su da NLC amma basa karkashin kungiyar. Ya kara da cewa, kuma bangaren lafiya a jihar ta Yobe na da matukar muhimmancin da baza'a kulleshi ba gaba daya.
Gwamnatin Tarayya ta amince ta biya sama da Naira dubu 60 a matsayin mafi karancin Albashi

Gwamnatin Tarayya ta amince ta biya sama da Naira dubu 60 a matsayin mafi karancin Albashi

Siyasa
Gwamnatin Najeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kungiyoyin kwadagon NLC da TUC a wani taron gaggawa da ta gudanar a ranar Litinin karkashin jagorancin sakataren gwamnatin kasar, George Akume a wani yunkuri na kawo karshen yajin aikin sai abinda hali ya yi da kungiyoyin kwadagon suka fara a wannan rana. Bangarorin biyu sun shafe sa’oi biyar zuwa shidda suna tattaunawa da juna kuma a karshe sun cimma matsaya a kan wasu batutuwa. Ministan yada labaran kasar Mohammed Idris ya shaida wa BBC cewa gwamnati ta amince ta yi kari a kan naira dubu 60 wanda shi ne sabon albashin mafi karanci na ma’aikata da ta gabatar wa kungiyoyin kwadagon tun farko, wanda suka yi fatali da shi. Ministan ya yi ikirarin cewa a karkashin yarjejeniyar da suka cimma kungiyoyin kwadagon sun amince su ...
Da Duminsa: Kungiyar Kwadago ta NLC ta amince ta dakatar da yajin aikin da take dan ci gaba da tattaunawa da Gwamnati

Da Duminsa: Kungiyar Kwadago ta NLC ta amince ta dakatar da yajin aikin da take dan ci gaba da tattaunawa da Gwamnati

Siyasa
Rahotannin da muke samu na cewa, Kungiyar Kwadago ta NLC da TUC sun amince su janye yajin aiki da suke dan ci gaba da tattaunawa da gwamnati. An samu wannan matsaya ne bayan zaman da wakilan kungiyoyin kwadagon da gwamnatin tarayya. Kungiyoyin zasu zauna da membobinsu gobe dan tattauna maganar janye yajin aikin. Gwamnatin tarayya ta amince a ci gaba da tattaunawa akan mafi karancin Albashi sama da Naira Dubu 60.
Mafarauci ya harbe abokin farautarsa inda yayi tsammanin dabbace

Mafarauci ya harbe abokin farautarsa inda yayi tsammanin dabbace

Tsaro
An kashe wani mafarauci Sunday Ijiola a Yewa jihar Ogun inda aka yi tsammanin dabbace. Atanda Agbobiado ne yayi kisan ranar 28 ga watan Mayu. Mafarauta kusan 15 ne suka fita farautar inda suka raba kawunansu a cikin daji. Da Atanda ya tabbatar da abinda ya aikata sai ya tsere. Wanda aka harba din dan kimanin shekaru 43 ya mutu akan hanyar zuwa Asibiti. Kakakin 'yansandan jihar Omolola Odutola ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace suna bincike akai.

Kungiyar kare hakkin Musulmi ta Murik ta jawo hankalin musulmai da kada su shiga yajin aiki

Duk Labarai
Kungiyar kare hakkin Musulmi ta murik ta bayyana cewa, yajin aikin da ake zai jefa rayuwar musulmai cikin wahala musamman ma ya dake fuskantar babbar Sallah. Dan haka kungiyar ta yi kira ga kungiyar kwadago data daga yajin aikin nada sai bayan sallah. Kungiyar ta bayyana hakane a sanarwar data fitar ta hannun babban daraktanta Professor Ishaq Akintola a yau Litinin. Ya bayyana cewa wannan yajin aiki zai saka musulmai wahalar ababen hawa dan haka suna kiran da a canja lokacin yin yajin aikin.
Dakarun da suka kewaye wurin tattaunawa da NLC masu gadin Ribadu ne – Sojin Najeriya

Dakarun da suka kewaye wurin tattaunawa da NLC masu gadin Ribadu ne – Sojin Najeriya

Siyasa
Rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin da ƙungiyar ƙwadago ta yi cewa sojoji sun kewaye wurin da suke tattaunawa da wakilan gwamnatin ƙasar, tana mai cewa masu ba da kariya ne ga mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro. Ɗazun nan muka kawo muku rahoton cewa NLC ta yi zargin sojoji sun yi wa ofishin sakataren gwamnatin tarayya tsinke yayin da suke ganawa da wakilan gwamnati kan yajin aikin da suke yi. Sai dai cikin wani martani da ta mayar a kan saƙon da NLC ta wallafa a dandalin X, rundunar sojan ta ce ba haka abin yake ba. "Ku sani cewa Mallam Nuhu Ribadu ma yana halartar ganawar kuma ya isa wurin ne da sojoji masu gadinsa da doka tanada," in ji saƙon. "Da zarar ganawar ta ƙare jami'an tsaron za su fice daga wurin tare da shi."
Za’a rataye matar da ta hallaka tsohon mijinta a Kebbi

Za’a rataye matar da ta hallaka tsohon mijinta a Kebbi

Duk Labarai
A ranar Litinin ɗin nan ne wata babbar kotu a Birnin Kebbi ta yanke wa wata mata Farida Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe tsohon mijinta, Alkalin Alkalai Attahiru Muhammad-Ibrahim. Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, an gurfanar da Abubakar a gaban kotu bisa laifin kisan kai a ranar 25 ga watan Agusta, 2022, yayin da aka shigar da babban tuhumar a ranar 26 ga Yuli, 2023. Mai gabatar da kara ya ce mai laifin ya daba wa tsohon mijin nata wani abu mai kaifi a cikinsa da wuyansa da kuma hannun hagu wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa. Da yake yanke hukunci, babban alkalin jihar, wanda ya yanke hukunci kan karar, Mai shari’a Umar Abubakar, ya ce kotun ta gamsu cewa wadda ake tuhumar ya aikata laifin, bisa ga hujjojin da masu gabatar d...
Jam’iyyar Labour ta ce yajin aiki zai ƙara wa ƴan Najeriya wahala ne kawai

Jam’iyyar Labour ta ce yajin aiki zai ƙara wa ƴan Najeriya wahala ne kawai

Siyasa
Jam'iyyar Labour ta yi kira ga ƙungiyoyin ƴan ƙwadago a Najeriya da su sake tattaunawa da gwamnati a kan maganar sabon albashi mafi ƙanƙanta maimakon shiga yajin aiki. Jam'iyyar ta ce a halin da Najeriya take ciki yajin aiki ba shi da amfani hasali ma zai iya ƙara wa ƴan ƙasar wahalhalun da suke ciki ne. Babban sakataren yaɗa labaran jam'iyyar Obiora Ifoh ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN). Ya ce tuni daman ƴan Najeriya na fama da katutun matsaloli, a don haka babu buƙatar yin abin da zai ƙara waɗannan wahalhalu. '' Ina ganin neman Naira 494 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi ba abu ne mai yuwuwa ba. Abu ne da ba zai ɗore ba saboda hakan na nufin cewa Najeriya za ta ɗauki duk kuɗin da take da shi ta riƙa biyan ma'aikata,'' in ji ...
Shugabannin ƙwadago da na gwamnati na tattaunawa

Shugabannin ƙwadago da na gwamnati na tattaunawa

Siyasa
Wakilan ƙungiyar ƙwadago ta NLC da TUC na can na ci gaba da tattaunawa da wakilan gwamnati a ofishin sakataren gwamnati da ke Abuja. Wannan dai na zuwa ne bayan kwashe sa'o'i da dama gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago suna yajin aiki a Najeriyar, inda asibitoci da makarantu da sauran ma'aikatu suka kasance a rufe. Gwamnatin shugaba Tinubu ta nemi 'yan ƙungiyar da su janye yajin aikin su koma bakin tattaunawa. Wannan tattaunawar ita ce zangon farko kafin wadda za a yi a ranar Talata.