Thursday, March 12
Shadow

Duk Labarai

Wani gurin Ibada ya bayyana a Legas inda musulmai da kirista ke zuwa suna ibada tare

Wani gurin Ibada ya bayyana a Legas inda musulmai da kirista ke zuwa suna ibada tare

Duk Labarai
Wani guri da ake kira da Jehova Allah a Legas ya bayyana inda musulmai da Kiristoci ke haduwa su yi Ibada. Gurin ana karatun Qur'ani a cikin sa sannan ana wakewake da addu'a irin ta Kiristanci. Lamarin ya baiwa mutane mamaki sosai musamman ganin yanda ba kasafai aka cika samun irin wannan hadaka ba a kasarnan. Rahoton jaridar Punchng yace an gina wajan ne shekaru 12 da suka gabata dan samar da hadin kai tsakanin musulmai da kirista.
Mun daina fargabar da muke yi akan Muslim-Muslim saboda Gwamnatin Tinubu ta mana Adalci>>Inji Kungiyar Kiristanci ta CAN

Mun daina fargabar da muke yi akan Muslim-Muslim saboda Gwamnatin Tinubu ta mana Adalci>>Inji Kungiyar Kiristanci ta CAN

Duk Labarai
Kungiyar kiristoci ta CAN ta bayyana cewa, sun daina bargabar da suke akan mulkin Muslim-Muslim. Kungiyar reshen Arewa ce ta bayyana hakan ta bakin shugabanta, Reverend Yakubu Pam. Ya bayyana cewa a yanzu sun daina Adawa da Gwamnatin ta Tinubu saboda yanda ta kewa kowane addini Adalci. Yace amma har yanzu suna kira ga Gwamnatin data baiwa kirista babban mukami dan ya wakilci bangaren kiristocin kasarnan.
Yarbawa sunce basu yadda da kotunan shari’ar musulunci a jihohinsu ba

Yarbawa sunce basu yadda da kotunan shari’ar musulunci a jihohinsu ba

Duk Labarai
Kungiyoyin dake fafutukar kafa kasar Yarbawa sun bayyana rashin amincewa da bullar kotunan shari'ar Musulunci a jihohinsu. Jihar Ekiti itace ta baya-bayannan da aka samu bullar kotun shari'ar Musulunci wadda har alkalai 3 Imam Abdullahi Abdul-Mutolib, Imam Abdulraheem Junaid-Bamigbola da Dr. Ibrahim Aminullahi-Ogunrinde sun yi zama sun saurari shari'ar rikicin aure guda biyu. Kamin nan a jihohin Lagos, Ogun, Oyo and Osun ma an samu ,aman kotun shari'ar Musuluncin. Zuwa yanzu, Jihar Ondo ce kadai bata da kotun shari'ar Musulunci a cikinta, hakanan itama Gwamnatin jihar Ekiti ta musanta cewa akwai kotun shari'ar musulunci a cikinta. Tuni dai aka samu wani Fasto me suna Pastor Oluwafemi J. Edafemi, ya jagoranci gamayyar wasu masu ruwa da tsaki a yankin na Yarbawa inda suka yi gang...
Duk da tallafin Gwamnatin tarayya, Farashin kayan abincin da ake shigowa dasu daga kasashen yayi tashin gwauron zabi

Duk da tallafin Gwamnatin tarayya, Farashin kayan abincin da ake shigowa dasu daga kasashen yayi tashin gwauron zabi

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, duk da tallafin da gwammatin tarayya ta bayar a fannin shigo da kayan abinci daga kasashen waje, farashin kayan abincin yayi tashin gwauron zabi. Rahoton yace Farashin kayan abincin da ake shigowa dasu daga kasashen waje ya tashi da kaso 37.65 kamar yanda hukumar kididdiga ta kasa, NBS ta sanar. An fitar da wadannan alkalumane a tsakanin watannin Disamba zuwa Najairu. Hakanan rahoton yace duk bayan wata, farashin kayan abincin yana kara tashi da karuwa.
Bidiyo:Kalli yanda matar aure ta baiwa saurayi lambar wayarta

Bidiyo:Kalli yanda matar aure ta baiwa saurayi lambar wayarta

Duk Labarai
Wata matar aure wadda 'yarsanda ce ta jawo cece-kuce bayan da ta baiwa Saurayi lambar wayarta. Matar wadda sunanta Chioma an ganta a cikin wani faifan bidiyon dake ta jawo a kafafen sada zumunta inda Saurayin ya kirata gefen titi. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1883120117271413123 Ya tambayeta, tana da aure ta amsa mai cewa Eh tana da aure inda yace yana sonta sannan ya karbi lambarta. Da yawa dai sun yi Allah wadai da wanda ya dauketa bidiyon sannan wasu sun yi Allah wadai da saurayin da be kyaleta ba tunda tace ita matar aure ce.
Gwamnatin tarayya tace za’a rika koyar da sana’o’in Gyaran fanfo, Aski, Gyaran waya, kwalliyar mata da sauransu a makarantun b0k0

Gwamnatin tarayya tace za’a rika koyar da sana’o’in Gyaran fanfo, Aski, Gyaran waya, kwalliyar mata da sauransu a makarantun b0k0

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya tace an saka sana'o'in Aski, Gyaran waya, gyaran fanfo, kwalliyar mata, Gyaran waya da sauransu cikin abubuwan da za'a rika koyarwa a makarantun boko. Za'a rika koyar da wadannan sana'o'i ne a makarantun firamare zuwa makarantun karamar sakandare. Wannan ya biyo bayan garambawul da akawa bangaren ilimi. Hukumar wayar da kai ta kasa, NOA ta ce an saka wadannan sana'o'i cikin karatu ne dan koyawa dalibai hanyar dogaro da kai. Sauran sana'o'in da za'a rika koyarwa sun hada da noma, kiwon kaji, gini, saka tayil, saka POP, da dai sauransu.
Buhari ya koma Najeriya bayan gabatar da shaida a kotun Paris

Buhari ya koma Najeriya bayan gabatar da shaida a kotun Paris

Duk Labarai
Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya koma kasar bayan gurfana a gaban wata kotu a birnin Paris na kasar Faransa. Cikin wani bidiyo da tsohon mataimakinsa na musamman kan harkokin sadarwa, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya nuna lokacin da tsohon shugaban kasar ke sauka daga jirgi a jihar Katsina. A farkon makon nan ne tsoffin shugabannin Najeriya biyu, Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari suka bayyana a gaban wata kotun cinikayya ta ƙasa da ƙasa da ke birnin Paris na a ƙasar Faransa domin ba da bahasi dangane da kwangilar aikin gina cibiyar samar da wutar lantarki ta Mambilla da ke jihar Taraba. Wani kamfani mai suna Sunrise Power ne dai ya kai gwamnatin Najeriya ƙara kan saɓa ƙa'idojin kwangilar, inda yake neman gwamnatin ta biya shi dalar Amurka biliyan...
Tsaffin Janarorin soja ne ke satar ma’adanai a Najeriya>>Oshiomhole

Tsaffin Janarorin soja ne ke satar ma’adanai a Najeriya>>Oshiomhole

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole ya yi zargin cewa, tsaffin janarorin soja ne ke satar ma'adanai a Najeriya. Oshiomhole ya bayyana hakane a yayin da shugaban kwamitin dake kula da harkar hakar ma'adanai a majalisar,Sampson Ekong ke muka sakamakon binciken kwamitinsa ga majalisar. Oshiomhole wanda shine shugaban kwamitin dake kula da harkokin cikin gida ya bayyana cewa, sun san wadannan tsaffin janarorin dan kuwa koda a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari sai da ya rubuta mai wasika akan ayyukan nasu. Ya kara da cewa, wadannan masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba suna safarar muhgan makamai dan gudanar da ayyukansu kamar yanda ake yi a sudan ta kudu. Oshiomhole ya bayar da shawarar cewa, maganin wannan matsala shine a samar da rundunar jami'an tsar...