Karanta Abubuwa 13 game da Kudirin Harajin da Shugaba Tinubu ya nace sai ya aiwatar duk da Kwamitinsa na tattalin arziki shun bashi shawarar kada ya aiwatar da kudirin
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yayi fatali da shawarar kwamitinsa na tattalin Arziki da suka ce masa kada ya aiwatar da kudirin gyaran haraji inda yace sai yayi.
Kakakin shugaban kasar,Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
Ga abubuwa 13 game da kudirin dokar da ya kamata ku sani:
Canja tsarin karbar haraji na mutum gudaguda ga 'yan Najeriya a ciki da wajen kasar inda tsarin zai koma na zamani.
Daina Karbar Haraji daga hannun masu fitar da kaya zuwa kasar waje dan karfafa fitar da kayan Najeriya zuwa kasuwannin Duniya.
Daina karbar Haraji daga kananan 'yan Kasuwa.
Ba za'a karbi Haraji ba a hannun masu daukar Mafi karancin Albashi ba, sannan ma'aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu za'a rage musu Haraji zuwa kaso 90.
Ba za'a rika karb...








