Yadda Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya dakatar da tawagarsa har sai da yara 'yan Makaranta suka gama wucewa a hanya.
Wannan ya faru a hanyarsa ta koma wa gida, bayan ya halarci daurin auren 'yar gwamnan jihar Katsina, A'isha Dikko Umar Radda.
Rahotanni da hutudole ke sami na cewa yanzu haka tsohon shugaban kamfanin mai na kasa, NNPCL, Mele Kolo Kyari ya shiga hannun EFCC.
Tun ranar Juma'a ne dai EFCC ta yi nasarar cafkeshi inda aka fara masa tambayoyi shi da wasu tsaffin ma'aikatan da aka kamasu tare.
Rahotannin sun ce zai kwashe karshen makonnan a hannun EFCC inda za'a ci gaba da tuhumarsa.
Hukumar sojojin Najeriya ta sanar da kama wasu mutane 4 dake kaiwa 'yan ta'adda kayan masarufi, biyu daga cikin wadanda aka kama din sojoji ne.
Sanarwar tace an yi bincikenne a tsakanin ranar 26 ga watan Afrilu zuwa 29 ga watan kuma an yi bincikenne a kananan hukumomin Bama, Kukawa, da Madagali na jihar Borno.
Kakakin sojin, Major General Markus Kangye ya tabbatar da hakan inda yace abin takaici ne irin wannan cin amana.
Ya jawo hankalin kwamandojin yaki dasu saka ido dan lura da sojoji masu irin wannan hali inda ya gargadi sojojin da kai kansu ga irin wannan hanya ta halaka.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin ƙwato duka wurare da dazukan ƙasar da ƴanbindiga ke ɓuya, ta hanyar girke sabbin dabaru na zamani domin yaƙi da ta'addaci da ƴan fashin daji.
Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga jagororin jihar Katsina a lokacin liyafar cin abincin dare da aka shirya masa a gidan gwamnatin jihar ranar Juma'a.
''Dangane da matsalar tsaro, matsala ce da ta addabi ƙasarmu', kuma na yi magana da sojoji, na tabbatar musu cewa za mu yi duk mai yiwuwa don kawo ƙarshen matsalar ƴanbindiga'', in Tinubu.
"Za mu samar da kayan aiki na zamani domin ƙwace duka dazukan ƙasarmu daga hannun miyagu, matsalar tsaro ta shafi duka Najeriya ne ba wani yanki ba, kuma mun sani cewa indai muna so ƙasarmu ta ci gaba to dole mu kawa...
Wani dattijo mai shekaru 70 a duniya, Awad Al-Thouaib, wanda ke da mata biyu, ya samu shawarar su da ya karo aure.
Al-Thouaib, dan garin Taif a kasar Saudiyya, ya karade kafafen watsa labarai bayan da ya sanar da cewa matan nasa sun bashi shawarar ya auri mata ta uku, har ma su ka ce ya nemi zuƙeƙiyar yarinya mai karancin shekaru ya aura.
A cewar sa, matan nasa sun mishi alkawarin biya masana kuɗin da zai dauki amaryar ta sa su je hutun angwanci a duk inda ya ke so.
Ya ce su ma matan nasa biyun sun fara tsufa, shi ne su ka bashi shawarar da ya nemo yarinya sabon jini yadda za ta tallafawa rayuwar sa.
Shafin Lifeinsaudia.com ya ruwaito cewa tuni matan biyu sun yi shirin biki na mijin nasu da duk wacce ya ga ta yi masa a matsayin mata ta uku.
TIRƘASHI: Añ bankado Natasha na wasa da hankalin jama'a ne kawai game da zargin Akpabio?
Daga Ibrahim Jamiu Adamu, Abuja
Da so samu ne ba zan ce uffan game da abin da ke faruwa tsakanin Sanatar da aka tura ta wakilci al’ummar Kogi ta tsakiya Natasha da Shugaban majalisar Sanata Godswill Akpabio ba. Amma bayan dogon nazari sai na gane cewa tabbas wannan turka-turka ta jefa al’ummar da suka tura wannan baiwar Allah ta wakilce su tauye musu hakki.
Ga mai bibiyar lamuran da ke faruwa ya san yadda aka kawo inda muke a wanan batu na zarge-zargen Natasha. A waje na ina ganin ƙarara tana nuna ba ta san darajar abin da aka damƙa mata ba.
Mu fara da yadda ta watsar da haƙƙin wakilcin da miliyoyin mutane suka damka mata, kowa ya ga yadda take ta kalaman ɓatanci don neman tausayar al’u...
Shugaba kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Yunwa da talauci na kan gaba cikin jerin abubuwan dake jawo Talauci a Najeriya.
Shugaban ya bayyana hakanne a wajan kaddamar da wasu ayyukan da Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya gudanar a yayin ziyarar kwaki biyu da ya je.
Shugaba Tinubu ya jawo hankalin Gwamna Radda dama sauran Gwamnoni da su mayar da hankali wajan gudanar da ayyukansu ba tare da la'akari da masu kushe ba.
Yace idan suka yi aiki me kyau shine jama'a zasu gani su yaba.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bar Katsina bayan kammala ziyarar kwanki biyu da ya je jihar.
D misalin karfe 3 na yammacin ranar Asabar ne jirgin shugaban kasar ya bar filin jirgin sama na Umar Musa 'Yaradua dake jihar.
Shugaba Tinubu a yayjn ziyararsa a jihar Katsina ya ziyarci sojoji inda ya karfafa musu gwiwa sannan ya kaddamar da wasu ayyuka biyu na titi da wata cibiyar ayyukan noma da gwamnatin jihar ta gina.
A yau Asabar kuma shugaba Tinubu ya halarci daurin auren diyar gwamnan jihar Dikko Radda kamin barin Katsina.