
A yayin da ake tsaka da jimamin Abunda Fusatattun matasa sukawa malamar Islamiya Ummulkhairi a Maraban Jos, Jihar Kaduna.
An sakewa wasu mutane 2 irin wannan aika-aika a kauyen Unguwan dake kusa da maraban jos Kaduna.
Rahoton yace mutanen biyu sun ari sabon mashinne inda suka tafi Zaria akai dan yin wata ziyara, shine suka bi ta kauyen.
Mutanen garin na ganin su aka fara musu ihun barayi aka tare aka musu aika-aika aka binne gawarsu, kuma wani abin mamaki shine dattawan garin sun san an aikata hakan amma suka yi shiru.
Kakakin ‘yansandan jihar Kaduna, DSP Mansur ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sun kama mutane 6 da ake zargi a lamarin.