Sunday, May 10
Shadow

Duk Labarai

An rantsar da shugabar ƙasa mace ta farko a Namibia

An rantsar da shugabar ƙasa mace ta farko a Namibia

Duk Labarai
An rantsar da Netumbo Nandi-Ndaitwah a matsayin shugabar ƙasar Namibia, wadda ta kafa tarihin zama mace ta farko da za ta jagoranci ƙasar. Tshohuwar ministar harkokin wajen ƙasar ta kasance jajirtaciyyar ƴar jam'iyyar SWAPO wadda ke mulkin Namibia tun bayan samun ƴancin kai daga Afirka ta Kudu a 1990. Da take magana da BBC, Nandi-Ndaitwah ta yarda da cewa wasu za su iya sukarta saboda jinsinta maimakon ayyukan da take yi - sai dai ta ce za ta ci gaba da yaƙi da cin zarafin jinsi. Netumbo ta shiga cikin jerin matan Afirka ƙalilan da suka jagoranci ƙasarsu tun lokacin da Liberia ta zaɓi shugabar ƙasa ta mace ta farko shekaru 20 da suka wuce.
Rashin lantarki ya tilasta rufe babban filin jirgin sama na Landan

Rashin lantarki ya tilasta rufe babban filin jirgin sama na Landan

Duk Labarai
An rufe Heathrow da ke yammacin London - tashar jirgin sama mafi cunkuso a nahiyar Turai - sakamakon gobara da aka samu a kusa da cibiyar lantarki da ke kusa da filin jirgin saman. Filin jirgin zai kasance a rufe har zuwa 12:00 na dare a yau Juma'a saboda matsalar lantarkin. Wakilin BBC ya ce babu wata sanarwa kan lokacin da za a iya dawo da lantarkin a Heathrow kuma filin jirgin ba shi da wani zaɓi illa daukar matakin rufewa domin kare lafiyar fasinjoji da ma'aikatansa. A bara fasinja miliyan 83 ne suka bi ta filin jirgin saman na Heathrow.
Dattawan arewa sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara bakin aiki

Dattawan arewa sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara bakin aiki

Duk Labarai
Ƙungiyar dattawan arewa ta nuna rashin jin daɗinta kan dakatar da gwamnan jihar Rivers da majalisar dokokin jihar da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi. A wata sanarwa da kakakin ƙungiyar Farfesa Abubakar Jika ya fitar, ya yi kira ga Tinubu da ya yi gaggawar mayar da gwamnan da mataimakinsa bakin aikinsu. Ƙungiyar ta ce duk da cewa sashe na 305 ya ba shugaban ƙasa damar ayyana dokar ta-ɓaci, "babu hujjar da za ta sa a ayyana dokar a jihar Rivers a yanzu," kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. "Dole ne shugaban ƙasa ya lalubo hanyoyin da za a warware matsalar rikicin siyasar jihar Rivers ɗin, sannan ya dakatar da dakatarwar da ya yi gwamnan da mataimakinsa da majalisar dokokin jihar domin tabbatar da wanzumar dimokuraɗiyya da adalci." Haka kuma ƙungiyar ta yi ga...
Bayan da taje majalisar Dinkin Duniya, Kafar Skynews da BBC, Sanata Natasha ta kuma je gidan yada labarai na DW inda a can ma tawa Sanata Godswill Akpabio tonon silili

Bayan da taje majalisar Dinkin Duniya, Kafar Skynews da BBC, Sanata Natasha ta kuma je gidan yada labarai na DW inda a can ma tawa Sanata Godswill Akpabio tonon silili

Duk Labarai
Da alama dai Sanata Natasha Akpoti bata da shirin hakura da maganar zargin nemanta da lalata da sanata Godswill Akpabio yayi ba. A ci gaba da neman hakkinta, a yanzu ta bayyana a kafar yada labarai ta DW inda a can ma ta bayyana irin zargin da takewa Sanata Godswill Akpabio. Sanata Natasha Akpoti a baya dai ta yi irin wannan bayyana a kafar Skynews da BBC. Hakanan ta je majalisar Dinkin Duniya. Da alama dai so take sai ta karade duka kafafen yada labarai na Duniya da wannan zargi nata.
An bayyana dan siyasa daya tal dake kayarwa da shugaba Tinubu gaba a zaben 2027

An bayyana dan siyasa daya tal dake kayarwa da shugaba Tinubu gaba a zaben 2027

Duk Labarai
A yayin da ake fuskantar zaben shekarar 2027 an bayyana dan siyasa daya tilo da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ke shakkar karawa dashi a shekarar 2023. Wani dan kasuwa, Stephen Akintayo ne ya bayyana hakan inda yace Peter Obi na jam'iyyar Labour Party ne ke kayarwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu gaba. Ya bayyana cewa, idan aka hada Peter Obi da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a matsayin mataimakinsa, Tinubu ba zai iya bacci ba.
Karanta Kaji:Sanatoci 3 kacal da suka ciri tuta suka ki amincewa da dokar dakatar da Gwamnan Rivers da shugaba Tinubu yayi

Karanta Kaji:Sanatoci 3 kacal da suka ciri tuta suka ki amincewa da dokar dakatar da Gwamnan Rivers da shugaba Tinubu yayi

Duk Labarai
Sanatoci 3 ne kacal suka ciri tuta inda suka ki amincewa da dakatar da gwamnan jihar Rivers da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yayi. A jiya ne dai majalisar dattijai data wakilai suka hada baki suka amince da dakatarwar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yawa Gwamnan Rivers. Saidai an bayyana sanatoci Seriake Dickson, da Enyinnaya Abaribe, da Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto a matsayin wadanda suka ki amincewa da wannan aniya ta shugaba Tinubu. Rahoton yace wadannan sanatoci ficewa suka yi daga zauren majalisar kamin kakakin majalisar ya bayyana amincewa da kudirin.
Idan Har Ɗan El-Rufai Bai Yarda Da SDP Ba, Wane Ɗan Nijeriya Ne Mai Hankali Zai Yarda Da Wannan Jam’iyya, Inji Reno Omokri

Idan Har Ɗan El-Rufai Bai Yarda Da SDP Ba, Wane Ɗan Nijeriya Ne Mai Hankali Zai Yarda Da Wannan Jam’iyya, Inji Reno Omokri

Duk Labarai
Idan Har Ɗan El-Rufai Bai Yarda Da SDP Ba, Wane Ɗan Nijeriya Ne Mai Hankali Zai Yarda Da Wannan Jam’iyya, Inji Reno Omokri. Nasir el-Rufai yana gayyatar Waziri Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi, da Kayode Fayemi su shiga jam’iyyar SDP tare da shi. Amma kawai wàwà ne zai amince da irin wannan gayyata, alhalin ma ɗansa, Bello El-Rufai, bai bar APC ya bi mahaifinsa ba. Daga Muhammad Kwairi Waziri
Kotu ta hana INEC shirya zabe dan yiwa Sanata Natasha Akpoti kiranye

Kotu ta hana INEC shirya zabe dan yiwa Sanata Natasha Akpoti kiranye

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, babbar Kotun tarayya dake Lokoja ta hana yiwa Sanata Natasha Akpoti kiranye. Kotun tace kada hukumar zabe me zaman kanta, INEC ta sake ta amince da bukatar shiryawa sanata Natasha Akpoti kiranye. Wani me suna Anebe Jacob Ogirima ne da wasu mutane hudu daga mazabar ta Sanata Natasha Akpoti suka shigar da bukatar a gaban kotun. Mai shari'a Justice Isa H. Dashen ta amince da bukatar tasu. Sannan an dage sauraren karar sai nan da 6 ga watan Mayu. A baya dai Bidiyo da hotuna aun bayyana na mutanen mazabar Sanata Natasha Akpoti inda aka ga ana shirya zaben yi mata kiranye. Sanata Natasha Akpoti ta fara samun matsala ne tun bayan da ta zargi kakakin majalisar, Sanata Godswill Akpabio da neman ta da lalata.
Kalli Bidiyo: Cikin sheshshekar kuka, Sanata Natasha Akpoti ta sake yiwa Sanata Godswill  Akpabio tonon silili inda tace harfa gaya mata yayi wai mijinta na morewa dan da gani tana juya masa kugunta da kyau

Kalli Bidiyo: Cikin sheshshekar kuka, Sanata Natasha Akpoti ta sake yiwa Sanata Godswill Akpabio tonon silili inda tace harfa gaya mata yayi wai mijinta na morewa dan da gani tana juya masa kugunta da kyau

Duk Labarai
Sanata Natasha Akpoti a hirar da aka yi da ita a kafar BBC ta bayyana cewa bata san me yasa wasu 'yan Najeriya basa gane irin halin da take ciki ba. Tace tana son ta samu guri ne da zata yi aiki ba tare da ana nemanta da lalata ba. Tace Sanata Godswill Akpabio har ce mata ya taba yi mijinta na morewa dan da gani tana juya masa duwawunta da kyau. Sanata Natasha Akpoti tace mata da yawa daga kasashen Africa daban-daban sun kirata inda suka rika gaya mata cewa suma suna fuskantar irin wannan cin zarafi a guraren aikinsu. Tace maganar cewa bata bi dokar majalisa bane yasa aka dakatar da ita ba gaskiya bane. kalli Bidiyon hirar anan